Chapter 37
Chapter 37
hira ta fadi,wayar ta ajjiye gefe tana cewa "Aure ne ya tasowa danki" da mamaki ta kalleta "D'ana,wa kenan?" "Abbas mana" kallonta sukayi gaba daya cike da mamaki,abbas din da kowa yasan dabi'arsa,mutumin da ko auren hafsa dinma kamar bazaiyi ba saboda tsabar I don't care manner irin nashi da rashin baiwa lamarin soyayya muhimmanci? "Abbas din yaushe har yaga wata yanaso?" Faccalar tata da yara ke kira da gwaggwo fanteka ta fada "Tayani tambaya gwaggwo,na dauka ma bashir ko yaya sa'id zata ce,ko kuma Sunusi" kai ta girgiza tana murmushi "Abbas ne" kai suka jinjina su duka,mabruka tace "Ya cancanci ya qara aure dama tuni,wannan rayuwar da akeyi a gidansa bata da ma'ana sam,naga qoqarinsa ma,ganin baida wannan ra'ayin yasa ban taba tuntubarshi da maganar ba,ga 'yammata nan cike a dangi,ya zabi wata ya qara ko zai samu sassauci,haba abun na hafsa yayi yawa" kai gwaggwo ta gyada itama "Gaskiya dai,yammata kyawawa fa gasunan masu hankali,ita wannan din a ina ya samota?,cikin yan uwansa ne?,amma banji batun ba sai yanzu?" Gwaggwo ta fada cike da son jin wace?,tana fata ya zamana cikin yaranta ne,duk da tasan zaiyi wuya,don inda cikin nasu ne da tuni ta fahimta,amma rabonta da abbas a gidan tun sanda tayi wata rashin lafiya ya shiga ya dubata "Ba cikin dangi bane,wata yarinya ce diya take a wajen muhsin abokinsa,dukkanku ai nasan kunsan muhsin?" Ta fada tana kallon fuskokinsu, gwaggwo da tuni fuskarta ta sauya tace "Qwarai kuwa" sai hajiya ta dora "Yarinya ce ma,amma nutsuwarta da hankalinta ya bani abbas din xai samu nutsuwa a gidansa,zai kuma ce ayi ayi,a bari a bari" "Turqashi" gwaggo fanteka ta fada ba tare da tasan kalmar ta fita a bakinta ba,wani bacin rau na motsa mata,yaron da dukkan alamu suke nuna zaiyi arziqi cikin dangin nasu,taketa qulafucin ganin ta samu ta jogana diyarta,lokaci daya hajiyan ta wargaza fatanta da burinta ta dauko wata bare ta maqala masa?. "Banda abun hajiya ruqayya,gida bata qoshi ba za'a baiwa dawa?,gamu da yaran yammata duka sun tasa saiki dauko bare ki bashi?,duk da itama hafsan akwai alaqa amma ai baiyi alaqar sa da yaran kawunnansa ba ko?" Gwaggo fanteka ta fada tana dora murmushin yaqe kan fuskarta "Gaskiya nima wannan tunanin yazo min" mabruka ta fada tana gyada kai, murmushi hajiya tayi "Auren dangantakar ai bai amfana komai ba gwaggwo,gwara a gwada baren ko a nan za'a dace ko?" Kai ta kawar tana tabe baki,bacin rai iya bacin rai yana cikata,wanann babbar dama haka za'ayi asararta?,suna ji suna gani "Da dai kin sake tunani gaskiya,duk yadda bare yake da dadi ai baikai dadin dan uwa ba" "Hakane" ta amsa mata a taqaice,tasan halin gwaggwon da mita,ita kuma dama can bamaison dogon magana bace,gwggwon na daya daga cikin masu kushe aikin dan sanda a sanda abbas ya samu aikin "Dan sanda?,me na sama yaci ballantana ya baiwa na qasa?,kayan cin hanci da rashawa" wannan shine abinda taji tana fada sanda hajiyan taje gidan da kanta tana shaidawa kawunsa mijin gwaggwon cewa ya samu aikin,tun daga matakin constable saai yanzun da daukaka ta fara zuwa masa ake kwadayin hada zuri'a da ita?,duk haqurinta da kawaicinta ita din ba mahaukaciya bace. Hirar duka saita fita akan gwaggwo fanteka ta zama mara dadi,don haka bata jima ba ta miqe ta yiwa hajiyan sallama ta fice. *WIDAD* Sanda ta bude ido ta ganta qofar gidansu sai taga kamar wasa,kasa jira tayi drivern da uncle muhsin ya daukar mata shata har qofar gida ya fidda mata kayanta,ta sauka daga nan ta nufi gate din da gudu gudunta,ji take kamar zata bude ido ta ganta ta koma bauchi. Cikin sa'a kuwa