Chapter 145
Chapter 145
wani irin tsoro ne keta mata tasiri,bayan ta gama ya tabbatar ta kammala komai na kwanciya,yayi tsaye hannayensa cikin aljihun wandonsa yana kallonta "Shikenan?,saida safe?" Kanta ta kawar gefe,tana jin ranta ya motsu,yanzun tafiya zaiyi wajen mummyn mimi,saita gyada masa kai a sanyaye,sannan tace "Mimi ba zatazo tayani kwanan ba?" Dan jim yayi kafin ya amsa "Sun wuce dakinsu kafin na fito,don't worry ki kwamta ki rufe idonki,yanzun nan zakiga safiya tayi, okay?" Saita gyada masa aki a hankali,tausayinta sosai yaji,yasan ko yaya batason rabuwa dashi,bare yanzun data saba da zama jikinsa kamar wata 'yar mage,ya sunkuya a tausashe yayi kissing dinta,ya juya zai kashe mata hasken dakin tace "Ka bari zan kashe" don batason duhun da zata zauna a ciki kafin bacci ya dauketa "Okay" ya furta can qasan maqoshi,ya juya a hankali ya fice a dakin yana waigenta. Idonta ta mayar ta lumshe tana jin ficewarsa,wani abu na tsaya mata a wuya,ta gwammace taci gaba da barin idon a rufe maimakon ta bude ta kalli hanyar da yabi ya fice din. Cikin mintunan da basufi qwaya biyu ba taji yanayin dakin ya fara sauyawa,kamar komai na dakin motsi yakeyi,ciki harda kujerar data kwanta a kan,zuciyarta tayi mugun bugawa, madaukakin tsoro ya mamayeta,kafin takai ga bude idanunta taji dukka wata gaba ta jikinta tayi nauyi,kamar wadda DANNAU ya danneta,ta kasa motsa koda dan yatsanta bare tayi yunqurin tashi daga inda take kwance.......... *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 95 Tayita qoqarin motsa wata gaba ta jikinta amma ta kasa,wata mummunar shaqa taji an yiwa wuyanta,abinda ya sabbaba mata numfashinta ya soma wahalar fita kenan,cikin gigita firgici da kuma tsoro ta soma bude idanunta a hankali tanason ganin waye a dakin?,waye yayi mata wannan aikin. Wayam......babu kowa a dakin,daga ita sai kayan gado labulaye zuwa frames a dakin. Idanunta ta wulga gefe,sai ya sauka ga bangon dakin da take fuskanta,wani irin motsi taga yana yi,yana kuma darewa a hankali,wani dogon hannu yana ratsowa har zuwa inda take kwancen,ta motsa bakinta da nufin addu'a amma komai ya gaza fita,idanun nata yana kan hannun da yaci gaba da ratsa bangon dakin yana qara shigowa hadi da ci gaba da shaqe mata wuya. Ci gaba tayi da kokawa da numfashinta tare da qoqarin ganin ta kira sunan Allah,tsahon wasu mintuna kafin ta samu ta fusgo addu'a da qarfi daga bakinta "Ya Allah..... innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta fada da qarfi,kalmar da tayi sanadiyyar yankewar komai,jikinta ya sake, bangon dakin ya koma dai dai,motsin da dakin yakeyi ya tsaya cak,ta miqe da mugun hanzari,ta nufi qofar dakin da gudu tana sake kiran sunan Allah da mabanbantan sunaye. Kai tsaye ta fada dakin abbas din ta maida qofar ta rufe sannan ta zube a wajen tana tokare bayanta da qofar kamar me shirin hanawa wani shigowa dakin,ya sulale ta zube a wajen tana riqe da wuyanta,saita fara karanta ayatul kursiyyu da qarfi,ko ina na jikinta yana wani irin rawa kamar me shirin ficewa daga hayyacinta. Ta jima a wannan yanayin tana karanta ayatul kursiyyu da dukkan addu'ar tsari da tazo bakinta,har sai da dukka yawun bakinta ya dauke,Allah ya saukar mata da wata nutsuwa,saidai har yanzu jikinta rawa yakeyi,tsoron dake tattare da ita ya ragu sosai,saidai a firgice take qwarai da gaske. Kusan awa guda kenan kafin ta samu kuka yazo mata,ta tattare guri daya cikin wani irin yanayi na tashin hankali,tana jinta ne tamakar a tsakiyar wani daji da babu gida gaba babu gida baya,ita daya qwal a sashen,ta ina zata iya fita tabar sassan?,ta baro wayarta a dakin da batajin zata iya