Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,307 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

taci,tana gama cin ta koma ta kwanta "Falo zaki fito ki kwanta,bazan barki ki sake kwanciya ba" "Ki qyaleni kawai ummu,tunda abba baya sona" ta fada da yanayi na quruciya tana kuma sake sakin kuka,baki ummun ta saki,tana magana kamar wata babba?,duk yadda taso ta fiddota amma taqi sai kwanciya. Koda aka fara dawowa daga idi tuni gidan ya fara cika da jama'a kamar yadda aka saba duk shekara,jikoki sun fara hallara,kowa fuskarsa da zuciyarsa cike da walwala da kuma farinciki,lokacin sallah lokacine na farinciki,amma wannan shekarar banda widad din,don kuwa duk budurin da akeyi tana kwance a qule a daki,da yake tana da kirki qwarai da son yara qananu,kowa yazo sai yace ina widad,saidai ummun tace bata da lafiya tana daki tana bacci. Duk yadda jikokinta ke karakaina a falon amma rashin walwala da fitowar widad din sai taji komai ma baya tafiya dai dai,maganar mahfood din taji itama ta soma fita mata a kai,gwara abar zancan,idan yaso a gwada bata wani,duk da abban nata ya gaya mata ita din bata son auren zumunci,to amma maiyuwuwa ta haqura idan aka gwada mata wani indai jininsu yazo daya,da wannan maganar a ranta tayita dakon shigowar alhaji don suyi maganar ita dashi. Bai samu shigowa gidan ba sai yamma liqis,zuwa lokacin manyan yayyensu maza dake sa mota sun debi yaran gidan da yawa zuwa guraren wasannin sallah da shaqatawa,gidan sai yayi shuru,sai dai daikun yara dake shigowa su fita,har sannan widad din tana daki a kwance,duk da tulin kayan sallar da take dashi bata sanya ko guda daya ba bare ta fito. Sai data gabatar masa da abinci yaci ya qoshi sannan ta fara magana dashi,yayi shuru yana sauraren ta har ta gama bayananta gaba daya,sannan yayi gyaran murya yana dubanta....... *_TOFA,TAFIYAR BA'A FARA BA,KO SHIMFIDA BAMU GAMA BA_* *_INA SAKE TUNA MUKU,IDAN KIN KARANTA HANGEN DALA,TO TABBAS SHAFAR MAI NE,WANNAN TAFIYAR TA FISHI ZAFI AMFANI DA KUMA DARUSSA_* *_LABARI NE DAYA QUNSHI TSANTSAR KISHI,KAIDI MUGUNTA DA KUMA SIHIRI_* *_MUGUN TAKU IRIN NA BAQAR KISHIYA_* *ZALLAR RAYUWAR GIDAJENMU TA GASKE* *MADARAR SOYAYYA MAI TSUMA ZUCIYA BURGEWA DA BARWA RAYUWA DARASI* *GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN* 0022419171 Maryam sani ACCESS bank *Saiku tura shaidar biya ta nan* +234 903 318 1070 *Masu tura katin waya kuma zasu tuntubi wannan number* 09166221261 *Yan nijer zaku tuntubi wannan number*🇳🇪🇳🇪 +227 90 16 59 91 *Thanks for choosing us* *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 06 "Gaskiya ne,kema kinzo da naki hanzarin,sannan a zahiri cikin musulunci babu auren dole,duk da shi mahmudu yana ganin kamar gata ne zaiyi mata,kuma hakan shine dai dai,to amma kuma duk da haka tana da damar da za'a bata zabi,iyaka idan aka duba ya zamana akwai kuskure ko rashin dacewa a ciki sai a soke lamarin",tana tausayin widad,tasan akwai maqiya da magauta fal cikin rayuwarta,shi ya sanya take a tsaye ga duk wani abu da zaya cutata mata. Bangaren widad kuwa haka ta yini ta kwana,ummu nata dakon zuwan mahaifinta suyi magana da alhajin,bai shigo gidan ba sai a washegarin da azahar,akayi sa'a alhajin shima yana nan amma yana shirin fita. Shuru abban yayi sanda alhaji ke masa maganar gami da bashi umarnin janye wancan qudurin nasa "Alhaji,naso ace an hada abun nan saboda a qarfafa zumunci,sannan yanzun bansan da wanne ido zan kalli isma'il ba(mahaifin mahfood)" murmusawa alhaji yayi "Akwai dangi da yawa,ba lallai sai mahfood ba tunda jininsu baizo daya ba,kada azo ayi abinda za'a zo daga baya ana dana sanin aikata shi,isma'ila kuwa shi da mahfood din kabar komai a hannuna zan magana