Chapter 51
Chapter 51
tafiya ta kammala" anty deena ce ta karbe cikin dariya "Aiko dai batason wahal daku biyan kudin biko,ai shikenan" dariya aka dauka a falon,kowa yana fadin albarkacin bakinsa,kusan yadda batulu taso a juya zancan ya zamarwa widad abun fada abun baizo a haka ba,kusan kowa dariyar quruciyar yakeyi. Sannu a hankali jerin motocin dake dauke da mafi yawan 'yan uwanta suka fara barin farfajiyar gidan alhj salim mai fata,motar da take ciki itace mota ya qarshe,duk da a tsarin tafiyar zata kasance cikin tsakiyar motar securities din da zasuyi musu rakiya har zuwa garin bauchin. A hankali tasu motar ta fara motsawa,yayin da taketa dagawa su Aafiya hannu tana fadin "Sai kunzo,karku damu,alhaji yace kamar wancan lokacin da naje gidan uncle muhsin,wannan lokacin har zuwa zasuyi shida ummu saimu dawo tare,idan zai taho ku taho tare dashi don Allah" ta fada tana kallon afiya,tans jin ba dadi itama,zuciyarta najin wani irin yanayi wanda.bata saba jinsa ba,irin yanayin dako sanda zataje gidan uncle muhsin bata sanshi ba,wannan shi ake kira da yanayi na rabuwa......rabuwa da gida..... rabuwa da muhallin da qaddara ta wanzar maka a haifeka a ciki......rabuwa da bigiren daka rayu kayi kuma gwagwarmaya a ciki.....fadi tashi tsakanin masoya da maqiya,zuwa wani bigiren da RUBUTACCIYAR QADDARARTA ta zana mata......BIGIREN dake qunshe da tarin qaddarorin rayuwarta.....qaddarorin dake da tsananin zafi quna da kuma barwa rayuwa tabo me cin rai. Tun suna tafiya tana biye da hirar wadanda suke tare cikin motar wato anty deena,anty madeena anty madeeha da inna uwa,wani bangaren na zuciyarta kuma nata hasaso mata kayayyakin da dukka ummu ta nuna mata ta kuma shaida mata nata ne gidanta za'a kai mata,yadda zata sarrafasu ta more kayanta,irin yadda taga su anty deena anty ramziyya basma da sauran yayyunta keyi,zatayi iko irin nasu kenan itama,zata saka wasu wanke wanke idan sunzo gidanta,sai qaramar dariya ta qwace mata ita kadai,tana fasalta yadda zata saka su rafi'ah aiki,kuma dole suyi,saboda jiya jiya taji anty madeena na cewa ita din yanzu dukka ta girmesu,duk kuwa da cewa sun babbata wasu watanni. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 33 Table guda ya kama shi kadai,sanye da fara sol din shirt me gajeran hannu,sai wani lafiyayyen trouser daya dace da boots din qafarsa,coffee kawai yake sha,duk da yana da buqatar abinci,loneliness yake da buqata,yayi hayaniya har baisan iyakar adadinta ba,abinda ba dabi'arsa bace,yana tsoron hakan ya haifar masa da ciwon kai,wannan yasa ya zabi ya kebe shi daya ba tare daya gayawa kowa inda yake ba idan ka dauke suraj. Tun jiya suke karbar baki,ko kusa ko alama bai dauka wani sabon bikin zasuyi ba,sai da yaje gidan hajiyarsa yaga yadda ta tashi gagarumin biki,ya koma gida bisa ga mamakinsa hafsat ta zauna tayi masa lissafi ta kuma karba kudade sosai daga hannunsa tana shaida masa itama taro zatayi "Ko yaya ma dai nakai ga qinta,tunda har an daura ta zama matarka,ina da ikon maida abinda ya faru ya zamana ba wanzajje ba?" Kai ya gyara cikin gamsuwa,ransa na masa dadi,yana sake samun nutsuwa,mamakinsa na sake daduwa akan hafsat din,fatansa da burinsa na dorewarta a haka na sake hauhawa,wanann abun yasa ba haufi ya ajjiye mata abinda ta buqata harda ma qari. Kusan komai mamaki yake bashi,auren yazo masa a hagunce,yanata kuma zuwa da abubuwan mamaki,bai dauka wani aure bane na azo a gani ba,amma sai gashi anata shirye shiryen