Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 83

Chapter 83

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,328 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

shigewa motarta,idanuwanta akan widad din,kamar zata gayawa hafsat sai kuma ta share,don bataga abinda yarinyar tayi mata bama,kawai dai hali irin na mata,taya kishin da bai shafeka ba. Sallar azahar kawai tayi ta fara gyaran gidan,duk da muguwar gajiyar da tayi,ta tuna sanda take dawowa daga makaranta,ummu tasa an hada mata komai,saidai tayi wanka taci abinci tayi shirin islamiyya,take qwalla ta kawo a idanunta,taji kamar ta watsar amma ba zata iya zama a datti ba,tsahon rayuwarta ko kadan batasan dauda qazanta ko datti ba,ummun nada wata irin mugu muguwar tsafta,kowa ya shaida,hakanan duk matan gidansu babu qazama. Tana gama mopping taji ana saka key za'a buda qofar sashen,ta tsaya a dan tsorace tana kallon qofar,har ya kammala budewa ya tura ya shigo. A kanta idanuwansa suka sauka,yayin da kuma ta sauke ajiyar zuciya tana jin tsoronta na zagwanyewa,baisan yadda akayi murmushi ya subuce masa ba,don ya gane tsoron nata taji da taba qofar da yayi,itama sai murmushin ya kubcewa fuskarta,ta kuma ji yar kunya ta kamata,tayi qas da kanta tana tambayar kanta me yasa ta fiya tsoro haka "Matsoraciya kawai" ya fada a hankali,murmushi ta danyi sannan ta turo qaramin bakinta gaba a shagwabe,kwatankwacin irin yadda takewa ummu,sai ya samu kansa da binta da kallo,batace komai ba shima haka,ya zauna hannun kujerar falon yana goye da hannayensa a qirji,lumsassun idanunsa nakan dan qaramin bakinta "Me kika ci?" "Ni?" Ta tambayeshi tana fidda idanu waje hadi sa taba lips dinta kamar mai tsoron wani abun, murmushi ya sake subuce masa "Eh me kikaci baki ajjiyemin ba?" Fuskarta ta narke a shagwabe "Nifa banci komai ba uncle,yunwa ma nakeji" ta fada tana shafa cikinta,shafaffen cikin nata yabi da kallo, idanuwansa suka kai har kan qugunta daya fito sosai ta cikin skeet din material na jikinta,ya janye idanunsa yana sauke numfashi,hirar da abokan aikinsa moses jackson da andrew sukayi yau ta fado masa a rai,har a lokacin suka cika shi suka kuma dameshi ya nemi tashi ya basu guri,sai suka dinga masa dariya suna tsokanarsa,ya sansu sarai,su din mayun mata ne,daya daga cikin abinda yasa ko kusa baya bari sukai ga ganin iyalinsa "Ina zuwa,bari na fito sai naga yau me za'a koya" sosai taji dadi,don har hakan ya bayyana saman fuskarta,tana son taga ta iya kalolin girke girke,saboda zumudi a falon ta zauna tayi jiransa,ba jimawa sai gashi ya fito. Sauri tayi ta dauke kanta sanda ya fito din,boxer ne a jikinsa sai wata armless shirt farare,kayan sun masu kyau sosai,saidai sun fidda qirar jikinsa. Har ya kusa isa kitchen din yaji bata biyoshi ba,sai ya waiwayo yana dubanta,tayi hanzarin sake dauke kanta gefe tana turo baki,shi wasu abubuwan idan yayi kamar baijin kunya wai?. "Ko baki shirya ba?" Ya tambayeta yana tsareta da idanunsa da suka rusuna yau din qwarai,kai ta girgiza ta kuma amsa masa ba tare data kalleshi ba "Na shirya.....amma.....amma" sai kuma ta kasa qarasawa "Amma me?" "Ka saka kaya don Allah mana" murmushin da bai shirya bane ya qwace masa,ya kalli jikinsa sannan ya dawo da dubansa kanta "Wannan meye a jikina idan ba kaya ba?" "Amma uncle,kalli gafarka kalli hannunka fa,ummu idan su yaa ma'aruf suka fito haka fada take musu fa" ta fada a shagwaben nan nata kamar zata saki kuka. Lallausan murmushi ya subucewa fuskarsa,for now yana ganin ya kamata ace ta fara sanin bambancin mutanen gidansu dashi,wannan yasa