Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,298 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ba,zan maka lamuni dai taje zuwa sanda komai zai lafa" murmushi yayi "Zahra ta dade tana nacin a bata widad ummu,su kansu su nujood zancansu yaushe zatazo,tunda anyi haka kawai ki haqura ku barmin ita" "Banyi alqawari ba" ummu ta shaida masa kai tsaye. Sanda widad din ta dawo falon bayan ta sauya kaya ummu ta shiga ciki ta duba dashishin da za'a girkawa alhajin,har yau har kwanan gobe tsufa jin dadi ko wadata bai hana dattijuwar matar aikin abincin mijinta ba. Cikin hikima uncle muhsin yake bugun cikin widad kan batun,tuni ta fara share qwalla,sai ya ajjiye spoon din hannunsa "Kinga share hawayenki,ba wanda zai miki auren dole,dake zan koma ma na kaiki wajensu nujood,ai zaki je ko?" Duk da nisa da ummu shine abu da tafi tsana,amma a yanzun sai takejin shine mafi dacewa,kawai tabi uncle muhsin din,tayi nisa da garin ko abbanta zai haqura da qudurinsa,bata da zabin da ya wuce wannan,don haka ta gyada kai hadi da cewa "Zanje uncle" "To shikenan,share hawayen ki bani labarin izifinku nawa yanzu a islamiyya" hira ce ta barke tsakaninsu,harma ta manta da fargabar tafiya tabar ummu,saima zumudin matsawa daga garin,ko banza ta gujewa wani ma'aruf abbanta dama auren da ake shirin qaqaba mata. Uncle muhsin shine auta ga ummu a maza,daga shi sai halimatu kenan,kuma qani ga abbanta da suke uwa daya uba daya,shi din ba mazaunin kano bane,yanayin aiki ne ya kaishi bauchi,da farko ma kamar bazaije ba,saida ummu ta qarfafa masa gwiwa,ta kuma nuna masa aiki ba inda baya kai mutum,yanzu haka shekararsa kusan goma sha uku da aure,yana da yara hudu,diyarsa ta farko widad ta girmeta da shekara kusan daya,dan boko ne sosai,yana da sauqin kai som mutane da kuma kirki,widad na ji dashi cikin dukka tulin qannen da mahaifinta ke dasu,saboda yadda yake nuna mata kulawa da kuma janta a jiki. Da kansa uncle muhsin din ya zauna da yayan masa mahmudu,ya sha fama sosai kafin ya gane abinda yake kwatanta masa,don daga bisani dole ummu da alhaji suka sake shiga maganar sannan ya janye qudurin nasa,ba kuma wai don ya haqura da maganar bane gaba daya,wannan ya sake qarfafawa uncle muhsin gwiwar tafiya da widad din "Taje dai ta huta,amma ban bar muku ita ba,kada ma kazo kace min ga zance ga magana". Kamar wasa sai ga widad tana murnar tafiya,har ta fara hada kayanta da kanta ma,latifa ita da anty madina sunata dariya "Ba cinya ba qafar baya,Allah dai yasa a qarke qalau kada ku dawo ranar da kukaje" suke tsokanar uncle muhsin sanda sukaga widad din nata shiri. Kwana uku kacal ya qara suka tattara sai bauchi,ranar da zata tafin gaba daya 'yan rakiyarsu har bakin motar uncle muhsin din,latifa ke riqon jakarta,tana ta tsokanarta "Uwar dakina kada dai zama yayi dadi a manta dani" widad dake sanye da atamfarta dinkin doguwar riga tayi dariya tana qwamewa gaban motar uncle din "Bazan manta dake ba inna latifa,kedai ki zuba ido zakisha tsaraba" dariya ta saki "To Allah yasa" itama ta amsa tana dariyar,suna dakon uncle muhsin ne,yana rabawa yaran gidan da sukayo masa rakiya kudi,'yan dari dari ne sababbi qar,baya rabo dasu,ya kammala ya dawo cikin motar ya zauna yana sake waina injin motar sosai,ummu ta zagayo ta durqusa tana musu addu'ar sauka lafiya,sannan ta zura hannu saman cinyar widad ta ajjiye mata kudi "Gashinan,kada kije baqon guri hannunki babu komai" murmushi uncle muhsin yayi bayan ya kalli kudin "Banda abinki ummu me zatayi da kudi?" "Ina ruwanka kai dai?" Ta amsa shi,tana gyara yafen mayafin dake saman kanta "Nidai bance a riqemin