Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 108

Chapter 108

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,317 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

masa mutum na gaba da zai kira ya bincika ko can taje,ya akayi ta iya fita daga gidan har ta fita ba tare da wani ya ganta ba?. Kasa zama yayi,sai kawai ya miqe ya dauki key din motarsa,tsoronsa daya kada yarinyar mutane ta bata cikin garin daba nasu ba,don yana da tabbacin zaiyi wuya ace shigowa akayi aka dauketa,don ya duba duk wani abu da zai iya bada alamun hakan bai gani ba,sai ya fita da yaran ya zubasu a motar suka fice daga gidan. Layi layi titi titi ya dinga bi yana dubata amma sam babu ita ba alamarta,har wajen azahar,ya tsaya a wani restaurant ya siyama yaran takeaway,ya dawo cikin mota ya zauna kenan wayarsa ta dauki tsuwwa,ya duba me kiran sai yaga muhsin ne "Kasan matarka ta tafi kano?" "Kano?" Ya tambayi muhsin din cikin mamaki qwarai,duk da dama yana cikin dimuwar son sanin ina tayi "Eh,yanzu muka gama waya da ummu,ta kirani tace na shaida maka,don tafiyar batayi mata kama data nutsuwa ba" qatotuwar ajiyar zuciya ya sauke yana jin wata nutsuwa na saukar masa "Alhamdulillah" ya fada a fili "Ka ganni a gefan hanya,tun dazun nake checking ko batayi nisa ba,ina shirin kira headquarter ma su bani mutane muyi aikin tare" "Subhanallah.......wanne irin sakarci ne wannan?,halan bata gaya maka ba bakasan da tafiyar tata ba" qaramin murmushi ya subuce masa,yasan sarai muhsin ba wasa,yanzun nan idan yace zai gaya masa gaskiya sai yace zai taba masa mata,shi kam a yanzun a yadda widad takai har cikin ruhinsa,baya jin ko ruwan sama zai lamunce masa ya taba masa ita "Me na tone tone?, tunda ka isar da saqon ummu shikenan,zan kirata" "Please abbas......kada kace zakayi kawaici,ka gayamin gaskiya" "Amma dai kasan indai kace zaka shiga tsakanin miji da mata zakaji kunya ne ko?" "I know.....but....." "But what?,shikenan kawai,ka qyalemu tsakaninmu ne" "Alright,Allah ya sawwaqe" daga wannan sukayi sallama ya aje wayar. Mamaki ya sake kamashi,yayin da qaramin murmushi ya subuce masa,rigimammiya ce yarinyar ta ajin qarshe,ya akayi har ta iya kai kanta kano?,da gaske batasan wannan rayuwar ba,batasan meye ma'anar aure ba at all "I will teach her......bazan bari ki subuce min ba,zan koya miki abubuwa masu zafin da zuciyarki zatayimin riqon tsauri da kyau" ya fada shi daya kamar me sambatu,abinda yake ji a ransa game da ita yafi qarfin a kirashi so,saidai wata irin zazzafar qauna da bai taba jin kamarta ba. Aje wayarta ummu tayi tana sauke dubanta ga widad data cusa kanta cikin pillow tana ta sheqa kukanta,kukan da tunda ta iso kano take kwararashi,tayi tambayar duniya amma taqi daga kai ta kalleta ma bare akai ga amsawa. Abu daya ne yasa hankalin ummu bai wani daga ba,widad din tata tayi fes tayi fresh,ta sake murjewa,ga kuma girma data qara,ta fara zama budurwa sosai,aure ya kwarzantata "Widad" ta sake kiran sunanta,shuru bata amsa ba sai kuka,tana tsoron su hada ido da ummun,tana ganin kamar zata gane abinda yayi mata a daren jiyan "Kinga idan ba zaki amsa min ba,ki daina kukan kada kanki yazo yayi ciwo" ummu ta fada tana miqewa "Ki samu waje ki kwanta" ta sake fadi bayan ta isa gaban wardrobe dinta ta fidda hijab,tayi sallar azahar sannan ta dauki wayarta ta fita tabar mata dakin,cikin ranta tana juyayin abinda ya faru,kodai ita da kishiyarta ne?,tunda muhsin ya sake kiranta yace abbas din yace babu komai,amma kishiya kuma......nawa widad din take da har kishi zai hadasu tayi wannan tafiyar afujajan. Da wannan tunanin ta isa falonta,ta iske latifa tana aje abincin