Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 153

Chapter 153

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,325 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

take takawa ba,kamar qayoyi ne zube a sassan nata gaba daya,haka ta dinga qoqarin dannewa ta fara gyaran sassan nata tayi ta kammala ta samu waje ta kwanta,wata muguwar kasala da nauyin jiki suna mamayeta,wanda a kwanakin nan sai sake gaba abun yake,har abbas din yace muddin sukaje hajjin suka dawo babu wani sauyi to ko bataso dole taje taga likita. Kamar wancan karon,wannan karon ma har bacci yadan fara fusgarta taji kamar an soma shaqeta,ta farka da sauri tana ambaton sunan Allah,sai numfashin ta ya ware ya koma dai dai,ta miqe a hankali tana sauke ajiyar zuciya,tana jin kamar ta fice a gidan kota yaya,sai ta zura slipper dinta kawai ta bude qofarta ta fito. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: Huguma* Page 100 A hankali take taka harabar gidan,tana jin kamar magnet ke janta zuwa waje,har ta kusa da gate din ta taka wani dan qaramin dutse mai tsini,zafin da ya soketa ya sanyata furta "Subhanallah" ta tsugunna tana dub qafar,Allah ya taimaketa bata huje ba,banda zafi da radadin da takeji kawai,koda ta dago sai ta tsaya tana duban qofar fita daga gidan dake kulle,tare da tunanin meye ya fito da ita a wannan daren?,saita girgiza kai ta juya tana komawa ciki. A hankali yake takowa zuwa dakin solar na gidan,don ya duba yana tunanin kamar sale bai kulle ba,cike da mamaki yake kallonta sanda take takawa zata koma sashenta,to daga ina take?,da alama ma bata ganshi ba,sai ya canza akala ya dosheta. A tausashe ya kamo lallausan tafin hannunta ta baya,tadan firgita kadan sannan ta waiwayo suka hada ido,ta saki waya ajiyar zuciya mai nauyi "Ina kikaje haka" "Babu ko ina,kawai na gaji ne" qarara ya karanto zallar gajiya da qin da takewa garin na bauchi a idanunta,sai ya jinjina kai "Muje kidan motsa,dama kin fara qiba ba dole ki dinga gajiya haka kawai ba".ya fada cikin salon tsokana yana lakuce mata kumatu,sai ta shagwabe masa tana tabe baki kamar mai.shirin sakin kuka,sakato.yayi yana kallonta tana sake tsumashi,don dama duka.yau din baiga wannan narkakkiyar shagwabarta ta ba,sai tsomoshi da shigar data dinga yi a sunan data dinga yi,duk sanda zai.shigo kuma sai yayi tozali da ita,ya dinga jin kamar ya dauketa subar gidan ya samu ya rage zafi,amma sanda yaga yawan jama'ar dake sashenta dole ya haqura ya hadiye,hafsat kuma ko a yanzun a dakinsa ya barta,ko kwana daya bata yarda ta bariwa widad din ba. Sassanyar iskar daren dake kada jikkunansu ta dinga haifar musu da wani yanayi cikin zukatansu,kada ma abbas din yaji labari,ya sake matsowa ya.kama hannunta suna ci gaba da strolling "Jibi zamu wuce,gobe ki kammala komai naki" da mamaki take dubansa har batasan murmushi ya subuce mata ba,bata dauka zasu koma da wuri haka ba,saboda taji yana cewa babu cinkoson aiki sosai,ya waiwaya a hankali ya sauke mata narkakkun idanunsa "Oh......murna ma kikeyi?" Nata fararen idon ta juya,lallausan murmushin dake qara fidda quruciyarta ta saki tana maida dubanta gefe "Dole ne ai......zan sake da uncle dina" murmushi mai dan sauti ya saki yana kallonta cikin mamaki,sannan cikin tsokana yace da ita "La la la.....eh lallai zan gayawa uncle muhsin,yarinyarsa tasan dadin mijinta" ya fadi qasa qasa dab da fuskarta,sai ta saki dariya tana zame hannunta daga nasa cikin jin kunya "Don Allah uncle karka fada" ya bita da sauri yana son cimmata yana sake tsokanarta kan sai fa ya gaya masa. Kamar yadda yace din kwana daya suka qara suka tattara suka koma kaduna abinsu,hafsat din tana ta cika tana batsewa,don ko fitowa batayi ba,daga daki sukayi sallamarsu suka gama. Ajiyar zuciya