Chapter 142
Chapter 142
lallen ba,abinka da farar fata,mugun kyau yakeyi mata,wani zubin har tukuici sai ya ajjiye mata. Duk da haka ya kama yatsun hannun nata yadan ja kadan yadda zata fahimci zancan yace "Dani dake waye yafi wani laifi?,Allah da kansa fa cikin qur'ani yake cewa 'yaku wadanda kukayi imani,kada ku shiga gidajen da ba naku ba har sai kun nemi izini kunyi sallama akan ahalin gidan,wannan shine mafi alkhairi a gareku,idan ma baku samu kowa ba a cikinsu gidajen kada ku shiga har sai an muku izini,idan kuma akace ku koma ku koma' kinga anan kin sabawa koyarwar qur'ani da sunnah" tunda ya fara maganar ta zuba masa ido tana hawaye,yau gidanta ake cewa ba zata shiga duk inda taso ba saita nema izini saboda ya ajjiye wata "Yanzu abbas gidana kake kafamin wadan nan sharuddan a kansa?" "Ya salam"ya fada yana lumshe ido takaici yana kamashi,wacce irin qwaqwalwa take da ita,yana gaya mata Allah da annabi tana gaya masa molanka da son zuciyarta, kafin ya buda idanun ta dora "A jikinka fa na sameta,ranar kwana na,kaci amanata kanason juya laifin kaina,wallahi sai yanzu na gane dalilin da ya sanya yarinyar nan ta fara rainani,kana raba mana kwana,kana duk abinda kakeyi dani da ita,tana shirme kana biye mata shi yasa take kallon kowa a banza.....". Tsam ys miqe "Excuse me"ya fada a taqaice yana rabata ya wuce,don bazai iya ci gaba da daukar rainin hankalinta ba,kamar yadda ya fuskanci gaba daya ba zata taba gane abinda yake nufi ba. Gaba daya ranar ta bata ta da kuka da takaici,taji a ranta ta riga ta gama yin sake,saidai har yanzu akwai sauran dama da zata nunawa yarinyar ita ba kanwar lasa bace. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 93 Widad kuwa sabgarta take a sassanta,don ko leqowa batayi ba bare ma su hadu,su mimi suna wajenta,sukaci lafiyayyen abincinta suka qoshi,daga qarshe ma bacci a nan ya dauki mimi,nawwara kawai ya dauka sanda yazo yi mata saida safe,tace yabar mata mimi din ta kwana a nan. Uwar bata wani damu ba,a lokacin kawai kallon raguwar hidimarsu bisa wuyanta takeyi,bayan ta kwantar da nawwara ta cimmasa a bedroom,ya gama shirinsa cikin kayan bacci,sassanyan qamshinsa ya cika dakin,yana zaune yana amsa waya hankalinsa kwance,saita bude closet dinsa ta duba doguwar riga cikin kayan baccin da yakan ajjiye a dakin,ta tube rigar lace din jikinta ta aza kayanta tayi fuska,babu batun sake wanka,tunda dai an tsira da wankan safe,ta dawo ta zauna,lokaci lokaci tana kallonsa har ya gama wayar ya aje yana dubanta "Ya akayi?" Ya fada yana kallonta, don yasan halinta,ungulu ce bata jewar banza,zaman da tayi lallai akwai magana a bakinta "jari nake buqata ka bani,jari na yayi qasa" yana daga kwancen yake kallonta,ya rasa me takeyi da kudi,ashana baya barin mace ta siya masa,ko yaushe cikin tura mata kudi yakeyi,suttura har wardrobe dinta baya rufuwa saboda yawansu kuma gashi ba sanyawa akeyi ba,hakanan ba bayar dasu akeyi ba,bata taba cikakken sati ba tare data nema kudi a hannunsa ba,sai ya lumshe idonsa sannan yace "Kamar nawa?" "Fice hundred thousand only" "Only?" Ya maimaita zancanta na qarshe,ba tare da ya jira amsarta ba yace "Allah ya hore" wani kallo tayi masa sheqe qe,amfanin da zatayi da kudin ta gama kasafta zasu fita ne a jikinsa,don ba zata iya fiddasu daga cikin kudinta ba,amma zaizo mata da wannan zancan "Allah ya hore,saidai idan ba zaka bayar bane?" Miqewa yayi ya zauna sosai yana kallonta cikin idanu "Kullum me yasa babban burinki da jin dadinki ki kawo sabani a tsakaninmu?,me yasa zaman lafiya baya miki dadi?" Maganganunsa sai taji kamar gugar zana yake mata,take ta cika tayi