ya fara takowa a hankali cikin lallausan carfet din falon,bata lura dashi ba sai ganin mutum tayi dab da ita. Gabanta ya fadi,sai taja baya kadan,bai damu ba ya zauna a gabanta saitin qafafunta yana kallon idanunta dake cike da quruciya,ta kuwa bata fuska sosai,gabanta yanata faduwa "Akwai bambanci tsakanina dasu yaaya ma'aruf da sauran duk 'yan gidanku,ni mijinki ne,na biya sadaki an daura min aure,ni dake ya halatta muga komai na junanmu,mu taba juna,mu kwana guri daya....muci abinci tare,na ganki a duk yanayin da kike....koda tsirara kuwa....." "La ilaaaaa" ta fada da qarfi hade da wani irin kuka,idanunta a kansa, tsoronsa yana shigarta,ta kwashe qafafunta ta mayar saman kujerar kamar mai shirin zurawa da gudu. Wata dariya ta bashi,wadda a wannan karon ya kasa riqeta sai daya dara,hannunsa saman bakinsa yana qoqarin controlling na dariyarsa,he don't know what to do next kuma.....he don't know how to explain her, tabbas goyon kakace ta gaske,kuma symptoms ne na cewa ta samu tarbiyyar qwarai. "Shikenan,is okay,ya isa,bazan kalli jikinki ba,amma sorry for saying that.... shikenan?" Da qyar ya shawo kanta suka shiga kitchen din,yana hada girkin yana nuna mata kamar yadda suka saba,saidai sam taqi sakewa dashi,yana matsowa take komawa baya,gashi shi ba gwanin hira ba,biyu ta hadu,da haka dai ya dinga nuna mata har suka kammala. Ita ta zuba abincin a warmers takai dining,ta gyara kitchen din,ko kafin ta fito har yayi alwala ya leqo yace mata ya wuce masallaci,don haka itama tana gamawa alawar tayi,tayi sallah sai kuma ta dawo falon ta zauna, maimakon taci abincin amma sai taji ba zata iya ci ba har sai ya dawo,hakanan ta zauna zaman jiransa,wayarta na hannunta tana game tana dakon shigowarsa. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: Huguma* Page 54 Tana tsaka da game din taji mararta ta murda,ta dakata tana zare idanu jin wani abu mai danshi ya fara fitowa ta jikinta,gabanta ya fadi,kada dai ace wannan jinin ne da bataso yazo mata?,yanzu ya zatayi?,yi na qarshe da tayi suna tare da latifa,hankalinta a kwance yake,ta dinga kula da ita da ciwon mararta. A tsorace tadan miqe don duba jikinta,sai tayi sauri ta koma ta zauna saboda mararta data murda mata,ta dafe marar tana jin yadda danshin ke biyo jikinta,hankalinta ya tashi sosai,kawai sai kuka yazo mata,tana ganin kamar ba zata iya ba. gumi ya fara yanko mata ya gauraye da hawaye,ta soma jan majina tana raba ido. Sallamar da yayi cikin falon ya sanyata sake tsorata,sai taji kamar ta tashi ta zura da gudu,idanunshi a kanta,cikin mamakin yanayin da ya ganta a ciki,itama shi take kallo kamar wacce ta aikata wani mummunan abu. A nutse ya qaraso,hannayensa zube a aljihun wandonsa "What's happening?,lafiya?" Tsareshi taci gaba dayi da idanu,saidai qwalla ta cika idanunta fal,har bata iya ganinsa sosai,kallonsa take kai tsaye,kamar mai tsoron wani abu dake a jikinsa,maimakon ta amsa masa sai hawayen ya fara saukowa,ta sake dora hannunta saman mararta dake qara murda mata. "Me ya faru ne?" Ya sake maimaita tambayar yana sake qoqarin karantar fuskarta,hawayen dai taci gaba da fitarwa,a hankali idanunsa ya sauka saman hannunta,yadan kalli wajen na tsahon wasu mintuna,sai ya matsa gaba a hankali yana qoqarin miqa hannunsa,sai kuma ya janye yana duban qwayar idanunta "Ciwo cikin yake miki?" Kai ta gyada masa,Hawaye na sake saukar mata,sai ya sake matsowa yana cire hannunsa guda daya daga aljihunsa "Oh sorry....sannu,tun yaushe?" "Yanzu" ta fada a narke, zuciyarta tana

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});