mai nauyi widad ta sauke sanda motarsu ta fita daga qasar bauchi tahau ta kaduna,har sai da abbas din ya juyo ya kalleta. *********Cikin wata muguwar zabura ta farka tare da miqewa zaune saman gadonta tana rarraba idanu,gumi sharkaf ya jiqa mata ilahirin rigar atamfar da take jikinta yana zartarwa cikin jikinta,kadan ya rage ta danne baby yusra dake bacci a gefanta,ji tayi kamar alqiyamarta zata tsaya,wannan wanne irin mafarki ne mai muni mara dadin gani?,me mafarkinta yake nuna mata kenan,widad dauke da baby tana miqo mata ita?,me hakan yake nufi?. Wayarta ta jawo tana dubawa kamar me neman wani abu,a sannan tayi ido hudu da number abbas,waddda itace kira na qarshe a jerin lambobin da aka kirata ko tayi kiran,awanni hudu da suka wuce,yake gaya mata jibi zasu iso bauchin,duk da sai da suka kusan dan samun sabani saboda a maganarsa ta fahimci da widad din xasuzo,abinda duk duniya ta tsana kenan a yanzu,take kuma neman hanyar da zata kawo qarshen faruwarsa. "Anya ba ciki ne da yarinyar ba?" Wata zuciyar ta gaya mata,saita hau girgiza kai da sauri kamar hauka sabon kamu,kai kace ita da wani suke magana a dakin "Inaaa,inaaa,bazaiyiwu ba" ta fada a fili,ba zata taba barin haka ta faru ba muddin tana raye,cikin abbas ace ya tabbata a jikin wata?,da kuwa lallai ta rako maya duniya,ta kuma cika hasararriya,iya qiyasta hakan kawai da tayi sai taji kamar zuciyarta zata tsinke tabar qirjinta,haka fa na nufin ya hada shimfida da ita?,ya santa a matsayin diya mace "Aah..... a'ah" ta sake fada tana girgiza kai da sauri. Ji tayi kamar ta kirashi tace su taho gobe,lallai kuma yazo da widad din, saboda tanason ganewa idanunta,shin da gaske ne abinda zuciyarta ke raya mata?,ko hasashe ne hadi da shirmen mafarki?. Wanann daren sai ya zame mata baqin dare,don tunda ta farka ta gagara komawa,saidai ta zauna idan ta gaji takai ta kawo har asuba ta risketa a haka. ********Sau biyu yana duba agogonsa sannan ya maida dubansa ga qofar fitowa daga sassanta,kusan minti goma tace tana zuwa,amma har yanzu bata fito ba,bata saba hakan ba,ba halinta bane,duk sanda zasuyi tafiya ko zasuje waje bata fiya bata masa lokaci ba,idan yace qarfe kaza kome takeyi ta kammalashi kafin wannan lokacin. Fitowa yayi daga motar hannunsa sanye a aljihun wandon yadin cashmere mai asalin kyau da tsada,wanda ya karbeshi qwarai,ya tunkari sassan nata yana fatan samunta lafiya. Saman kujera ya sameta zaune,tayi likimo a ciki kamar bamai shirin tafiya daga kaduna har bauchi ba,sai daya isa kanta sanann ta daga idonta ta kalleshi,saita miqe cikinmu mutuwar jiki tana sauko da qafafunta qasa hadi da gyara rufin veil dinta tana cewa "Sorry uncle,yanzu nakeson fitowa" "Me ya sameki?" Ya tambayeta kansa tsaye yana tsare sosai da idanu,qas tayi da kanta,batason gaya masa amai tayi kuma jiri take ji,batason hankalinsa ya tashi "Me yake faruwa dake ne?,ki gayamin gaskiya,karki yadda kicemin ba komai,jiya da daddare na ganki,tashinki nawa kina shiga toilet,na tambayeki kuma kikacemin lafiya qalau" yadda yayi tambayar cikun seriousness sai ya koma mata ASP abbas sosai,miskilin nan mai tsare gida da baiwa masu laifi tsananin tsoro,dole ta buda baki a hankali tace "Amai nayi,sai jiri,sai kuma fitsari da nakeji,idan naje yi kuma sai naga dan kadan,marata tayi kamar an saka dutse" shuru yayi yana kallon fuskarta,wani abu ya darsu a ransa,amma sai wata zuciyar ta kawar,don ba haka ya saba gani ba,ya miqa hannnunsa a hankali ya taba wuyanta ya janye hannun jin babu zazzabi "Subhanallah,amma shine kike ta cewa ba komai baby?" Kai ta langabe batace komai ba,sai qishirwa dake damunta,kamar ya gane me take nufi,ya isa fridge ya ciro mata ruwa mai madaidaicin

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});