yarinya acan ba,aro na baku" ta sake jaddada masa abinda yake ranta,sai yayi dariya kawai yana tayar da motar,dai dai sanda widad kema ummun godiya,duk da itama din batasan amfanin me kudin zasuyi mata ba. Har motar ta fice daga harabar gidan suna waigen juna ita da ummun "Zauna sosai kada ki baro kan naki a gida kije bauchi da iya gangar jiki" uncle muhsin ya tsokaneta,sai tayi dariya tana zama sosai din,saidai tun a lokacin taji ta fara kewar gida,taji kamar ta koma,to amma idan ta tuna abinda ta gujewan sai taji dadi,hankalinta kuma yadan kwanta,ko ba komai za'a daina zancan,tana saka ran maganar ma tabi ruwa ta huta. Suma shirin ficewa a unguwar motar ma'aruf din ta sako kai,uncle muhsin yadan dakata kadan,sai ta lafe sosai ta kwantar da kanta saman cinyoyinta ta yadda bazaya ganta ba,ma'aruf din ya gaidashi sukayi sallama,uncle muhsin yaja motar sukayi gaba yana dariyar widad din cikin ransa,quruciya sai abarta. *ZAFAFA BIYAR 2023* IDON NERA Mamuhghee KI KULANI miss xoxo A RUBUCE TAKE Huguma RUMBUN K'AYA Hafsat rano DAUDAR GORA Billynabdul Account number 0022419171 Maryam sani Access bank Saiki tura shaidar biyanki ga 09033181070 VTU OR MTN RECHARGE CARD 09166221261 AL'UMMAR NIJER SU TUNTUBI WANNAN NUMBER +227 90 16 59 91 Thanks for choosing us *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 09 Suna tafe a hanya uncle muhsin din yana janta da hira,ta saki jiki sosai sunata hirarsu da yake abokin hirarta ne dama,a nan ya fahimci interest dinta itama game da karatu,da yadda take da kaifin basira,tun suna hirar har suka gaji kowa yayi shuru,saita maida hankalinta ga kallon titi da yadda suke wuce dazuzzuka,can qasan ranta ta dinga jin wata kewa tana shigarta,zuciyarta ta karye,suna dada yiwa kano nisa. Tun tana iya bin hanya da kallo har baccin ya soma fusgarta,babu jimawa kuwa yayi awon gaba da ita,ta saki jiki sosai tana barcinta abinta. Bata tashi farkawa ba sai da uncle muhsin ya iso qofar gidanshi ya tsaya yana jiran mai gadi ya bude masa qofa,idanunta ta bude a hankali tana murzasu hadi da budesu da kyau tana qarewa wajen kallo. Tun a sannan tasan ta shigo baqunta,ta kuma shigo sabon waje,quaters ne dake da qarancin jama'a tare da qarancin gine gine,saidai kuma duka manyan gidaje ne ta wajen,tana nan zaune har ya buda gate din gidan ya dawo ya shigar da motar. Sanda ya kashe motar waiwayo yayi yana tsokanarta "Yar qauyen kano yau gata a bauchi" kasa magana tayi saboda kewar ummu data fara shigarta,sai murmushi kawai data saki,dai dai nan matar gidan ta iso. "Kai kai kai.....abba wa nake gani haka?" Ta fada tana dariya gami da murza bdanunta,saboda baice mata da widad din zasu taho ba "Wa idanunki suka gani?" Shima ya fada yana dariyar "Tabdi,wai Allah na,anya kuwa ba gizo idanuwa kemin ba?" "Shafa kiji dai" ya sake fada yana dariya gami da qoqarin fitowa daga motar yana duban widad din "Fito mu shiga ciki" yace da ita yana fita daga motar "Gaskiya na ciri tuta,abba wacce irin addu'a ne ka yiwa ummu ta baka widad?" Ta sake fada tana karbar jakar hannun widad din tare da sake bude mata qofar motar sosai. Tare suka jera zuwa ciki hadiyya matar uncle muhsin da yaranta ke kira hajjaa nata mamakin zuwan widad din "Saurin me kike ne?,zakiji komai fa" cewar uncle muhsin. Tunda suka shiga falon gidan ta gane yaran gidan basa nan,da yake ranar makaranta ce,har dakin yaran hajjaa ta rakata sannan tace da ita "Ki alwala ki sallah,ki shiga kitchen da abinci ki diba kici,su nujood din sun kusa dawowa,yanzun nan zaki gansu" a nan dakin ta barta ta

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});