Chapter 38
Chapter 38
da jikokinta suna amsa wannan sunan. Cikin girma da mutunci gami da karamci suka gabatar da neman auren abbas ga widad din,aka sake jaddada basu,suka nema alfarmar karbar kudin aurensu harda sadaki,take alhaji yasa aka karba komai,suka karbi roqonsu na daurin auren sati mai zuwa. A ranar zancan auren widad ya fara yawo a dangi,abinka da family house,kowa idan yaji zai gayawa na kusa dashi,bugu da qari widad din 'yar gatan ummu,mai masoya da kuma tarin abokan adawa. "Uhmmm,sunje sun zaba mata miji ba,ai dama wannan yadda akaci buri a kanta nasan sai me abun hannu zasu bata" wannan shine abinda wasu suka dinga fada,musamman da suka samu labarin muqamin da ya riqe a gwamnatin bauchin,da kuma wanda yake kai yanzu,gani sukeyi uncle muhsin ya dauketa ne dama kawai don ya aikata hakan. Ita kuwa sam batasan ma me akeyi ba,don har ta koma islamiyya,wadda tun tafiyarta qaunar makarantar bata bar ranta ba,sanda ta koma din sai ta samu basu wani tsere mata ba,tunda ta dora daga inda ta tsaya a bauchin. **********Karfe shida saura na yamma suka iso gidan ita da Aafiya rafi'ah da widad din,bayan tasowarsu daga islamiyyar,gab da zasu shiga gate din gidan Aafiya ta kalleta "Nifa zancan bikinki naji ummanmu tana yi,wai nan da sati daya" "Nifa abinda yake hadani dake tsokanarki" widad ta fada tana watsa ragowar alawar data siya cikin jakarta "Wallahi nima haka naji,don kafin mu tafi islamiyya naji umma tana waya a karbo atamfofi akai mana wajen mai dinki" "Mahaukata,sai kuyi ai" widad din ta fada tana yin gaba abinta tana dan waqenta. Bata ma tsayasu ba ta zarce sassan ummu abinta,tana sallama a falon ta soma zare hijabinta daya dameta,gashinta mai santsi ya ware,don dama ita din ba ma'abociyar saka dankwali bace,tafi sanya hula,itama ba ko da yaushe ba,sai ummu tayita fama da ita. Ummu da anty halima ne a falon "Anty halima ina nabiha?,kikace idan zaki sake zuwa tare zaku zo?" Widad ta fada tana barewa alewan ta tura bakin yaron anty halima dake kan cinyarta. Da kallo anty halima ta bita,tana dan jin tausayin widad din "Oh ni sadiya?,wannan wacce irin amarya ce ummu?" Dan murmushi ummun tayi,ita kanta tausayin widad din takeji,har yanzu ma bata zauna tayi magana cikakkiya da ita ba kan auren da tasan widad din batasan meye shi ba,bata kuma da labari cikakke akan yinsa. "Au ina yini?" Ta fada tana dariya bayan ta tuna nata gaidata ba,ba kuma tare data maida hankali ga maganarta ta farko ba "Lafiya lau widad,nabiha zasuzo,sai satin biki in sha Allah" "Allah ya kaimu" ta fada tana gyada kai hankalinta kwance,saita dubi ummu a shagwabe "Yunwa wlh nakeji ummu,dazu banci abinci ba Aafiya ta matsamin na taho mu tafi" "ki wuce latifa tana kitchen ki karba" "Tom" ta fadi tana wurga jakarta ta zarce kitchen din,yayin da dukka su biyun suka bita da kallo. Ummu ce ta fara dauke idanunta tana sakin ajiyar zuciya,anty halima tace tana dariya "Wai,wa yaga widad amarya" kai ummu ta kada "Tausayinta nakeji halima,ban taba kawo rabuwarmu a nan kusa ba" tabe baki anty haliman tayi "Kaji ummu,to mu da aka rabu damu din tun bamu kai haka ba me ya samemu?,gamu ragal damu?,itama zata ware ne kamar kowacce mace" kai ummu ta girgiza "Ba zaki gane ba halima,dukkanku kunfi widad wayo sanda aka muku aure,kawai don lokaci yayi ne ba yadda zanyi,amma ban shirya kaita wani uwa duniya ba" "Tunda dai babanta ya