Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 57

Chapter 57

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,327 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta sauya wasu?,a dakinsa?,saita damqe jikinta waje guda kamar wadda ya taho zai rabata da suturarta,ta jijjiga kai da qarfi "A'ah,wadan nan nakeso na jikina" dariya taso qwace masa amma ya danne,a yadda take acting yasan lallai batasan meye cikakken ma'anar aure ba,to amma me yasa take tsoro haka,sai ya rabu da ita,ya jawo wayarsa da nufin kiran hafsat din yayi mata sai da safe,duk da baisan me ya fiddata daga dakin ba,ya tsammaci zatace zata kwana kamar jiya. Sau uku yana kiranta tana katse kiran,abun yadan daure masa kai,amma saiya tattara ya watsar,dare yayi,hutu yake buqata "Ki koma gado ki kwanta" ya sake fadi,kamar dazun dai a firgice tace masa a'ah,sai da yayi da gaske sannan ta kuma taga ya yibi filo da bargo yana shirin bar mata dakin sannan taji ranta ya sake. K'ofar tabi da kallo sanda ya fita,sai kuma ta fara baza idanu,dan banzan tsoron nan nata ya dawo,ji tayi kamar ta bishi,amma ba zata iya ba,curewa tayi waje daya ta lulluba har kanta,saita saki kuka,anty deena ce.....duk ita tace sai tazo,gashi nan sun rufe mata qofa,bayan sunsan ta fita,kewar ummu ta taso mata,ta dinga hawaye ita daya cikin filo,har bacci barawo ya saceta. A hankali ya bude qofar dakin,duk da akwai qarancin haske amma yana iya hangenta a cure waje daya,sai ya kada kansa ya wuce bandaki. Alwala ya daura ya dawo dakin,ya feshe jikinsa da turare ya sauya jallabiyyar jikinsa,ya taka a hankali zuwa gefan gadon,hannu yasa ya bubbuga saman filon a tausashe,ta motsa kadan kamar zata tashi,sai kuma ta sake qudundunewa,cikin muryar barci tace "Don Allah ummu,ba'a idar ba,yanzu aka tayar" shuru ya danyi yana nazarinta,ta kwabe fuska gaba daya tana tura baki gaba a shagwabe,har kuma a hankali ta saki bakin nata,da alama ta koma bacci sosai. Kai ya girgiza kawai,bai hango komai ba banda zallar quruciya a tattare da ita,shikam baisan ya al'amuran zasuci gaba da tafiya ba,bai hango sauqi ba,sai nauyi daya sake hawa kansa,sai ya juya a nutse ya nufi qofa,yana kama handle din zai.bude ta bude idanunta a hankali, saboda yadda taji cikin jikinta ba'a gida take ba,saboda duk sanda tayi irin haka ummu saita takurata akan sai ta tashi koda ba'a tayar da sallar ba. Tana qyallara ido ta hangoshi,saita zabura ta miqe tana rarraba idanu,a nutse ya waiwayo ya kalleta,sai baice komai ba ya sanya kai ya fice. Sai data daina jin motsinsa sannan ta miqe a hankali cike da tsoro ta tura bandakin ta shige tayo alwalar itama ta dawo ta gabatar da sallar,har Allah Allah take ta idar ta fice zuwa wajensu anty madeena,tana idarwa bata ko tsaya addu'a ba tayo waje. Cak ta tsaya a qofar falon kamar zata saki kuka,ganin garin da duhu har yanzu,gashi dukka fitilun harabar gidan an kashesu,dan banzan tsoronta kuwa bazai barta ta wuce sashenta ba,saita koma.bakin qofa ta rabe tana maida qananun hawayen dakeson sauko mata,ba zata koma cikin dakin ba kuwa,a nan zata yita zama har sai gari yayi haske. Baiyi zaton zai sameta zaune a bakin qofa ba,don haka cike da kuzari da kuma hanzarinsa ya buda qofar falon "Subhanallah" ya fada da sauri yana kama murfin qofar ya riqe a hannunsa,sai kuma yadan dai daita yanayin fuskarsa yana kallonta "Me kikeyi a nan?" Mele baki tayi fuskarta a yamutse,da alama qiris take jira ta