Chapter 107
Chapter 107
U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: Huguma* Page 70 Duk da cewa baikai ga cimma gaci ba,duk da cewa buri da muradinsa bai cika ba......amma ta kaishi wata duniya data sake haukata tunaninshi,ta sake ninka burinsa......ta sake kwadaita masa ita,ta kuma haifar da wani yanayi da kai tsaye zaka kirashi da ZAZZAFAR K'AUNA a karon farko,cikin jininsa ya dinga ji cewa eh weedad din ta dabance,zata iya zamowa ta musamman cikin mata..... za'a iya kiranta da 'yar baiwa,ya samu wani irin nutsuwa da tarin ni'imomin dake hutar da zuciya su kuma sanya ma ruhi nutsuwa tattare duka a iya jikinta kadai,tun baikai ga afkawa waccar duniyar ba. Wani irin ciwo yakeji har cikin zuciyarsa sanda take rera wani irin kuka,ciwo ciwo takeji daga can qasanta duk da baiyi yawa ba,saidai hankalinta a mugun tashe yake,me ya aikata mata kenan?,da wanne fuska zata kalli mutane?. Yayi lallashi yayi ban bakin amma a banza,har sai da bacci ya taimakeshi ya dauketa,sai ya zareta daga jikinsa a hankali ya shimfidar da ita,ya kunna bedside lamp ya matso da ita kusa da fuskarta sosai. Kallo na haqiqa ya zauna yana qare mata,baisan da wanne suna zai kirata ba,baisan kuma a wanne matsayi zata iya tsayawa cikin zuciyarsa ba daga ranar da ya maidata tashi,a yanzun Allah ne kadai yasan me yakeji a kanta,qauna soyayya tausayi da kuma shauqi gaba daya, mintuna qalilan amma sun canza matsayinta daga wani bigire zuwa wani bigiren na daban. Ya jima zaune kamar mai karanta littafi yana kallon baby face dinta da tayi jazur da ita,sannan ya sauke ajiyar zuciya,ya zura qafafunsa ya sauka daga saman gadon ya shige bandaki. Tsarkake kansa yayi sannan yayi wanka,ya fito ya tsane jikinsa da kyau ya sauya kaya sannan ya koma saman gadon,bai jishi dai dai ba har sai daya jawota jikinsa,tunane tunane ne masu tarin yawa ke masa yawo a kai,shi kansa idan yace ga dai dai lokacin data ma zuciyarsa wannan muguwar illar yayi qarya,wani abu mai qarfi akanta ya dinga shigarsa,sai ya dinga jin gaba daya duniyarsa ta ta'allaqa da ita. Kiran sallar asuba ne ya tasheshi,har ya gama shirinsa na fita masallaci bata ko motsa ba,bacci take sosai tana kuma sauke ajiyar zuciya lokaci bayan lokaci,har sunkuya saman kanta zai tasheta yaji ya kasa tashin nata,yaja mata bargon ya rufeta bayan yayi kissing goshinta,ya fita yana waiwayawa kamar wanda akace za'a dauketa kafin ya dawo. Sanda ya fita sallar yayi mamakin ganin cunkoson jama'a a layin nasu,ya qarasa a hankali ya fara musabaha da mutanen dake wajen "Munyi tunanin baka gari ai yallabai" daya daga cikin dattawan layin ya fada yana duban abbas "Me yake faruwa alhaji audu?" Abbas din ya tambaya yana dubansa "Wallahi daren jiya 'yan fashi suka shigo gidan maqocina alhaji isah" "Subhanallah" ya fada cikin alhini "Kusan kowa yaji abun,don tun wajen karfe daya na dare suka shigo unguwar,basu fita sai qarfe uku" "Ya salam,Allah bai sa naji ba,amma aka rasa wanda zaiyi kiran koda wayata?" "Wallahi Allah ya daukewa kowa wannan tunanin" matsawa gaba ya fara yi zuwa gidan alhj isah din,inda mutane suka fara dandazo "Badai wanda suka raunata ko?" "Eh to,sun harbi yarinyar sa,suna hanyar kaita asibiti" "Kun kira jami'an tsaron?" Cikin alhini alhj audu ya girgiza kai "Kusan awa guda kenan amma babu su ba dalilinsu" sosai ran abbas din ya baci,ya tambayi police din wanne area dinne alhaj audu ya gaya masa,sai ya fidda wayarsa yayi kiran dabai wuce na minti uku ba cikin bacin rai "you must be there before thirty minutes" abinda ya fada kenan ya kashe wayar ya mayar aljihu "Kada kowa ya shiga cikin gidan,sannan suma mutanen gidan a gaya musu su nisanci inda abun ya