Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 45

Chapter 45

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,311 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

jama'ar da suka halarci wajen suka haida,labarin kuma ya kai har cikin gida ya fara yawo a tsakanin mata. Dai dai lokacin widad na zaune tsakiyar anty deena da anty warisha,sai sharban kuka takeyi,duk yadda sukayi da ita tayi shuru bare a samu ayi mata kwalliyar daurin aure taqi,sai suka sakata a gaba kawai suna kallonta. Anty madina ce tayi sallama ta tana turo qofar dakin,dakin da babu kowa sai su ukun kawai,warisha ta amsa sallamar anty dina dake danna wayarta kai kawai ta daga ta kalli anty madina "A'ah,na zata zanzo na tarar kun gama,an gama daurin aure fa,angwayen ma yanzun zasu shigo za'ayi hotuna" "Inafa akayi kwalliya,kin ganta nan ko kayan taqi ta saka ma,ni bansan me yake damunta ba" anty deena ta fada tana ajjiye wayarta a saman madubin dakin. "Ashsha,haba widad,mene hakan?" Hawayenta taketa qoqarin tsayarwa ta hanyar shareshi da hannuwanta amma hakan ya gagara,wani irin bacin rai tsoro da kuma takura takejin kanta a ciki,wanda ita kanta batasan dalili ba,kawai batason barin gida ne,hakanan shi uncle abbas din ta yaya za'a wani ce shine mijinta tana zaman zamanta?. Anty madina ce ta cewa su deena din su basu waje minti biyar kacal,nasu musa ba suka miqe,anty deena ta dauki mayafinta mahadin lace din jikinta ta fara yin gaba,don dama ta fara gajiya da zaman lallashin widad din,wadda bata da alamun daina kukan. Cikin mintuna goma sai ga hawayen ta tsaya tas,anty madina kuma ta shiryata da kanta,hatta da undies ita ta bata ta saka,tana jin kunya tana nonnoqewa,ta shiryata cikin wani lafiyayyen lace fari da ummu ta kashe maqudan kudade wajen siyansa,aka kuma shirya masa nutsatsen dinkin doguwar riga,gashinta da yasha gyara ta tufke mata,sannan ta qawata mata kanta da sarqa ruwan gold da aka sanyawa saman ka,wanda kusan al'adace ta asalin yarensu,hannayenta sun sha warware masu kalolin gold masu asalin tsada,haka yatsun hannunta kowanne zobe ne bibbiyu daga tsakiya. Fes widad din ta fito,asalin quruciya da qaranci shekarunta na sake bayyana kansu,wanda ya cakuda da qyallin amarcin da akewa kowacce mace feshinsa,komai kyau ko muninta,indai sunan nan na amarya ya hau kanta. Kiransu anty deena tayi sanda taji hayaniya ta fara cika gidan,muryoyin maza na tashi,alamu dake nuna tawagar angwaye ne suka shigo gaisawa da surukansu,daga inda take sai ta dinga jin kamar an daureta,gabanta ya tsananta faduwa,wani tsoro yana shigarta,kanta a qasa,nutsuwa ta musamman irin wadda duk wanda yasan widad din bai santa da ita ba ta saukar mata. Shi daya ne cikin motar kwance a seat din gaba,ya dage dukka baqaqen gilasanta,da hular da kuma babbar rigar duka ya ciresu ya jefa seat din baya,ta cikin motar yana iya hagen kai da kawon jama'a,ciki harda gungun abokansa da suka masa karar da ko auren farko bai sameta ba. Amatsayinsa na jimi'in tsaro,duba daya yayi musu yana daga kwancen ya fahimci shi suke nema,yasan zancan bai wuce ace su shiga cikin gidan,abinda sam bashi a tsarinsa kenan,saboda yana kallon haka a mazaunin keta haddin shari'a,tu dazu ya shigo ya kwanta,ya kuma gargadi Samuel kada ya gayawa kowa yana ciki. Idanunsa ya janye a hankali daga inda yake kallo sanda yaji ana knocking qofar motar,fuskar suraj yake hangowa wanda yayi wujiga wujiga saboda yawan al'ummar dake wajen,sai yasa hannu a nutse yana daga kwancen ya buda murfin motar,suraj ya sunkuyo yana sako kansa. Ajiyar zuciya ya sauke "Gaskiya baka kyauta mana ba,kaifa ake nema tun dazun,zaa shiga gaida iyaye da kakannin amarya,ga masu hotuna suna jira suma zasu wuce" kamar wanda baya son