Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 22

Chapter 22

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,291 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

maka alkhairi,tunda nasan zuwa yanzu ko kudin ma ka rasasu ba samunsu zakayi ba,gwara ka tsira da lafiyarka da mutuncinka" "Dalla malami sakeni,wallahi yau sai naga wanda ya tsaya masa" ya fadi yana kumfar baki,maganar tasa ta sake hasala abbas,saidai bai nuna hakan ba koda a saman fuskarsa,yana ji ya zama wajibi ya bashi tarbiyya da bashi da ita,sai ya juya ga tsahon "Kada ka sake bashi haquri baba" hannu ya saka a aljihunsa ya fidda dubu uku ya miqa masa "Hau mashin dinka ka tafi,Allah ya tsare" zaburowa yayi yana fadin "Idan ka barshi ya tafi rigimar nan ta koma kanka wallahi" "Na karba"ya amsa masa yana sawa tsohon muqullin babur dinsa ya kunna masa,dai dai sanda motar 'yan sanda ta iso,hakan ya baiwa tsohon hanyar wucewa,yana tafe yana jerantawa abbas din addu'o'in samun albarka da gamawa da duniya lafiya. Matashin bai fahimci waye abbas din ba sai da jami'ai suka cika hannu dashi shi da dan sandan dake goya masa baya,sai a sannan ya nemi russunawa ya fara roqon ya saka a sakeshi,ko kallonsa baiyi ba ya dubi Samuel "Ku sakayamin su a bayan kanta saina nemesu,mato ya tuqa motarsa a kaita station a ajjiye" "Consider it done sir" ya fada yana saluting nashi. *MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA* *DAUD'AR GORA* Billynabdul *KI KULANI* Missxoxo *IDON NERA* Mamuhghee *RUMBUN K'AYA* hafsat rano *A RUBUCE TAKE* Huguma *ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN* 0022419171 Maryam sani Access bank Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number 09033181070 *MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU* 09166221261 *YAN NIJER ZASU TUNTUBI WANNAN NUMBER* +227 90 16 59 91 *Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*🙏🏾🙏🏾 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *_Arewabooks:huguma_* Page 14 Ta tsakiyar mutane da suka cika a wajen 'yan kallo ya samu ya ratsa ya koma motarsa,yabar mutane suna ta tattauna maganar,da yawansu hakan da yayi ya sake burgesu saboda diban albarkar yaron tayi yawa,yan bani na iya kuma na ganin baiken hakan,suna ganin kamar yayi amfani da qarfin ikonsa ne. Abinda ya faru akan hanyar ya qarawa kansa zafi,ransa ya dinga sosuwa duk sanda ya tuna girman shekarun mutumin da abinda qaramin yaro yayi masa,a nutse yaci gaba da tuqinsa har ya shiga unguwar tasu,qofar gidansu yayi parking,yana shirin fita a motar sukaci kacibus da qanin mahaifinsa suka tsaya suna gaisawa,wannan yaja masa jinkirin shiga gidan,sai bayan la'asar sa wasu 'yan mintuna bayan sunyi sallar la'asar a masallacin qasan layinsu sannan suka taho tare da kawu hassan din,yanata masa godiyar uban gudunmawar daya bayar na auren diyar kawu hassan din,har suka iso gida,kawun ya shige gidansa dake jikin gidansu abbas din. Tun a harabar gidan ya fuskanci kamar gidan yau ba iya mutanen gidan bane kawai a cikinsa,muneera dake wanke alayyahu cikin famfon dake baiwa shukokin da suka qawata harabar gidan ruwa ta amsa sallamar tasa gami da gaidashi ya amsa mata,har yaa taka zuwa gaba sai ya tsaya cak ya waiwayo ga muneera "Hajiya na ciki ne?" "Eh sallah takeyi" fasa shigar yayi,saboda hayaniyar daya danji,a yanzun kuma ba abinda yake buqata sai zaman shuru,don haka ya juya akalarsa zuwa sitting room din baqi dake harabar gidan daga gefe "Idan ta idar ki gaya mata na shigo,amma zan dan kwanta kadan" "To uncle" ta amsa masa tana daukan kwandon alayyahunta tayi ciki,shi kuma ya murza key din daya gani a jiki ya bude falon ya shiga. Yasan tsaf falon yake,duk da ba shigarsa akeyi akai akai ba,babu inda hajiyarsa ke bari da