faru.... alhaji muje muyi sallah tukunna" tare suka rankaya da alhaji audu zuwa masallacin suna sake tattauna yadda abun ya faru,bashi da nauyin bacci sam,kamar yadda bai saba dogon bacci ba,amma yayi mamakin yadda jiya har akayi aka gama abun baiji ba,lallai da gasken gaske 'yar qaramar yarinyar ta gigita masa rayuwa da kyau a jiyan,ta kuma shirya janshi zuwa wata rayuwa ta daban,baisan sanda wani siririn murmushi ya kubce masa ba. Wannan case daya faru a unguwarsu ya hanashi komawa gida da wuri,sunata bincike kan abun har sai da suka samu nasarar tracking barayin cikin taimakon Allah da kuma qwarewar da yake da ita,sai wajen qarfe daya na rana sanann ya gama nasa aikin,ya danqawa wadanda alhakin kula da area din yake a hannunsu,ya zare safar hannunsa ya miqawa daya daga cikin police din,gaba daya hankalinsa yana kanta tun dazun,dauriya kawai yakeyi. Sama sama ya amsa gaisuwar yaron gidan nashi ya wuce zuwa cikin gidan,kai tsaye sashensa ya wuce,ya tura qofar falon ya shiga,bata falon bata bedroom din,sannan bata toilet,sai zuciyarsa ta raya masa ko tana sashenta,don haka ya juya akalarsa zuwa can. Kaf ya gama dubawa bai ganta ba,sai abun ya shiga bashi mamaki,baya da niyyar shiga sashen hafsat din yau gaba daya,amma dole ya shiga ya gani ko tana can. Dukkansu suna falo ita da yaran,tuni falon ya koma 'yar gidan jiya,tana saman kujera zaune abinta,ta cika tayi fam da fushi,daga abbas din har widad din kowanne da nasa laifin a wajenta,donme yarinyar zata tafi gidan hajiya tayi zamanta?,uban waye zaiyi mata aikin da tafi kowa sanin itace zata yishi?,sannan abbas din me yake nufi da ita?,har azahar tayi amma ya kasa leqowa yaga lafiyarsu?,jikinta ya soma sanyi amma wani sashen na zuciyarta yana qarfafa mata gwiwa,tare da sake kambama mata laifukansa,duk da haka ta soma rasa qwarin gwiwarta,tasanshi....yana da danne zuciyarsa da hanata saurin fushi,amma kuma idan yayi fushin bashi da dadi sam. Boyayyar ajiyar zuciya ta sauke sanda taga shigowarsa,ya tsugunnawa yaran suka haye bayansa,fuskarsa na fidda murmushi,zuciyarsa dauke da tausayinsu,da babu alamun an musu wanka "Ina antynku?" "Daddy ta dawo?,ka kaini wajenta" mimi ta fada,abinda ya tabbatar masa kenan bata shigo ba kwata kwata "Ina kwana?" Ta fada ganin yana niyyar miqewa ba tare daya kalleta ba "Lafiya" "Ga breakfast dinka har ya huce baka ci ba" "Na qoshi" ya amsa mata yana ficewa riqe da yaran. Hankalinsa yadan tashi,ina ta tafi to?,ya tambayi kansa,sai ya jawo wayarsa ya kira layinta,a kashe layin yake,ya sauke wayar yana fidda iska daga bakinsa,gidan hajiya ta koma?,wata zuciyar ta gaya masa,har ya danna kiran layin hajiya sai ya kashe,idan ta tuhumeshi dalilin komawarta baisan me zaice mata ba,don haka ya kira layin umar. "Kana gida ne?" "Eh hajiya za'a baka?" "Weedad tazo?" "A'ah yaaya,tun jiya dai dana kawota gida" "Okay,karka cewa hajiya ga abinda na tambayeka" "To yaaya" umar din ya fada ,kafin ma ya qarasa abbas din ya katse kiran,sai yaji hankalinsa ya sake tashi. Muhsin ne ya fado masa,baiyi qasa a gwiwa ba yayi kiransa bayan sun gaisa kafin abbas dinma yace komai ya rigashi magana "Jiya jiya muke zancanku,inajin madam fa gobe ko jibi zata shigo ganin diyarta,nace ban da tabbacin kunxo weekend wannan satin" "Jiya mukazo,amma kuma banajin zamu jima zamu koma,yanzun ban fiya sakewa a bauchi ba,ayyuka sunyi yawa a kaduna" hira kadan suka taba sukayi sallama,don shima muhsin din fitowarsa kenan daga gida yana kan hanya yana driving. Wayar ya ajjiye,ya koma gefen gadon ya zauna hannuwansa cikin sumarsa yana murzata a hankali,yanason qwaqwalwarsa ta hasaso
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155