fam ta fara zubda maganganu "A hakanne banason zaman lafiya?,duk da tarin haqurin da nakeyi kai baka gani ba?,ina cewa makaranta ka maida waccan yarinyar kana kashe mata kudi,ko ka dauka bansan private ka kaita mai tsada ba?,itama taci kudinka ballantana ni,ita din da duka duka kwananta nawa a rayuwarka,duk kawaicina baka ganshi ba kenan tunda ni dama a wajenka babu abinda na iya na alkhairi" Ido ya maida ya rufe kamar me shirin bacci,saidai ba baccin zaiyi ba,yana sauraren bugun zuciyarsa ne da duk bugawa take bugawar da zallar qaunar yarinyar tare da ambato sunanta,she means alort to him,batasan wace widad cikin rayuwarsa ba,yana dai qoqarin dannewa ne kawai,bai baiwa soyayayyarta kaso daya cikin goma damar fitowa ba saboda kada ya bada kafar barna ko baraka a tsakaninsu,a wannan yanayin yasan duk bayanin da zaiwa hafsat din a banza,ba zata fahimceshi ba sam,idan idanunta suja rufe kan abu kamar cin qwan makauniya,burinta kawai ayi mata abinda ranta yakeso,yana jinta tana ci gaba da zayyano dalilai marasa tushe bare makama,da ya gaji da jinta sai ya miqe tsam kawai ya dauki pillow ya yada a qasa ya kwana abinsa,abun da ya sake tunzurata kenan,ta miqe ta cire rigar baccin jikinta ta maida rigar lace dinta data cire,ta buda qofar tayi ficewarta,yadan bude idanunsa a hankali yabi bayanta da kallo harta fice,sai ya gyara kwanciyarsa yana rufe idanunsa,sam baiji wata damuwa ba don ta fita din,tun yana tunane tunane har bacci yayi gaba dashi. A ranar kwanan kuka tayi ta godewa Allah,gaba daya tsanar widad ta gama cika mata zuciya,abubuwa da yawa basa faruwa saita sanadin zuwanta,gaba daya ta hargitsa mata gida ina dalili?,cikin ranta da zuciyarta takejin matakin data dauka shine dai dai, hukuncin data yanke kuma yayi dai dai,domin a yanzun babu wani abu da zai saurin sadata zuwa ga cimma burinta idan ba ta wannan hanyar ta biyo ba. Washegari widad din ta shirya ita dasu mimi,tun da safe tayi musu wanka,ta cire kaya cikin wadanda abbas a taho musu dashi ya manta su cikin kayanta tayi musu kwalliya da kyau suka wuce gidan hajiya. Taji dadin ganinsu matuqa,ta rasa inda zata sanyasu,a nan akayi mata jan lalle har bayan hannunta,hatta hajiya sai data yaba, idanunta na buye da Widad din tana ji a ranta anya ba juna biyu widad din ke dashi ba?, quruciya ta hanata ganewa,shi kuma uban gayyar hankalinsa baikai ba?,amma da yake hajiyan bata cika sanya baki a lamuran surukanta ba duk da tana jin widad sosai cikin ranta,kamar diyar data haifa a cikinta,duk da haka sai tayi shuru,cikin ranta ta bisu da addu'a. Da yamma tace masa zata koma taje tayi girki,suna shirin tafiya sai gashi,tayi mamaki don bata tsammaci zaizo ya dauketa ba,haka kawai yaji duka gidan babu dadi bayan fitarsu,amma hakanan dai ya daure suka wuni da giwar tasa a haka😂,duk da babu abinda ya tsinta a zaman,don gaba daya babu fara'ar arziqi a tattare da ita bare hirar arziqi,to dama yaya lafiyar kura bare tayi hauka?. Tunda ya shigo shima yake binta da kallo,lallen ya sake fito da ita sosai,ya kasa daurewa har sai daya bita kitchen yasha dumin jikinta sannan ya samu nutsuwa,suka tattare sukabar gidan hajiyan suka wuce gida. Tare yau sukayi girki kamar yadda suka saba a Kaduna,gaba daya yau sai takejin kasala,har yana tsokanarta "Kindaiyi qiba baby kawai" saita hau bubbuga qafa "Niba wata qiba,Allah banaso" dariya mai taushi ya saki,ya dauketa cak ya dorata saman kantar kitchen din "Ni kuwa bakiga yadda kikayimin kyau ba,komai ya fito yadda nakeso.....fiye ma da yadda nakeso,sannan kin qara dad......." Hannu tasa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155