Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 75

Chapter 75

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,328 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

rawa,taja da baya tana yarfe hannu jikinta yana rawa,hawaye na shirin tarar mata a ido,shi bai kula bama,don ya duqa zai dauke ruwan bayan ya furta "Subhanallah" sanda ya dago harta samu waje ta rakube,ya bita da kallo yana mamakin yadda take matuqar tsoron tarayya dashi,kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa,ya bude gorar ruwan ya fara sha,sannan ya miqe yana cewa "Zanje sallah,idan na dawo zaki shiga ciki ku gaisa da mutanen gidan,ga abinci nan a leda ki dauki naki" kai ta gyada masa gabanta na faduwa,bata samu nutsuwa ba har sai da yayi alwalar ya fice,ta bishi da kallo tana hararar hanya qwalla na gangaro mata,yanzu idan ummu ko mommy suka ga wannan abun da yakeyi fa?. A falo ya tsaya jiranta,ta fito yafe da mayafin abayar bayan ta cire hijabin da tayi sallar dashi "Koma ki samo babban mayafi,akwai mutane a waje" yayi maganar sanda yake dage labulen falon yana sake duba farfajiyar gidan,jikinta ta kalla,itadai bataga wani aibu a haka ba,amma sai batace komai ba ta koma ta lalubo mayafi cikin kayanta ta fito,suka jera zuwa cikin gidan. Babban gini ne,don yadan fi nasu girma da kayan alatu,sanda ta shiga ta samu matar gidan a falo,ta karbeta da fara'a,saidai tunda ta gaidata ta rasa me zata cemata. "Ban gane fuskar taki ba,ko kanwar amaryar abbas ce?" Qas tayi da kanta tana jin nauyi yana kamata,saita girgiza kai alamun a'ah "Ko amaryar ce da kanta?" Saita daga kai alamun eh,matar ta maida kanta sosai tana kallon widad din sosai,abbas data sani,abbas dake da.babbar mace kamar hafsat yaje ya auro wannan qwailar?,lallai Allah mai iko,sau tari mazan da suka fiya izza da kuma jin kansu daga qarshe haka suke qarewa,har gwara wannan din,kyakkyawa ce data amsa sunanta,komai nata mai ban sha'awa da daukan hankali,nan gaba kadan idan ta ida zama cikakkiyar mace lallai ba shakka sai an kalleta an qara,dole hankalin hafsat din ya tashi,amma a fili sai tace da ita "Ma sha Allah,Allah ya bada zama lafiya kinji amarya" bata iya amsa mata ba,sai shuru data sakeyi kawai kanta a qasa,gaba daya bata jinta a sake,tun asali dama ita din bamai saurin sabo bace,tana da wuyar sakewa da baqin fuska,don haka bata wani jima ba ta miqe tace zata tafi "To ina zuwa" ta fadi tana miqewa ta shige ciki,ranta da zuciyarta fal mamaki,ba jimawa ta fito da wasu kayan barci set uku ta bata,hannu biyu widad ta saka ta karba sannan ta fito. A inda ta barshi ta sameshi,ya sake mata jagora suka koma ciki,tana ta kallon gate,ji take kaman ta fita ta miqe qafarta,suna shiga falon ta miqa masa kayan kamar yadda takewa ummu a gida idan an mata kyautar abu "Gashi" ta fada tana ajjiye masa kusa dashi,dai dai lokacin da ledar ta zame,matan dake jikin takardar sanye da irin kayan baccin dake cikin ledar suka fito. Kusan tare suka dauke idanunsu shi da ita,taja baya da sauri qafafunta na sarqewa zata wuce ciki "Zonan" yayi kiranta yana karantarta,da baya da baya ta dawo,ita a lallai ba zata iya kallonsa ba,har abun yaso bashi dariya,ya dake da yanayin dakiyarsa da kuma miskilancinsa "Dauke abinki ki tafi dasu" "Banaso" ta fada kai tsaye tana maqale kafada,a mamakance yake kallonta "Bake ta bawa ba?" "Ni ta bawa,amma banaso,bana saka irinsu" dariyar da yaketa riqewa ta subuce masa,amma saita fita ta sigar murmushi "Zauna" yace da