Chapter 9
Chapter 9
sanyo qafafuwansa. Idanu yake bin widad din dashi,yaji kalamanta guda biyu na qarshe,zallar bacin rai ne kwance akan fuskarsa,ita kanta suna hada ido da abban nata ta sadda kanta qasa gabanta yana tsananta faduwa,mahfood kuwa miqewa yayi yana masa sannu da zuwa "Zauna mahfood......me naji kina fada widad?" Tsoro da firgici suka hanata yin koda qwaqwqwaran motsi bare ta amsa shi,cikin tsawa ya sake maimaita mata tambayar,saita ida rikicewa gaba daya,ta kuma saki kuka a lokaci guda,saboda sam sam bata saba da irin wannan tsawar ba. "Dan uwanki kike gayawa bakiso saboda baki da kunya?,wato kin fara girma kenan widad?" Ya fada cikin mugun fada da kuma daga murya,sautin muryar tasa da ya isarwa da ummu saqon akwai abinda ke faruwa a falon,taji kuma ta kasa nutsuwa saboda kama sunan shalelenta da taji anyi,saita yunqura ta miqe tana duban na'eema "Ki qarasa hada muku kayan waje guda ki maida daya dakin kafin gobe gidan ya sake cika,ina zuwa" ta fada tana takawa a hankali saboda dan ciwon qasa da take fama dashi lokaci lokaci. Isowarta wajen kadai tafahimci abinda ya faru,fada sosai abban yake zuba mata,da alama ransa ya baci sosai "Mahfood dan uwanki ne,da kike cewa kuma bakya sonshi gwara ki koya tun wuri,don baki da miji sai shi,shi zaki aura ki jini da kyau" ya fada yana kama kunnensa da hannunsa guda daya "Tashi ki bani waje" ya fada a tsawace,ta gudu ta miqe tayi hanyar dakinsu fuskarta jiqe da hawaye,saman gadonta ta fada wanda ba kasafai ma take kwana a dakin ba,koda yaushe tana maqale da ummu,a dakinta take kwana,koda tana wajen alhajin to itakam tana dakin nata,haka zata hada duka filallukan dake saman gadon ta qudundune a ciki saboda shegen tsoron da take dashi,bare ma ba kasafai ummun ke barinta ba,wani lokaci ma bata sanin bata dakin idan baccinta yayi nisa ko kuma nauyi. Kan mahfood a qasa sanda abba ke bashi haquri "Nasan harda quruciya abba,har yanzu shekararta sha hudu" "Da kuma sakarci ba" "Ayi haquri" ya sake fada kansa a qasa,sannan ya miqe yayi musu sallama ya fice daga sassan ummun yace zai shiga cikin gidan su gaisa da sauran mutane. "Ka dinga bin al'amarin nan a hankali mahmudu,wannan fadan duka ba shine ba" ummu ta fada bayan dukkaninsu sun zauna "Ummu abunne yake dauren kai,anata cewa quruciya ce,to amma tana sake girma tana sake qinsa?" Kai ummun ta jinjina,ita kanta bataga na meye abba din sai ya matsa har haka ba,shi zumuncin da yakeson a qarfafa a kuma sake qullawar ai ba dole sai ta hanyar hada aure ba,inda akwai wata diyar gareshi wadda tadan tasa kamae widad din ma ita zaifi mata sauqi ya maida alqawarin kanta,bata qaunar wannan rikicin da aketa yi da widad din "Kasan haduwar jini ne,idan kuma Allah bai sanyata tsakanin bayinsa ba babu yadda za'ayi" "Haka ne,Allah yayi mana mafita" "Ameen ya hayyu ya qayyumu" ummun ta amsa masa,sai ya miqa mata babbar jakar da yasa aka shigo da ita,wadda ke shaqe da kayan sallah na mutanen da ya saba yiwa duk shekara,wanda yaran gidanne 'ya'yan qannensa da suke sa'annin widad,wasu kuma qasanta a shekaru,ga kuma nata na musamman ita da widad din da alhaji "Alhajin baya gida ne?" "Kasan yau daren sallah,suna can fadar mai martaba,har sai an sanar da ganin wata sannan" kai ya jinjina,don kusan al'adar sa ce duk shekara "To Allah ya dafa mana" ya amsawa ummun. Kuka take sosai da hawayen daya fara jiqa pillow din da take kwnace akai,juyin duniya na'eema tayi ta tashi tayi haquri ta dauki abincinta taci amma ko kulata batayi ba,sosai take jin qin mahfood din cikin ranta,ko sau daya bata