Chapter 120
Chapter 120
ta bude idonta suka sauka cikin nashi,sai tayi saurin maidasu ta rufe,wani mugun kyau yaga ta qara masa a hakan "Zaki iya tashi muje asibiti?" Fuska ta narke,ita kam gaba daya bata qaunar abinda zai sanya ta motsa,amma hakanan yayi mata dabara cikin lallabawa ya sanyata tashi ta saka hijab dinta suka fito. Yana driving amma duk bayan wasu sakanni sai ya juya ya kalleta,ta tattare gu daya cikin seat din motar,sai ya miqa hannu ya kashe ac din motar,yadan qara speed don su isa da wuri. Already samuel ya gama komai,dr jessica ce da kanta,cikin girmamawa ta nuna musu seat,ya zaunar da widad wadda taketa bi da kallo,cikin zuciyarta tana ta yaba kyanta,shi kuma ya tsaya daga bayanta kamar wani bodyguard. Akwai sanayya tsakaninsu,don haka ta fara gaidashi cikin girmamawa,ya amsa mata tare da tambayarta aiki "me yake damunki madam?" Dr jessica ta tambayi widad tana murmushi,idanu a narke ta maida dubanta ga abbas,saboda batasan kalar amsar da zata bata ba,sai ya share kamar bai gane tana kallonsa ba "Uhmm,inajinki madam,fell free,kiyi bayani" ta fada tana jan takardar dake gabanta. Bai ankara ba sai sheshsheqar kukanta da yaji,ya daga kai da sauri daga danna wayar da yakeyi yana dubanta,sai yaja kujerar kusa da ita ya zauna har gwiwoyinsu na gogayya dana juna "Listen widad?,me kuma ya faru?" Muryarta a shaqe a kuma shagwabe qwarai tace "Kaine" sosai sound dinta ya taba zuciyarsa,ya saki murmushi "Okay,to ya isa,dr......she had her first night,she feels that the place is hurting her" kai dr jessica ta gyada sannan tace "Muje na duba" bata gane me take nufi ba sai data hau gadon da take duba marasa lafiya bayan abbas ya taimaka mata,nan ta fara raba idanu,ta kuma narke masa tana hawaye sosai,don kunya takeji ta buda gurin kuma a sake gani?. Da qyar yasha kanta yana riqe da tafin hannunsa cikin nata ha dr jessica ta gama dubawa ta koma kan kujerarta "It's bruises,you hurt her a lot sir,but ba damuwa,she will recover in a few days" ta fada tana jan takarda "Saika qara haquri sir, she's too young,dole ta samu ciwuka haka musamman idan ya zamana anyi gaggawa,but with time zata saba" tura baki widad tayi gaba,itama dr din nan bata da kunya,zata saba dame?,yayin da abbas yadan saci kallonta ya saki boyayyen murmushi "Allah yasa" ya fadi qasa qasa,cikin ransa yake hasashen lokacin da widad din zata sallama masa ruhi zuciya da kuma rayuwarta,lallai da ya shiga jerin maza mafi sa'a a duniya. Magunguna ta rubuta mata masu kyau,sannan ta basu wasu shawarwari har hakan yasa widad din tadan sake,saidai kunya kamar qasa zata tsage ta shige,tana ganin kawai abbas din ya gama kunyatata. Ko a hanya da wani irin nutsuwa da takatsantsan yake driving din,dukka hankalinsa da kulawarsa yana kanta,haka da suka koma gida,ya sanyata gaba da tambayar abinda takeson ci,saidai taqi sawa bakinta komai don bata da appetite,gaba daya taste din bakinta ya gama daukewa,tana ta faman koke koke,ta narke masa qwarai,dama hausawa sukace mai neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki,tsohuwar rigima da kuma shagwaba gaba daya ranar bawan Allah abbas aka juyewa,shi kuwa ya sanya hannu bibbiyu ya karba,saboda a yanzun jinta yake dai dai da ruhinsa. Girki kusan kala uku yayi mata amma tace bata ci,daga qarshe sai daya hade girar sama da qasa ya zaunar da ita ya dinga bata da kansa sannan ya samu taci,ya bata maganungunan tasha bayan ya tilasta mata ta shiga ruwa. Saman cinyarsa ya dora kanta,taso ta zame amma ya hanata,yanason kawo kusanci sosai a tsakaninsa da ita,ya kuma fidda dukka wani tsoro nasa daga zuciyarta daya dasu a daren jiya,sai tayi likimo ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya,ita kanta tana matuqar son kwanciya a jikinsa,bata taba jin wani guri da take jin wani nutsuwa da kwanciyar hankali idan tana gurin ba irin cinyar tasa,amma for now tsoronsa takeji, tsoronsa takeji sosai,gani take kamar idan tayi bacci zai sake maimaita mata abinda ya aikata mata jiya. Sannu a hankali bacci mai dadi yayi awon gaba da ita,ya sauke ajiyar zuciya yana gyara mata kwanciya sosai yana kallon fuskarta, murmushi ya sake subuce masa,yakai.hannu zai shafi lips dinta sai kuma ya janye hannu da sauri gudun kada ya tasheta. Wuni guda ranar suna tare cikin gidan,kwata kwata ma ya manta da wani batun aiki,sai da aka nemeshi a gurin aikin sannan ya bada excuse din yana da patient. A daren duk yadda taso bijirewa kwana dakin haka ya mata dole ta kwana a dakin kuma cikin jikinsa,dukkansu shi da itan wani irin ni'imtaccen bacci ne yayi awon gaba dasu. Ko cikin duniyar baccinsa ya tabbatar da cewa wani gagarumin ci gaba da sauyi ne ya tunkaro rayuwarsa,sauka da shigar numfashinsa cikin wata irin nutsuwa. Washegari bayan sun idar da sallar asuba,dukkansu shi da ita suna saman abun sallah,kowanne jinsa yake kamar a wata sabuwar duniyar,musamman abbas da yakejin jiki da qirjinsa wasai,babu komai a ciki sai wata irin mahaukaciyar soyayyar widad din. "Ina kwana?" Ta fada qasa qasa kanta a qasa tana murza tafin hannunta. Gaba dayansa ya waiwayo,sai ya saki murmushi,ya cira hannunsa a nutse ya miqa mata yana cewa "Zo nan mu gaisa da kyau" manyan idanunta da suka dan fada kadan ta daga ta kalleshi,sai ta noqe kafada,don gaba daya tsoronsa takeji "Please mana baby doll" ya fada da wata irin kwantacciyar murya,qas ta sakeyi da kanta tana tuna kalaman mommynta,sai ta miqe a hankali ta fara takowa zuwa gabansa. Da idanu ya bita,yana jinta tana tsarga masa har cikin jinin jikinsa,yabi takunta da kallo,akan tsari take ajiye qafafun nata kamar wadda ake qirga ma adadin takunta. A gabansa ta tsugunna tana watsa masa qamshin jikinta,lumshe idonsa yayi zuciyarsa na bugawa,duk yadda taso daurewa ya kauda kai ya gaza,sai yasa hannunsa ya fusgota a tausashe yayi masauki a jikinsa. A tausashe ya maida hannuwansa ya rungumeta "Kin tashi lpy my baby?,ya jikin?" Ya rada mata a hankali cikin kunnuwanta,har sai da duk wata tsiga ta jikinta ta tashi,ta lumshe idonta gabanta yana bugawa da sauri da sauri "Da sauqi" "Ma sha Allah......haka nakeson ji,Allah yayi miki albarka" har cikin zuciyarta taji sanyin addu'ar,ya motsa bakinsa zaiyi magana,kafin yace komai wayarsa dake gefe ta dauki ringing. A nutse ya sauke idanunsa yana duba mai kiran,hafsat ce,sai ya tsaya yana kallon wayar kamar mai son karanto dalilin kiran nata ta cikin wayar. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 79 Kaman wanda aka yiwa hani da daga wayar har ta katse sannan ya miqa hannu ya dauki wayar,yana shirin binta kiran ya sake shigowa,sai ya gyarawa widad zama a jikinsa sosai,yana sake riqeta a jikinsa cikin wani taushi da salo "Ina ka shiga ne inata kira" abinda kunnuwansa suka fara jiye masa kenan,sai ya lumshe idanunsa ya kuma bude lokaci guda "Assalamualaikum" ya furta a nutse,a tunaninsa zata ankara da kuskurenta ta kuma gyara "Wa'alaikumus salam......inata kiran wayarku baku daga ba duka ku biyun" ta sake maimaitawa tare da amsa sallamar duka guri guda. Danne zuciyarsa yayi kadan,idan da sabo yaci ace ya saba da duk wata dabi'a ta hafsat din,to amma kullum baqin halayenta sake qaruwa sukeyi "jiya gaba daya ko ka nemeni,sannan itama inata kiranta bata daga ba" ta kuma fadi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155