dasu" kansa a qasa amma ransa a matuqar bace ya amsawa da alhaji,gami da yi masa godiya da fatan samun qarin shekaru masu albarka da lafiya me dorewa. Ummu da kanta ta shiga dakin inda widad keta fama kwanciya don yi mata albishir,a kwancen ta sameta,ta janye rufarta tana cewa "Tashi......ruwa sarkin kwanciya" sake curewa tayi waje daya tana turo baki gaba,don har ta gaji ma da kukan "Nace ki tashi hakanan, kwanciyar ta isa,maganar aure ce an janyeta an fasa" da sauri ta waiwayo tana kallon ummun gami da jin fitar maganar daga bakinta kamar almara,ko kuma tayi hakanne don ta tashi ta sake?,babanta fa?,wanda baya fadin abu ya canja,wanda baya magana ya sabata,tsayayyen akan duk abinda ya sakawa ransa zai aikatashi,to amma kuma......ummu bata qarya sam sam tasan halinta,fadi da cikawa ce,sannan yadda take qaunarta ta tabbatar ita da alhaji ne suka aikata hakan,sai kawai ta bugo wani tsalle ummu bata ankara ba sai jinta tayi a jikinta ta dane mata wuya cikin madaukakin farinciki. Murmushi ummu keyi tana jin farinciki cikin ranta itama,tasa hannunta tana banbanreta a jikinta tana cewa "Zaki qarasani 'yar nema,ashe duka iskanci ne,mitsitsiyarki dake wai kinsan meye auren dole,maza saiki sauka ki shiga bandaki ki wanka ki shirya ki shiga cikin 'yan uwanki" ummu kuwa bata kai qarshen zancan ba ta dire sai bandaki,tayi wankanta sarai,akwai kayan dama da taketa cin burin sakasu,yau kuwa zata gwangwaje kwalliyarta,latifa ta zuba mata abinci taci da kyau,sannan ta tsala kwalliyarta cikin wani lace mai azabar kyau da tsada da ummu ta dinka mata ita kadai,ta zauna ta tsara kwalliyarta dai dai da shekarunta da kuma iyawarta,sai gata ta fito dagwas dagwas gwanin kyau. A falo ta samu ummu tare da baqin da suka fara zuwa mata yawon sallah,wanda duka 'yan uwa ne da surukai,batulu ce matar baban widad din,haka suke rabawa duk sallah,wata zata fara zuwa gaida ummu dayar ta zauna a gida,washegari ko wata washegarin sai dayar tazo. Jakarta ummu ta kaba ta zuba mata sababbin kudi 'yan biyar biyar,duk da tasan halin kayarta,qila sai a gama yawon sallar a ci a cinye bata kashesu ba,daga qarshe dasu da wadanda ta samu duka dawo mata dasu zatayi "Ga barka da sallah ta nan" rungume ummu tayi tana dariya cikin farinciki "Na gode ummu" sai a sannan ta waiwaya ta rusuna kadan tana gaida batulu. Can qasan zuciyarta maqare fal da baqinciki da takaicin yarinyar,amma a saman fuskarta kadaran kadaham,tayi qoqarin gyara mood nata ko don ummu dake wajen ta amsa mata "Yammatan ummu,lafiya lau sai ina?" "Wajen anty madina zani" ta amsa mata tana yin gaba,duk da qarancin shekarunta,amma kwanyarta na iya tuna wasu abubuwan da suke gudana tsakaninta da matan baban nata,suke kuma kan gudana din,shi yasa dai dai da wuni guda bata marmarin zuwa gidan nasu bare ayi batun kwana,ummu ma ba zata bari ba,koda kuwa babanta yana da muradin hakan. Kamar ko yaushe chamber ta hadu a sassan anty madina,shigarta wajen kallo ya koma kanta,masu tankwa da yabawa nayi,masu baqinciki suna nasu aikin,ko meye saman fuskarka kusan ta saba dashi,uwa uba ga quruciya da bata sanyata daukan abubuwansu da muhimmanci,fatanta da burinta kawai ta shiga cikin 'yan uwanta ayi mu'amala da ita kamar kowa. Wunin ranar gaba daya cikin walwala ta yita,sai takejin kamar wadda aka daddaure ayau ta samu 'yanci,sai dare ta dawo sassan umnu,tana gefanta tana bata labarai na abinda suka faru,kowa cikin jikoki na zaune saman carfet suna cin abinci amma ita na nanuqe da ummunta,tare suka ci abinci kafin dare ya miqa su wuce dakin kwanciya. Sai bayan isha'i a ranar alhj mahmud ya koma gida,har lokacin akwai sauran damuwa da bacin

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});