fashe "Ina kwana?,can zan koma,kuma wajen da duhu bazan iya fita ba" sai daya juya ya sake kallon harabar gidan,shi yasa aka kashe fitilun saboda yaron gidan yace sunata wasa da wutar kada su lalata qwayayen,qwayaye ne masu tsada da daraja "Basu bude ba suma,ki koma ciki sai rana ta fito" kai ta maqale a kafada,sannan ta miqe kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,ta koma saman kujera ta takure waje daya,bai sani bama ko hawaye take sharewa. Dakin ya wuce,bai jima ba ya dawo,ya haye saman doguwar kujerar daya kwana a kai,yaja bargonsa zuwa qugu ya rufe, lokaci lokaci yana dan daga idanu ya dubeta,yadda take curewa waje daya ta kwanta shine ke bashi mamaki,amma baice da ita komai ba. Wantsalowa tayi daga saman kujerar sanda agogo ya gama buga qarfe bakwai dai dai,suna hada idanu sai kuma ta koma dai dai ta zauna,fuska a narke take dubansa,cikin salo na roqo da magiya tace "Don Allah.....ka rakani,gari yayi haske fa?" Ido ya tsura mata na wasu sakanni yana kallonta,sai ya janye idanun nasa yana zame bargon jikinsa,daki ya sake shiga,bai jima ba ya fito yana gyara button na rigarsa "Muje" da saurinta ta sauko muryarta tabi bayansa,don kafin yakai qofa har ta kusa cimmasa,yadan sake binta da kallo sannan ya buda qofar suke fice. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 37 Cak ta tsaya sanda suka isa bakin part din nata,ta juya tana fuskantar sa,fuskarta a narke,tana wasanda yatsunta,da alama magana takeson masa,amma ta kasa sai motsa yatsunta da takeyi,shi kuma ya kafeta da idanu,ganin ta kasa magana sai yayi gyaran murya,ta daga idanu ta dubeshi,kafin yace wani abu ta magantu "Don Allah kada ka shigo" mamaki maganar tata ta bashi,sai ya kafeta da idanu yana neman ba'asi,bata gane ba,murya a narke tace "Kaji?" Saiga qwalla ta biyo bayan maganar,bai shirya ba amma dole ta sanya qaramin murmushi ya qwace masa,sai ya kauda kansa gefe na sakanni yana danne murmushin kafin ya dawo da dubansa gareta,ya gama gano abinda take nufi,don haka yace "Is okay" sai ya juya a hankali yabar wajen yana nufar sashen hafsat. Ajiyar Zuciya ta sauke tana binsa da ido,sai taji dadi a ranta da ya tafin,don idan da ya tsaya ba shiga zatayi ba,da wanne ido zata kallesu?,me zatace musu?,ta samu relief don haka ta juya tana dosar qofar falon nata. Kamar wata munafuka haka ta dinga rarraba ido tana rabewa a bango,jikin labulen bakin qofa ta tsaya tana leqen falon,inna laila ce saman dining ita da batulu,sai nujood zaune saman kujerar falon,Momma na zaune daga qasa,dukkansu kowa sanye da hijab,da alama tun tashin asuba ne basu koma ba. Tana daga tsayen ta hangi anty deena ta fito dauke da wata jaka ta ajjiye saman kujera,ta kalli nujood tana cewa ta tashi su sake gyara falon,latifa ta riga ta gyaro ciki,saita matso ta wajen bakin qofa zata dauka mopper dake ajiye a wajen. Motsin mutum ya sanyata waiwayawa ta dubi wajen,cikin mamaki take kallon widad "Ke kuma me kike yi a nan a tsaye ke daya?" Rau rau tayi da idanu,a yadda anty deena ta kafeta da idanu saita fara hawaye kawai "Meye haka widad?" Tambayar da ta sanya jikinta rawa,saboda tana ganin kamar anty deena din ta hangi abinda ya faru jiya,hankalin anty deena yadan dauko kadan,ta zaci ko wani abun ya gudana tsakaninsu,sai kuma taji hankalinta yadan kwanta kadan da taga yanayin tafiyarta bai canza ba,tana tausayinta,koda wani abun

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});