tana buda gate din ummun ta hanga tsaye a farfajiyar gidan ita da kawunnanta,sanye da atamfa da kuma hijabi,hannunta riqe da carbi,da alama salla ta idar suka tasota,akwai zancan da sukeyi. "Ummunaaa" ta fada da qarfi sannan ta kwasa da gudunta,ta isa gabanta ta fada jikinta tana ruqungumeta. Sai da ummun tayi taga taga zata fadi kawu ya tareta "Ashsha,ashsha,zata kada mana uwa" sai ta saki dariya tana sakin ummun suka miqe tsaye dai dai ummun itama tana dariya idanunta akan fuskar widad din,kamar fa shekara bata ganta ba. "Ke dawa?,yanzu kike tafe?" Ummu ta fadi tana dubanta "Ni kadai yanzu yanzu na qaraso" "Iyeee,muhsin din barmin ke yayi ke kadai kika kamo hanya?,tabdijan ,zamu hadu dashi kuwa"kafin ta qarashe drivern uncle muhsin din ya shigo da jakankunanta,suka gaisa yace zai koma,ummu tace a'ah sai yaci abinci,suka wuce ciki ita da widad tace taje ta kawo masa abincin,su kawu kuma suka fice bayan an bashi wajen zama anan farfajiyar gidan. Zuwa wani lokaci sai ga sassan ummu ya dan cika da sauran yaran gidan,su Aafiya rafi'ah fareesa da sauran wadanda suke shekaru kusan daya,sun baibayeta tana ta basu labarin bauchi. "Kano fa tafi dadi Allah" ta fada daga qarshe tana yamutsa fuska,dariya sukayi mata "Daga baya kenan,bayan kin gama kwanakinki" dariya tayi tana cewa "Da gaske nake muku,bari kuga" sai ta wuce daki ta janyo jakarta,ta fidda jakar ledar kayan makeup din da hajjaa ta damqa mata tace inji abbas,tunda ta taho kayan suke daukan hankalinta,komai na ciki ya burgeta ya kuma yi mata kyau,harda takalmi me tsini irin nasu basma da aka sako musu a lefe,tayita maitar takalmin sai basman ta jefa mata harara "Ba baki zanyi bafa,kiyi addu'a kema Allah ya kawo me siya miki" fushi tayi tana tura baki tabar gurin,sai gashi ta sameshi sama ta ka,bayan shi harda mayafi da hand bag qarama mai matuqar kyau,a nan ta zazzage musu kayan,suka dinga santinsu,daga baya ta daukarwa kowa wani abun daga cikin kayan kwalliyar. ************* Kwana biyu a tsakani tana kitchen tana cin abinci suna hira da latifa,ta ajjiye warmer din data zuba abincin alhaji a ciki tana cewa "Ashe dan bauchi kika samo mana kuma" kallonta tayi tana ci gaba da cin abincinta,don ita har ga Alla ma ta manta da wani batu "Dan bauchi?" "Eh mana,naji abba mahmudu yazo suna zancan da alhaji ai" "Auho,wai abokin uncle muhsin" "Shifa" sai widad din tayi shuru kawai,don batasan me zatace ba,itadai ba sanin soyayya tayi ba bare ta tantance tana sonsa ko bata sonshi,kawai dai taji bata damu ba bata takura ba kamar sands ake zancan mahfood da ma'aruf. Sosai ummu ta dinga juya zancan bayan da mahaifin widad ya zartar da cewa an bawa abbas widad don,amma bata taba kawo cewa zasu nema aurenta a nan kusa ba haka,taji abun sosai a ranta,a yadda ta lura kuma shi mahmudu din a shirye yake da auren diyarsa,tasan watarana komai tsahon zaman da zatayi da qaunar da takewa widad su rabu dole ta aurar da ita,so a yanzun bataga nata hurumin da zata hanashi bada auren 'yarsa ba,tunda dukkan bincike da shaidu sun tabbatar da nagartar me neman auren kamar yadda musulunci yayi umarni. Amma babban abun shine,kishiya daya tabbata widad din nada ita,ta yaya yarinya kamar widad din zata iya fuskantar abu me wahala da zafi kamar kishi?,bata sani ba,saidai tana fatan ko mai zaizo da sauqi fiye da yadda suke zata. Kwanan widad din biyu da dawowa maneman auren abbas din suka iso kano qarqashin jagorancin uncle muhsin,sunga karamci irin na kanawa,duk da cewa su din ba kanawa bane usul,amma tunda an haifi 'ya'ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155