bada ita,alhaji kuma ya goyi baya dole saidai ayi haquri,yanzu kawai yadda za'a tattarata akaita bata iya komai ba,kunbi duk kun shagwabata,bata iya komai ba,komai yi mata akeyi" anty halima ta fada tana mele baki,ta rasa wanne irin so ummun takewa widad?,tamkar ma ba mahaifin widad din ta haifa ba,ita ta haifa,ko ita diyarta ta cikinta bata jin tana mata son da takewa widad din. KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 25 Murmushi kadan ummu tayi,qarara ta hango kishin widad a idanun halima,ta rasa me yasa haliman ta kasa sabawa da hakan,sai ta gyara zama "Mu dinma uwayenku da sanda aka aurar damu banajin munkai ya widad din,a gidan muka iya abubuwa,tun mun kwamacala har muka qware,yanzu gashi ba'a ce mune muka haifeku ba" kauda kanta anty halima tayi,tasan dama duk yadda takai bakai isa ka fadi wallen widad ko ka kusheta ga ummun ba. Yau din tun qarfe takwas ta qudunduna a bargo cikin dakin ummu,bayan ta gama qarewa kayan data gani jibge a dakin ummun kallo,tun shekaran jiya taga ummun nata jibge kaya a dakin nata,itadai bata ce ga dalili ba,ta dan tura baki taja bargo abinta,bacci yau takeji da gaske,don ko sassan anty madina da aka cika ana hira yadda aka saba taqi zama,bugu da qari kuma yadda suketa faman kiranta da sunan amarya,wanda ta dauka duka tsokana ce irin tasu yau ta sauka a kanta suka tasota gaba,ita kuma bataso. Fakare tayi tana jiran bacci ya iso,gefe daya tsoro tsoro takeji saboda ummun tana wajen dattijon mijinta,buda qofar dakin akayi a hankali,sai ta tada idonta tana kallon me shigowar ba tare data tashi ba,ummun ce,hannunta dauke da babbar baqar leda "Yauwwa,gwara ma da bakiyi baccin ba,tashi" kai tsaye ta miqe din,don itama tanason yiwa.ummu tambayar "Ummu...wai wannan kayan,na wanene duk sun cika miki daki?" "Kayan aurenki ne" ta amsa mata gaba gadi tana kallon fuskar widad din,cike da fargabar yadda zata kalli zancan,kada ta watsa musu qasa a ido. Idanun ta fitar,fuskarta babu wani emotion saina mamakin "Aurena ummu?,duka wadan nan kayan?" Kai ta gyada mata "Eh,harda wasu ma" ta fada tana bude mata ledar "Wannan babanku yace ki zaba iya wadanda kikeso za'a dinka miki" da mamaki ta sake duban ummu "Wai duka nawa ne?" "Kadanma kika gani shalele ta,za'a kawo lefe a kawatuna duka naki" murmushi ya subucewa widad,kawai taji farincikin na kamata "Harda kayan kwalliya ma irin nasu anty ramziyya?" "Sosai,inajinma yafi nasu" ta fada tana murmushi ganin bata dauki zancan da zafi yadda ta saba ba,da wannan hirar ummun ta dinga hilatarta tana jaddada mata zancan auren,quruciya ta sanya widad din bata wani damu ba,saima cika da tayi da zumudin zuwan ranar da za'a kawo mata kayanta,wanda ummun tace mata sai ranar daurin aurenta. ********Wasa gaske saiga shirin biki nata kankama daga bangarensu widad,sam bata wani damu ko daga hankalinta ba,abinda ya baiwa kowa mamaki,yayin da wasu kuma hankalinsu ya kwanta ganin bata qi yadda ta saba ba,'yan adawa kuma fadi suke "Shegiya dama da guntun wayonta,gashi tayi luff kamar ba ita taqi 'yan uwanta har mutum biyu ba" oho,ita dai sabgar gabanta takeyi kawai,tana lissafin ranar da za'a kawo mata kayan kwalliya. Daga bangaren su abbas kuwa maganar ta fara yawo,da yawa daga cikin dangi wadanda sukaci burin zuwan wannan rana,ranar da abbas zai qara aure labarin baije musu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155