Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 44

Chapter 44

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,317 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

"Yanzun nan rabi'atu cousin din abban mimi tabar gidan nan,kinsan yarinya qarama yaje ya dauko?,ko shekara sha biyar bata cika ba?" Ta qarashe maganar tana tabe baki,takaici yana cikata. Dariyar da anty ummee ke qyalqyalawa tayi kasake tana saurara,sai daga bisani tace "Kai haba?,kice raino ya dauko?,tirqashi,to ke ai ta fadi gasassa,babu kuma wani sauran kishi da tashin hankali daya rage miki" "Kamar yaya?,haba anty ummee,idan za'a maka kishiya ma ai sai ayi maka isassa,wadda zaku goga da ita,ba wata can qasan qasanka ba" "Tabdijan" anty ummee ta fada sannan ta dora da cewa "Amma bansan baki da hankali ba sai yau,ke!,kishiyar da zata shigo ta goga da ke ai masifa ce,me yayi miki zafi?,to idan baki sani ba bari na gaya miki,Allah sonki yake shi yasa ya hadashi da qwaila,a yanzun ne za'a fara wasan ma da kyau,dama dukka tana hannunki,idan kika dauki.maganganun da mukayi dake rannan kikayi amfani dasu da kyau to ina me tabbatar miki yadda zaki bawa su mimi da nawwara umarni itama haka ne,ba boka ba malam,komai zaizo miki da sauqi,kina daga kwance kina sarrafa gidan a hannunki,yanxu saurara nayi miki wani sabon karatu......." Gyara zama tayi sosai tana bada hankalinta ga anty ummee din,tana hasashen qamshin gaskiya cikin msganganun anty ummee,sai taji ranta ya fara yin fes "Ina jinki" ta cewa anty ummeen...... *********Can quryar gadon ummu take kwance abinta,ta duqunqune waje daya,duk kuwa da cewa gidan a cike yake da baqi jikoki da surukan gidan,wanda a baya duk lokaci irin wannan tana tare dasu sunata sabgoginsu,sabanin yau da gaba daya take jinta wani iri,musamman da aketa mata abubuwa daya banbanta dana 'yan uwanta,aka kuma tsameta daga cikinsu. Tana daga kwancen tana kallon yadda ummu ita da warisha qanwar abbanta suketa hada kaya cikin manyan buhunhuna da kwalaye,wanda gaba daya kayan ummu tace nata ne,gidanta za'a kai mata ayi mata jeranta,itama ta samu nata gidan na qashin kanta,duk sanda ummu ta fadi hakan dadi takeji,amma yau gaba daya jikinta ya sanyaya,gwiwarta ta fara sagewa. Ana tsaka da wannan latifa tayi sallama ta shigo dakin ummun,ta tsaya daga bakin qofa yana gayawa ummu game gyaran jiki tazo,tunda widad din taji haka ta runtse idanunta tahau baccin qarya,ita kwata kwata batason wannan kwabe kwaben da aketa shafa mata yau wajen sati guda kenan,tana jin sanda ummun ta waiwaya tana qwala mata kira,amma sai ta sake lafewa cikin bargo tayi kamar bacci take,har ta gaji da kira ta juya ga latifa "Inaga kawai abar aikin nan haka,dama yau da gobe ne kawai ya rage" "To shikenan,bari na sallameta,yauwa......anty madina tace na gaya miki,kayan miyar ya za'a yi dasu,a markada gaba daya azubasu a freezer baya?" "Eh hakan yayi,don kada su lalace kafin jibin" "To shikenan" sai latifan ta juya ya fita,su kuma sukaci gaba da hada kayan,tana labe cikin bargo tana satar kallonsu,tana jin anty warisha na cewa "Banda abun ummu nawa ma jikin widad din yake,me ya sameshi ma da za'a mata gyara,ita da dama fatarta me kyau ce,a haka ma a karon banza daukan ido takeyi" "Wallahi madina ta matsa sai anyi mata,to ya na iya,itakam dama ta iya biyewa shirmensu,yanzu haka ta gama tsara musu komai,har kudi tasa muhsin ya karba musu wajen ango wai zasuyi walima" dariya warisha ta sanya "Kai,Allah mai iko,widad amarya" sai ummun ta murmusa kawai,don dauriya kawai takeyi