rana "Batace komai ba ummu?" Latifan ta tambaya cikin damuwa "Uhmmm.....bata ce ba,nifa banga wani alamun damuwa tattare da ita ba,nafi zaton shirmenta ne kawai ya motsa,idan kuwa haka ne zataci qaniyarta,ta yaya zata dauko qafa daga bauchi ta taho kano ba tare da izinin mijinta ba?,baya ga haka kuma ita kadai a wannan rayuwar da muke ciki?" Ajiyar zuciya latifa ta sauke "Ayi mata dai a hankali ummu,ai ruwa baya tsami banza" "Kin manta widad din ne ashe" ummu ta amsa mata,wanda tana rufe bakinta momma tayi sallama "Barka da rana ummu" ta fada tana 'yar fara'ar da batakai zuci ba,da kallo ummu ta bita "Ke kuma daga ina da rana haka fatsar fatsar?" Murmushi ta danyi tana wuwwulga idanunta wai ko zataga himilin kayan widad din da akace an ganto ta shigo ita kadai "Zan fita ne nace bari na leqo,idan kina da canji ki aramin" "Canji?" Ummu ta maimaita cikin mamaki,saboda irin wannan ita baya hadata da surukanta "Eh....eh" dan shuru tayi tana karantar momma din,sai kuma tace "Allah ya kyauta,shiga kitchen ki yiwa latifa magana ta baki" amsa mata tayi sannan ta nufi kitchen din tana kalle kalle a falon ta gefan idanunta. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 71 Har ta karbi kudin ta dawo da baya,tunda dama.ba karbar kudinne a zahiri ya shigo da ita ba "Wai niko latifa,akace widad tazo ita kadai da tsakar ranar nan,kuma na shigo banganta ba,ko tana bandaki?" Kallonta latifa tayi,banda tana ganin girmanta cewa zatayi tana cikin masai ba bandaki ba,amma saita dauke kai tana ci gaba da aikace aikacenta "Kinsan ni bana shiga hurumin wasu,iya matsayina nake tsayawa a gidan nan,inaga da kin koma wajen ummu da kika wuceta a falo,zakifi samun bayani" ta gane sarai magana takeson gaya mata,sai kawai tace mata "Eh,kuma haka ne" ta juya ta fita tana tabe baki a ranta tana fadin "Koma dai meye idan tayi wari maji,oh.....yau ga 'yarso a gida,da alama ma dai auren ne ya balle,dama waye zai dauki wannan sakalcin nata,shafaffa da mai". Tun tana kukan har bacci yayi awon gaba da ita ba tare data sani ba,bata farka ba sai wajen qarfe uku na rana,ta miqe ta zauna tana murza idanunta,ta manta shaf a dakin ummu take,komai ya dawo mata,tabi dakin da kallo,dai dai lokacin ummun ta buda qofar ta shigo,tazo ne dama fa dubata kota tashin. Qin yarda tayi su hada ido,sai ta kauda kanta tana kallon qasa "Ki tashi kiyi wanka kici abinci" kai ta gyada,sannan ta zuro qafafunta qasa ta miqe,har yanzu wajen tana jinsa wani dundurus,duk da zafin zuwa yanzu ya baje. Ruwa me zafi ta hada sosai tayi wankan,wajen yin tsarki taji ruwan dumin ya mata dadi a wajen,ta dinga kwararashi har sai data ji wajen ya saki gaba daya sannan ta fito,ta samu ummu ta aje mata doguwar riga cikin ire iren kayanta da bata gama kwashewa ba daga gidan,ta sakata tayi sallar la'asar da aka soma kira sannan ta daure ta fito falon ummun. Su biyu ta samu,ita da anty madina,madinan batasan da zuwanta ba,don bata gidan,yanzun ta dawo ta biyo kawowa ummu sallahu data bata,baki ta riqe cikin madaukakin mamaki da kuma farinciki "Widad din ummu..... innalillahi,yaushe kika zo,babu sanarwa bare nayi miki kyakkyawar sauka?,saida kika bari ranar da bana nan fisabilillahi" murmushi ya qwace mata,karon farko kenan tunda tazo gidan. Tabe baki ummu tayi tana duban anty madina "Waye ma yasan da zuwan nata?,koshi mijin nata ai baisan zata zo ba,muma ganinta kawai mukayi" gaban anty madina ya fadi "Kamar yaya?,widad me ya faru?" Tambayar dai dai take da sukar bulalai a jikinta,ta yaya zata iya ce musu ga abinda yayi mata?,sai kawai ta fara hawaye bayan ta

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});