taka koda qofar dakin ne bare tayi kiran abbas,cikin wannan yanayin taci gaba da zama a bakin qofar dakin,rabi kuka rabi addu'a,a haka ta qare darenta tsaf a zaune dungurgur har aka kirayi sallar asuba. A jikinsa ya dinga jin tunaninsa ya karkata a kanta,don haka ana idar da sallar asuba ya baro masallaci ya wuce sassanta. Kamar numfashinta zai tsaya haka taji sanda taji motsi yana buda sassan nata da key dinsa,ta qanqame jikinta guri daya tana sakin kuka sosai tana kiran sunan Allah,har ya buda ya shigo falon ya kuma duba dakinta bai ganta ba tana zaune a wajen ta kasa motsawa,mamaki ya cikashi ganin har bandaki ya duba,babu ma alamun ta shiga,don a bushe bandakin yake,sai tunaninsa ya bashi ya duba dakinsa,don haka ya fito ya nufi qofar dakin. Daya murda handle din yaji alamun a kulle take sai hankalinsa yadan kwanta,cikin ransa yana murmushin ya akayi ta canza daki ta koma nasa dakin?,sai ya gyara tsaiwarsa yana rayawa a ransa lallai yau zaiyi mata tsiya. Knocking yayi,widad dake zaune jikin qofar ta runtse idanunta tana jin kamar numfashinta zai dauke,ya sake qwanqwasawa murya can qasa ya kirayi sunanta,abinda ya bata qwarin gwiwar miqewa da hanzari ta bude qofar,batayi wata wata ba ta fada jikinsa,ya tareta da sauri cikin mamaki da tashin hankalin jin irin kukan data fashe dashi. A rude yake ta jero mata tambayar me ya sameta?,me ya faru?,menene?,amma ta gaza amsa masa tambaya ko guda daya,sai sake riqeshi da tayi da kyau kamar mai tsoron kada ya subuce mata,a haka tana jikinsa ya jata zasu koma dakin amma ta turje taqi,dole sai parlor suka dawo saman kujerar tana kwance a jikinsa tana gurzar kuka. Kusan minti talatin suna a haka sanann ya soma lallabarta,yace tayi sallah?,tace a'ah "Kije kiyi sallah sai kizo ki gayamin abinda ya faru" ko motsawa daga jikinsa qi tayi,sai a sannan ya sake experiencing tsoron dake tattare da ita,mamakin abinda ya haifar da irin wannan tsoron daga wajenta ya saukar mishi,duk da ya sani ita din matsoraciya ce,to amma tsoron nata baikai haka ba,hasalima ta fara sabawa da gidan,ta rage tsoron sosai. Sai shine da kansa ya rakata bandakin ya kuma tsaya tayi alwalar ta kuma yi sallar,ta hanashi motsawa ko ina,tana kwance a jikinsa wani irin zazzabi ya fara saukarwa jikinta,dole yaja duvet ya lullubesu ita dashi, hankalinsa gaba daya ya tashi,gashi tambayar duniya ta gaza ce masa komai,sai dan uban kukan da take masa.. Wani irin tsoro ke dawainiya da ita shi yasa ta kasa gaya masa,tana ji kamar idan ta fada masa abun zai sake dawo mata,don haka ta kasa cewa komai sai kukan,hankalinsa dukka a tashe yake,yayi lallashin duniya tayi shuru tunsa taqi fadin abinda ya faru amma ta kasa yin shurun,sai hawaye da taketa fitarwa,a haka har rana ta fara fitowa tana kwance a jikinsa saman gadon,a haka yayi azkar dinsa yana duban fuskarta wadda a sannan bacci ya fara fusgarta,wani irin zazzabi yana sake lullubeta. A hankali bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita,sai a sannan ya samu ya zare jikinsa ya tula mata pillows yadda zata tsammaci shine,ya miqe ya soma bincike gidan wai ko wani abun ta gani,tun daga dakinsa zuwa nata dakin,bandakunansu qasan gado kitchen ventilation dinta dako ina amma baiga komai ba,dole ya haqura ya wuce kitchen ya hada ruwan zafi yasha zuciyarsa cike da wasu wasi da tunane tunane. Sanda ta farka zazzabin ya riga yayi qarfi a jikinta,dole ya zare mata rigar jikinta ya jiqa towel ya soma rage mata qarfin zazzabin,ba yadda bai lallabata tayi wanka ya kaita taga likita ba amma taqi,yace zai kira Dr gida nan ma tace
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155