qazanta cikin gidanta,koda kuwa ba'a amfani da wajen,bata lamutar datti ko qura,wannan yasa babu haufi ya nufi daya daga cikin kujerun Three sitter ake falon yayi kwanciyarsa,ya miqe bayansa sosai saman kujerar yana lumshe idanunsa hadi da sakin ajiyar zuciya,yanason baiwa kwanyarsu hutu,bayason tuna komai da zai dameshi. Minti kusan goma yana a haka,yanata kokawa da tunane tunanen dake kwanyarsa,saidai surutai da 'yan iface ifacen dake gilamawa kadan kadan ta wajen nadan damunsa lokaci bayan lokaci,bai wani dameshi da yawa ba,wannan ya sanya yaci gaba da barin idanuwansa a rufe. Gigitaccciyar qarar data cika harabar gidan ta sanyashi durowa daga saman kujerar ba tare daya shirya ba,muryar nada matuqar kaifi da zaqin da zata iya huda kunnuwan duk wanda ke wajen,zaman dirshan yayi saman kujerar yana rufe idanunsa jin yadda qarar taqi tsagaitawa,ya rintse idanunsa yana jin yadda kansa ke sara masa sanadiyyar qarar,tsaki yaja dabmugun qarfi ya kuma miqe a fusace ya nufi qofa yaje yaga wanda ke qarar kamar wanda ake cirewa rai. A hankali ya yaye labulen ranshi a bace idanuwansa a farfajiyar gidan yana son ganin wanne tashin hankalin ne haka yake faruwa,idanunsa suka sauka a kanta,a lokacin ta jima da fara tsalle tana runtuma ihu hadi hadi da hawaye face face saman fuskarta,tuni 'yar hular dake saman kanta tayi nata waje,gashinta da koda lafiya lau yake sabulewa daga jikin ribbom ya baje abinsa iska tana daukarsa. Idanunsa ya zube mata,yana qare mata kallo,me ya sanyata wannan tsallen a gigice?,kunama ce ta harbeta ko maciji ta gani?,saidai kunamar,don ya tabbatar cikin gidan nasu ba za'a samu maciji ba,sai ya rasa me ya kamata yayi,ihunta yana sake cika masa kunne,baikai qarshen tunaninsa ba hajiya ta iso wajen da hanzarinta ita da muneera,a rude take qoqarin kama widad tana tambayarsu nujood me ya sameta?,sai ya harde hannayensa a qirji,ya zauna a hankali saman hannun kujerar dake daura da qofar yana kallo da sauraren abinda yake faruwa "Kyankyaso ne ya shigar mata riga" idanunsa ya lumshe yana jin wani haushinta yana cikashi,kyankyason takema wannan kamar wadda taga mutuwa?,bai bude idanun nasa ba yayi shuru yana sauraren muryar hajiya tana cewa "Kyankyaso?,riga kuma?,garin yaya?" "Musaddiq ne ya saka mata(qanin nujood dake binta)" "Ashsha musaddiq baka kyauta ba" hajiya ta fada tana qoqarin kakkabe mata rigar. Hannu daya ya sanya ya sauke labulen,ya kuma tura qofar da qafa sannan ya koma saman kujerar ya kwanta kamar dazun yana sake jan tsaki,ko a ina hajiya ta samo su suka cikawa mutane gida da hayaniya?. Still idanuwansa suna rufe,yana jinta cikin sheshsheqar kuka tana gayama hajiyan yadda abun ya faru,ta yima musaddiq fada sosai sannan ta hada kansu suka wuce cikin gidan. Ana kiran sallar magariba ya wuce masallaci yayi sallah sannan ya shiga cikin gidan,zuwa sannan babu kowa daga hajiyan sai muneera "A'ah,shigowar magariba kuma yau kayi abbas?" "Ina nan tun sanda wannan tsanyar ke ihu" dan shuru tayi na sakanni,sai kuma ta saki murmushi "Wai widad?,aikin musaddiq ne wallahi" "Musaddiq din muhsin wai?,dama sune?" "Sune,a nan hajjaa ke barinsu,idan ta taso daga makaranta take daukansu,widad kam ai bata da hayaniya ko kwaramniya,shaqiyancin musaddiq dinne,yasan yadda take tsoron kyankyason ya saka mata shi" kai ya jinjina kawai ba tare da yace komai ba,sai a sannan hankalin hajiya kuma ya dauku ga fuskarsa,ya akayi har ya shigo gidan tun yamma bai nemeta ba,fuskarsa ta nuna akwai damuwa tattare dashi "Allah dai yasa lafiya" ta fada bayan sun gaisa,furzar da iska yayi daga bakinsa,ya motsa baki zaiyi magana ta datsi numfashinsa "Kada kacemin babu komai" shuru ya ratsa falon na wasu

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});