ita yanata kokawa da dariyar tasa,ta baya ta zauna har yanzu taqi yarda su hada ido dashi. "kinsan amfanin wadan nan kayan?" Fuska ta qara daurewa,tana sake tabbatarwa basu hada ido ba,kai ta girgixa masa ba tare da tayi magana ba "Oya....open your mouth,ban jiki ba" "Ban sani ba,kayan 'yan iska ne fa" tayi maganar tana narke fuska,kamar zata saki kuka. Wannan karon duk yadda yaso boye dariyarsa sai data fidda sauti,yayi qoqarin daidaita kansa,da gaske ta jahilci aure,da alama aiki je jajur a gabansa a kanta,bai tsawwala sai ya samu komai daga gareta ba,amma aqalla ta gama sanin meye auren kansa,don da alama batasan meye shi ba. "Kwashesu ki tafi" ya bata umarni a taqaice,ta baya ta zuro hannunta ta jawo ledar zuwa gabanta,sannan ta miqe da sauri sauri tayi dakinta. Tana shiga ta jefa ledar saman sofa bed tana zumbura baki kamar zata fashe,ledar ta qarasa yayewa kayan suka fito sosai,bata gama kula da hotunan jiki bama sai yanzu,ta qarasa tana daga kayan saita jefar zuciyarta a a cushe "Lallai matar nan ma 'yar iska ce ashe itama,don me zata bata wadan nan kayan?" Hadasu tayi ta cukuikuye ta jefa cikin sif,ta koma saman gado ta lafe a cikin bargo abinta,idanunta ta rufe,tana fata bacci ya dauketa tun tana iya jin motsinsa,basai waje yayi shuru ba. °°°°°°°°°Washegari ma haka ya fita,bai tsaya yin breakfast ba,yauma ita dinma kamar jiya,bayan ta gama 'yan gyare gyarenta da zata iya,saita dawo bakin window din falon ta zauna,lokaci lokaci tana yaye labulen tana leqa farfajiyar gidan,abinda ya tayata zama kenan,duk da yace mata tana iya shiga cikin gidan ta zauna a can,kota debe kewa,amma kasancewarta mara saurin sabo taji gwara tayi zamanta a nan har zuwa sanda ya dawo gida. To tsahon kwanaki biyar kusan haka rayuwar ta dinga gara musu,da safe idan zaya fita aiki zai sameta ne a falo,sabida yafi dakinta haske,zatayi masa a dawo lafiya bayan ta gaidashi,ya ajiye mata kudi ya kuma tambayeta bata da matsala,sannan ya mata sallama,takan bishi da idanu tana jin kamar ta bishi,wani lokacin yana ankare da ita,wani zubin hankalinsa yayi gaba,zata gyara dakinta data fara sabawa dashi,ta gyara falo ta goge shi tasa,duk da cewa tana daukan lokaci kafin ta gama,amma yana kintsuwa,kyan sharar nata da gyaran nata yake gani,saboda tafi hafsat nesa ba kusa ba, at least ita bata barin qura ko datti,sabanin hafsat din da ko ina a birkice yake,duk da suna da komai a store,to amma bata taba dora girki ba,yana sawa a kawo mata abinci,idan ya dawo tana cikin falon,amma wata qurya ta daban,a can zata zauna ba um ba um um,tana kallonsa kawai,duk da tana buqatar hira da wanda zatayi hira dashi,sai idan yaga tana gyangyadi kota gaji zai rakata ta kwanta ya dawo falo yaci gaba da sabgoginsa kafin ya tattara shima ya wuce nasa dakin. Duk sanda tsautsayi yasa ta farka cikin dare kuwa da qyar da sudin goshi take komawa baccin,saboda dan banzan tsoro,a rayuwarta bata taba kwana daki ita daya ba sai a wannan karon. Bangaren hafsat kuwa kullum a rana saita kirata,ta tambayeta me ya faru a jiya,me yake faruwa a yanxu,amsa kawai take buqata,tana ji zata katse wayarta,saidai idan weedad dince tabi bayan kiran tace a bata su mimi. Zuwa sannan fa fara jin dadin wayarta,da kanta da kanta ta koyi yadda ake sarrafa abubuwa da dama a cikinta,ta dauko games kala kala da suke debe mata kewa sosai,wannan yasa dogon wunin kadaicin da takeyi ya ragu sosai. _wannan kenan_ *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});