daga kowanne bangare. Wayarsa dake yashe saman table din ta soma haske,saboda tuni ya maidata silent,idan kira ya shigo sai.ya duba ya tabbatar mai muhimmanci ne kafin ya daga,a yanzun ma suraj ne don haka ya danna green ya kuma maidata handsfree ba tare daya dauki wayar a hannunsa ba ya barta nan saman table din. "Baka dawo bane?,kana ta ina?" "I will be back......akwai damuwa ne?" "Babu,kusan ma an kammala komai,har presidential lodge din da za'a zuba sauran baqin ya zama ready" "Good,thank you suraj" "What are friends for" murmushi ya saka ya kashe wayar. Har ya daga coffee din zai sake sipping tunanin kiran Samuel yazo masa,ya lumshe manyan idanunsa kadan sannan ya budesu yana tuna yadda hajiya ke bashi amanar yarinyar,tun ranar da aka daura aurensu har yau din nan,ba ranar da zata fito ta fadi bata ambata masa cewa amana ce ta iyayenta ba,sannan amanace ta ita kanta hajiyan,farincikin da yaga hajiyar nayi da auren kawai ya isheshi shima,bashi da burin daya wuce ganin walwalarta,da kuma farincikinta,wannan ya qara masa qaimi ya danna number samuel din. Cikin girmamawa da kuma nuna respect yake amsa kiran ogan nasa,ya tambayeshi hanya yace komai lafiya,ya gaya masa a inda suke a yanzun,ya kashe wayar yana irga adadin mintunan da suka rage musu su qaraso bauchin,sai ya shanye sauram coffee dinsa ya miqe yana maida wayarsa aljihu,ya dauki key dinsa ya nufi parking lot na gurin shan coffee din. °°°°°°°Cike gidan yake da 'yan uwanta da abokan arziqi har zuwa compound na gidan,wani abun mamaki ko kuma rashin sabo ga duk wanda yasan gidan ko kuma ya saba wucewa ta gaban gidan,ko gari banza da wahala kaga tayi baqo,don ita din mutum ce mai tsananin rowa da tsumulmula,rashin kyauta rashin faran faran da rashin iya tarbar baqo. Daga cikin gidan kuwa,cikin bedroom din,hafsat din ce zaune a gefan gadonta,sai anty ummee da tayi tsaye gaban cupboard dinta tana zaqulo mata kayan data saka,sai mita takeyi cikin masifa "Duk wannan uban suturar bansan me kike dasu ba,ke baki saka ba ke baki bayar ba,duk kayanki na fadan kishiya kuma bansan gidan uban da kika kaisu ba,kudin dinki da gyaran daya baki suma ina kika kaisu oho" "Don Allah anty ummee kawai ki dauko kayan da zaki dauko ki barni naji da abinda nakeji" hafsat ta dago kanta da takejin kamar zai cire ta fadawa ummee din,sai ta waiwayo ta dubeta,idanunta har sun kada sun canza kala,tabe baki tayi,ta juyo hannunta riqe da wani lace,wanda a ido yayi mata kyau sosai,tana kuma saka ran zai zaunawa hafsa din "Da wannan raunin naki da kuma rashin juriyarki bana jin zakici nasara maganar gaskiya,yau kawai.....tun bata kai ga shigowa gidan ba?,ina ga ta shigo?,ta wanzu a cikinsa?,zakici nasara kuwa?,wannan siradin ba na raguwar mace mai raguwar zuciya bane,hanya ce mafi sauqi ta mallakar kowa da komai......saidai.....tana yiwa yawa yawna mata wahala,ciki harda ke da alama" Hannunta dake dafe da kanta ta saki,ta sake daga kanta tana kallon anty ummee da kyau,muryarta a mugun karye,ita kadai tasan me takeji tsakanin zuciya da qirjinta "Wanne qoqari zanyi anty ummee bayan wannan?,kinsan me nakeji kuwa?,har na fara nadamar daukan shawararki,qila da ace abinda zuciya ta ke gayan nayi na aikata.....wala'alla da ban fuskanci zafin da nakeji a yanxu ba....." "Da kuma kinyi biyu babu ba.....da baki samu darajar da kike ganinta a idanunsa ba,da nutsuwar da kike qaryatawa a yanzun
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155