batason aga rauninta. Tun tana labe tana kallonsu har baccin gaske ya dauketa,bata farka ba sai dab da la'asar,sanda ta tashi dakin babu kowa,sun gama aikinsu sun fice,bandakin ummun ta shiga ta daura alwala,ta shimfida abun sallar tayi sallarta,saita dan zauna tana jin hayaniyar su nabiha da sauran jikokin gidan,daga bisani ta gaza daurewa ta fito. Ido kuwa yayi mata caaa,mutane anata kiranta da amarya,saidai ta tura baki tayi gaba abinta,itafa shi yasa tunda aka fara baqin ma batason fitowa,a haka dai ta samu ta wuce sassan anty madina,a canne ta sake sosai abinta,harta manta da komai ma,har sai da anty madina tace lallai gobe za'a tsefe kai ayi kitso,a nan fa suka raba gaari da ita,saboda ta ambato maqiyinta wato kitso. *RANAR DAURIN AURE* Cikin jerin gwanon motoci na alfarma suka taso,tun daga garin bauchi zuwa cikin garin kano,qarqashin jagorancin jami'an tsaro da matakai masu tsauri,a ranar tamkar dai wani shugaban qasa,duk yadda ya dauki daurin auren sai ya wuce masa haka,tamkar dai dama ya dade da shiryama hakan,shi kansa cikin sabuwa dal din motarsa yake,yana seat din baya shi da suraj,sanye da wata danyar shadda wadda koda gari aka baka ka canki kudinta ba zaka ajeta nan kusa ba. Tunda suka taso fuskar hafsat ke masa yawo,tunda zancan ya tsiro bai taba jin tausayinta irin na yau ba,yana hangen yadda fuskarta ta sauya a sanda yake shiga motarsa cikin shigar dake jikinsa a yanzu,saidai zuciyarsa cike take fal da mamakin mene ya sauya hafsat?,me kuma ya kawo wannan sauyin?,yasan halinta ciki da bai,meye ya sanyata zub da makaman yaqinta?,wannan amsar ce har yanzu ya kasa lalubota,sai tarin wasi wasi da yake fama dashi kullum kwanan duniya. Tun daga titin farko zuwa abinda yakai layin da zao sadaka da ainihin gidan alhj salim mai fata cike yake tanqam da jama'a,idan akace maka jama'a ina nufin jama'a na gaske da zakayi tsammanin daurin auren wata hamshaqiyar budurwar data ci ta qoshi da karatu da wayewa akeyi,gaba daya unguwar a hargitse take sakamakon halartar daurin auren da manyan 'yan siyasa gwamnoni da kuma qusoshin gwamnati da abbas yake hulda dasu sukayi,jama'a dake tsaye a gefe guda suna ci gaba da lissafa gwamnonin da sukaga suna shiga unguwar tasu,sai da suka lissafa shida casss!. "Bisa dukkan alamu wannan karon babban kamu akayi a gidan nan,lallai yau sun jawo babban kai,kai kaga motocin dake ta gilmawa kamar daurin auren 'yar shugaban qasa?" Ire iren maganganun da matasa 'yan zaman banza a bakin layi keyi kenan,sunayi suna ci gaba da dorawa a lissafin su. Daga can cikin gidan kuwa a shaqe yake da jama'a,ko ina idan ka kalla hada hada akeyi,zaka tsammaci an dauki shekaru ne ana yiwa bikin tanadi,saidai hausawa suna cewa,kowanne aure da arziqinsa yake zuwa,wanna haka yake,domin kuwa a lokacinne aka baje lefen widad wanda ya iso ne tare da 'yan daurin aure,akwati mai sunan akwati,akwati na alfarma guda goma sha biyar,kowanne maqare da sutturu masu daukan hankali,duk wanda ya daga idanu ya kalla koda baiso magana ba sai bakinsa ya subuce ya furta "Ma sha Allah"mafi yawan mutane cikin family da wadanda ke cikin gidan dake zuba idon suga wani abun kaico ya bulla sai jikkunansu suka fara yin sanyi,musamman da labarin irin manyan mutanen da suka halarci bikin yajewa kunnuwansu.......... KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 29 Qarfe biyu na rana bayan sallar azahar aka daura auren asp abbas da amaryarsa widad mahmud salim akan sadaki naira dubu dari,dubban

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});