yin magana ya buda bakinsa "Duk da wannan uban jama'ar zamu kama mu shige musu gida suraj?" "To ya za'ayi,al'adace" kai ya girgiza "Ba dani za'ayi wannan aikin ba,idan ya zama dole ka sallamesu su tsaya iya waje,mu shiga koda mu uku ne muhsin yayi mana jagora iya sashen ummu kakarsa mu gaisa mu fito" dan hade rai suraj yayi,sai kuma ya saki dariya "Kai mutumina,anya ba kishin matarka ka fara ba?" Wani kallo ya watsawa suraj din "Waikai me yasa baka da girma saina jikinka,yarinyar da idan auren qauye ne na haifi kamarta?" "Allah yasa motsin gado ce,bar ganin allura,duk qanqantarta qarfe ce,any way.....banga laifinka ba,bari ina zuwa" ya fadi yana maida murfin motar ya rufe. Sai da yayi settling komai yadda abbas din yakeso sannan ya sanar dashi,hularsa ya dauka ya mayar saman kansa,ya riqe babbar rigar a hannunsa,yana jin ta masa nauyi,saboda rashin sabo da sanyata,tunda gaba daya aikinsa yafi alaqa da qananun kaya. Kamar jiransa maroqa da masu buga kakaki suke suka fara busarsu suna wasa shi,baisan a inda suka san muqaminsa da kuma muqaman da ya riqe a baya ba,duk da juniors dinsa da suke masa bodyguard hakan bai hanasu binsa da kide kidensu ba "Ka sallamesu don Allah" yace da suraj,saboda yadda yakejin kidan na haura masa har saman ka,sai da suraj din kuwa ya sallamesu da kudi masu tsoka sannan suka ja suka tsaya daga nan suna ci gaba da yagar rabonsu a hannun duk wamda suka fuskanci dan gaban goshin bikinne. Babban falon ummun cike yake da jama'a,saidai da yake yana da yalwa babu laifi ba'ayi cushewar da zaka fuskanci yawan jama'ar dake cikinsa ba. Duk da fargaba da kuma alhinin rabuwa da widad din tata hakan bai hanata qure ado fiye da duk wani bikin jikarta da za'a yi ba,ta cake cikin wani danyen lace purple color daya haska farar fatarta dake dan bayyana yanayin shekaru da suka soma hawa kanta. Muhsin ne ya gaya mata ga abbas nan zai shigo,don haka ta kira hauwa'u da batulu(matan baban widad) tace su rage mata jama'ar falon. Duk da jikinsu a mace yake saboda ganin irin hidimar da akeyi amma wannan aikin kam cikin karsashi suka yishi,saboda suma suna buqatar ganin mijin widad din sosai,cikin lokaci qalilan falon ya sake fili,ya zamana sai manya a cikin dangi suka rage,dai dai lokacin sukayi sallama suka shigo cikin falon su uku. Kamar yadda a tsarin zubi da halitta gami da kwarjini ya fita daban......hakanan adonsa da shaddar jikinsa ta banbanta data kowa,sai ya fito kamar wani wata a cikin taurari,qanwar ummu da sauran jama'ar dake wajen ke marabtarsu,har suka samu waje qasan carfet suka zauna bisa tsari na tarbiyya,sannan aka soma gaisawa. "Da gani babu tambaya,wannan na tsakiyar shine surukin namu ko?" Batulu da wani malolon abu ya tsaye mata a wuya ta fada,fuskarta kwance sa murmushin yaqe,kusan kowa a wajen sai da yaji banbarakwai,saboda ba ita ya dace tayi tambayar ba,ko banza ya kamata ace akwai kunya tsakaninsu,saboda a yanzun sune kamar copy na mahaifiyar widad. Murmushi suraj ya danyi,baisan dangantakar ta da widad ba,ya dauka abokiyar wasa ce,tunda suna irin haka,dalilin da yasa ya maida mata kenan cikin salo na wasa "Aah,nine fa,kingi batan dabo" "Allah ya sanya alkhairi,yasa anyi kenan,jikanyar tamu qaramar yarinya ce qwarai,sai anyi haquri da halayen quruciya da za'a yita gani,Allah ya bada zuri'a dayyi ba" qanwa ga ummu tayi hanzari katse doguwar maganar da batulu keson taja,falon sai ya game da addu'ar ameen ameen. Abbas din na shirin miqewa muhsin yashigo yana fadin ina widad din afito da ita,azo ayi musu hoto "Ya salam" yafada a ransa,me yasa muhsin zai masa haka,bashi da zabi illa yayi jiraye. Anty madina da anty deena ne suka fito da ita ta can

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});