taba jin tana sonshi ko yana burgeta ba,yana da kirki ta sani,amma ita ba wani magana datayi kama data aure a tsakaninsu da take jin zata yiwu. Har abbanta ya tafi tana kwance tana kuka,ummu na falon bata motsa ba,duk da na'eema ta gaya mata,bataso taje taga yanayin da take ciki zuciyarta ta karye ta gaza bata qwarin gwiwar yiwa mahaifinta biyayya,wannan yasa tayi zamanta a falo,duk da zuciyar da hankalinta na kanta. Duk wanda ya shigo nemanta sai tace masa kawai tayi bacci,wasu su zauna suyi hirarrakinsu wasu kuma su wuce,tana nan zaune har qarfe goma na dare,zuwa sannan juriyarta ta qare,sai ta miqe ta shiga dakin da kanta. Tana kwance rub da ciki har yanzu,saidai ba zaka iya tantance bacci take ko idanuwanta biyu ba,ta qarasa a hankali tasa hannu tana taba kanta gami da kiran sunanta,sheshsheqar data sauke hadi da ajiyar zuciya ya tabbatar mata idanuwanta biyu "Meye haka wai widad?,tashi mana" ta fadi tana qoqarin dagota ta zaunar da ita,sanda ta kalli fuskarta sai zuciyar ummun tayi rauni,kallon marainiya takewa widad shine dadin abinda yasa batason komai ya sameta mara dadi,yarinyar da batasan dumin uwarta ba?,gaba daya fuskar tata ta tashi ta kuma yi jazur da ita abinka da farar fata "Kukan kike har yanzu kamar wadda akace mata zata mutu?,tashi ki wanke fuskarki kici abincin naki" "Ni banaci" ta fada muryarta na rawa hawaye yana sake barke mata,sai kawai ta fada jikin ummun tana sakin sabon kuka,har cikin ranta ummu takejin kukan,sai ta fara lallashinta,da qyar ta ciyo kanta taje ta wanke fuskar ta sanyata a gaba taci abincin,da qyar tayi cokali biyar tace ta qoshi,ummun taso sanyata a gaba su wuce dakinta ta kwana kamar yadda ta saba amma tace anan zata kwana,tunda ga na'eema,sannan Aafiya ma yau a nan zata kwana,dole ta rabu da ita tabar musu dakin bayan ta ja mata kunnen kada ta sake irin wannan kukan,ta kwantar da hankalinta kuma. *_W A S H E G A R I_* Kamar yadda suka saba kusan kowa da kowa ake tafiya sallar idi a gidan,akwai wadatar ababen hawa,kowa zai diba iya mutanen da motarsa zata iya dauka,tun sassafe kowanne sashe suke tashi yaran suyita shiri,iyayen kuma suna qoqarin qarasa abincin sallah wanda idan an dawo saga udi za'a dira akai a fara ci da kuma rabo,to hakanma wannan karon ta kasance,har sassan ummun hayaniya ce ke tashi,saidai banda widad dake nannade a bargo,ko motsawa batayi ba bare ta shirya,sunyi sunyi ta tashin amma taqi kula kowa,ummu kuma tunda ta fito da asuba ta tadasu sallah bata kuma fitowa ba,sai alhaji ya gama shirin idinsa. Karo na biyu latifa fa dawo,wadda itama ta shirya fes da ita cikin dinkin sallarta,duk sallah sai an mata dinki kamar kowanne yaro ko jika dake gidan,dinkinta masu kyau da tsada har kala hudu ko uku "Widad din ummu,kiyi haquri ki tashi ki shirya,kinga kowa ya gama shiryawa,yanzun nan zakiji an fara tafiya"ta fada cikin lallabawa,bakam tayi kamar bata a wajen,duk iya dabara da hila ta latifa haka tayi ta haqura,daga qarshe dai haka suka tattara suka tafi sallar suka barta. Bayan ficewarsu ummu ta fito "Ja'irai,tunda naji shuru nasan sun tafi,kafin su dawo su hana mutun sakat" tayi maganar tana tura qofar dakin,sai idanunta ya sauka kan tudun bargon dake kan gado,cikin ranta zuciyarta ta bata mutum ne,sai ta qarasa tana yaye bargon. Salati ta saka ganin widad din kwance tana sharbar kuka "Na shiga uku ni laila?,wai dama baki haqura ba widad?" Hankalin ummun ya tashi sosai,haka ta sanyata a gaba sai data tashi tayi wanka ta kuma zuba mata abincin safe
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155