Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 78

Chapter 78

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,315 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yana shirin tada motar,kafin ya gama rufe bakinsa wayarsa ta dauki kuwwa,sai ya qarasa kunna motar ya barta tana daukan zafi ya duba me kiran. Hajiyansa ce,nutsuwa yayi sosai ya daga wayar a ladabce yayi sallama,ta amsa masa cikin nuna kulawa da qauna,ya soma gaisheta gami da tambayarta lafiyarta,duk da jiya ma da yammaci sunyi waya da ita "Yaushe zaka zo gida ne?,ka manta kabar wata iyalin naka a nan?" Tambayar yaji banbarakwai,saboda ba al'adar hajiya bane yi masa irin wannan tambayar "Yanzun haka ma muna cikin mota zamu fito daga Kadunan....." "To alhmdlh ma sha Allah" haka kawai yaji zuciyarsa da ransa basu kwanta masa ba "Hajiya lafiya dai ko?,ko wani abunne ya faru?" "Babu komai,Allah ya tsare hanya" "Hafsat ce ta kawo miki maganar?" Ya sake dai tambayar hajiyan "Nace babu komai,Allah ya tsare hanya,ina widad din?" Waiwaya yayi yana kallonta,ita sam hankalinta ma da alama baya wajen,yana farfajiyar gidan inda mai gadin gidan yaketa gyaran flowers,dauke kansa yayi ya maida gabansa "Tare zamu taho in sha Allah" "To hakan yayi,sai kun iso" "Madalla hajiya,Allah ya saka da alkhairi" sukayi sallama kowa ya aje wayar. Iska ya furzar yana tada motar,idan ya rantse ko kaffara bazaiyi ba hafsat ce takai qararsa wajen hajiyan,don ya sansano hakan daga muryar hajiyan,yasan ta boye masa ne kawai saboda kare martabar hafsa a wajensa,wai me yasa ita din bata jin kunya ko nauyin kaishi qara?,yanzun wannan abun har ya isa takai qararsa gaba?, just one week daya qara baizo ba?,bayan he explains to her?,baisan sai yaushe zata fahimci illar wannan muguwar dabi'ar tata ba,baisan sai yaushe zata gane zubarwa da kanta kima da daraja takeyi a wajen iyayensa ba. Ya danyi gudu,hakanan banda sallah basu tsaya sunyi komai ba a hanya,don haka awanni biyu da rabi suka kawosu bauchi daga kaduna. Ba'a jima da idar da sallar la'asar ba suka shiga unguwarsu,ya faka motar a harabar gidansa,kafin ya sake wani abu tuni widad ta balle murfin motar ta fice saboda hangosu mimi da tayi,suma tuni sukayo wajen,saboda sun shaida motar daddyn nasu. Binta yayi da kallo kawai,har zuwa sanda ta isa garesu suka rungume juna,sannan suka iso bakin motarsa suna dakon fitowarsa. Tare suka rankaya zuwa ciki,mimi da nawwara kowacce na bada nata zancan,fuskar widad fal fara'a,har suka isa falon hafsat din. Kallo daya ya yiwa falon yaji bacin rai ya saukar masa,kullum jiya i yau,dukka gyara da qyale qyalen daya zubawa falon daga bikin widad din tafiyarsu kaduna zuwa zuwansu yau gaba daya sun fara dakushewa,sai ka rantse kayan sunyi shekaru bakwai da sakasu,kai koda shekaru bakwai dinne indai ba qazamar mace ta ainihi ba bai kamata suyi wannan dafewar ba,ko ina tarkace ne dake nuni da cewa babu wadatacciyar sharar da falon yakeso,uwa uba turkish carpet dinta ruwan madara ya fara yin qaura daga aihinin kalarsa zuwa brown, qawataccen center table din daya zuba kudade ya siya mata an soma kwanceshi,ba wasu sassa a jikinsa. "Ina Mommy din?" Widad ta tambayi mimi "Tana kitchen,wanke wanke take" "Muje ki rakani" ta kama hannun mimi din suka wuce kitchen din. Bata a kitchen din,amma qofar backyard na kitchen din a bude yake,sai suka sanya kai can. Turus widad tayi tana duban iyayen kwanukan dake yashe a wajen tamkar anyi taron biki ko siyasa an watse,kusan dukka wasu kwanuka na kitchen dinta suna wajen,tana tsakiyar su ta hada kumfa a babban baho tana wankewa,tanayi tana maganganun qasa qasa,daurin qirji ne a jikinta na zanin atamfa,sai rigar shirt,kanta dankwalin zanin ne data masa daurin gaban goshi,daga qasa kana iya hango qananun gashinta sun burtso. "Mommy sannu da aiki" widad ta fada tana murmushi,hafsat ta waiwayo da sauri suka hada ido da widad din,a take taji ta muzanta,bata taba kawowa a yau idan hajiyan ta kirashi zai taho ba,dukka ta dauka sai gobe,don haka yau taci burin qarar da yininta tana gyaran kitchen,tasan shi da falo da toilet sune abu na farko da yaqi jinin ya gansu ba'a kintse ba,yau din kuma alhamis,ta zaci zai taho gobe juma'a ne. Sake juya idanunta tayi akan fuskar widad karo na uku kafin ta samu sukunin amsa sannun tata data yi mata,idan idanunta ba gizo yayi mata ba yarinyar qara haske da kuma qiba tayi,ga wani dan banzan qamshin turare da taketa bulawa hancinta,wani abu mai qarfi ya taso ya kama zuciyarta, muryarta ta sarqe,har sai da hakan ya bayyana cikin sautinta,ta jefa mata tambayar muryarta a cushe "Dake da waye?,da yammar nan?" "Ni da daddynsu mimi" tayi maganar tana kallon qofar da zata sadaka da kitchen din,saboda tuni hancinta ya shaida mata wanzuwarsa a wajen,sassanyan qamshinsa daya fara yo gaba. Idanun widad na kansa haka na hafsat,yayin da nasa idanun ke kan hafsat din da tarin kwanukan wanke wankenta,wanda ko ba'a gaya masa ba yasan halin nata tayi,wato tayi girki ta jiqa kwanon,gobe ta bare sabo ko wankakke ta sake wani girkin a ciki. Tuni idanusa suka cika taf da bacin rai,banda wanda ya shaqa daga falo,da kuma dattin daya hanga akan sumar yaransa,ga qurajen zafi da suka fesowa nawwara,tabbacin ba'a kunna musu gen kamar yadda ya bar sallahy,bayan ya aje kudin komai da komai. "Sannu da zuwa" ta fada tana miqewa hadi da sauke zaninta data yaye cinyoyinta "Yauwa" ya fada yana komawa da baya,cikin sa'a ko rashin sa'a,sai ya taka sauran rubabben abincin data kwakwkwafe a kwandon shara,Allah yasa boots ne a qafarsa,yaja da baya ya murje qafar tasa ya fice daga wajen. Cikin shan jinin jikinta ta soma takawa zata bishi,har tayi taku uku saita waiwayo tana duban widad,zuciyarta na cika da kishin kwalliya da sutturar jikinta "Zauna ki kamamin wanke wanken nan ina zuwa" "To" ta amsa mata,babu gardama,ta soma ratsawa ta cikin kwanukan tana tattare hannun rigarta,ta zauna kujerar data tashi,ta fara jan kwanukan tana wank su,mimi na mata hira. Har ta doshi hanyar sassansa saita tsaya,ta kalli jikinta da kyau,ita kanta ta shaida tsami takeyi,sai tayi ribas,ta koma da baya zuwa bedroom dinta,ta kunna heater a gurguje ta saba sabulu ta dauraye da ruwa,ta tsaya gaban mudubin ta ta balbala turare sannan ta zura wata doguwar rigar baqar atamfa,ta dora daurin dankwalinta sannan ta fito. Har zata wuce ta tuna tabar mimi a can,saita koma ta tsaya daga qofar kitchen din tana qwala mata kira,yarinyar ta taso,ta kama hannunta suka bar wajen,tana jefawa widad harara a fakaice "Saikin gane Allah daya ne wallahi yarinya,muje zuwa wai mahaukaci yahau kura". A falo ta samu nawwara,tasha chocolate har ta godewa Allah,ta aje mimi a nan ta wuce kai tsaye bedroom dinsa. Yana tsaye gaban mudubi yana maida maballin wata jallabiyya mai azabar kyau,hade take da wandonta da aka yima aikin zare daga qasa, lallausan qamshinsa daya karade dakin ta zuqa,tana son turarensa matuqa,saidai ko ya bata bata iya jurewa shafawa kullum da kullum Sarai ya hangeta ta cikin madubi sanda take shigowa,amma bai fasa abinda yakeyi ba,hakanan bai waiwayo ba,jikinta ya qara sanyi,ta tako a hankali kanta a qasa,tayi mazauni a kujerar bayansa "Sannu da zuwa ya hanya?" Ta sake fadi "Lafiya" ya amsa mata a taqaice,ya dauki comb yana sake taje kansa,sannan ya daura agogo ya dauki daddumaersa a qagauce "Zanje sallah na dawo,ki gyaramin sashe na" daga wanann ya juya ya fice a dakin,yana jin yadda shegen turarenta daya tsana yake

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});