Chapter 41
Chapter 41
banaso,ka riqe kyaututtukan ka!,wallahi baka isa kuma ka qara aure ba!,ni kadai ce matarka!,ni kadai zaka zauna da ita duniya da lahira!!" Ta fadi da wani qaaraajin tana dubansa da idanunta da sukayi jazur suka kuma firfito kamar wadda aka shaqawa borkono. "Cool down,karki bari ranki ya baci kinji......zauna muyi magana ta fahimta dake" ya fada with softness yana yunqurin kamota ganin tana shirin miqewa,fusgewa tayi tana jifansa da wani mahaukacin kallo,ta bude bakinta cikin madaukakin sauti ta fara gaya masa dukkan maganganun da suka zo bakinta,miyagun kalamai na aibatawa da kuma tunzuri,sai ya koma kawai ya zauna,ya harde hannayensa a qirji yana kallonta a nutse. Ya sani ita aka tabo,kasancewa batun lamari na kishiya a wajen mace babban al'amari ne da ba kasafai suke iya daukan wannan mummunan labarin ba,wannan dalili ya sanya ya bata dama taketa fadin dukkan abinda taga dama ba tare da yayi yunqurin dakatar da ita ba,duk da kalamanta akwai wuce gona da iri da kuma zaqewa da yawa,amma yayi haquri ne ya jura saboda yasan wani ciwo ne da radadi daga zuciyarta,wanda shine ya dasa mata shi yanzu yanzu. "Shine ka zauna kana kallona?, wallahi abbas baka isa ba,wallahi nace bazaiyiwu ba" sai tayo kanshi,tana rarumo kwalaben turaren dake saman madubinta ya soma qoqarin jifansa dasu. Cikin qwarewa ya dinga sanya hannu yana cafe duk wadda ta jefo,ganin ko daya bata sameshi ba sai tayi kukan kura ta jawo bed lamp ta wurgota. Bai samu tareta ba,amma ta dakar masa hannaye,glass din jiki kuma ya yankeshi ba tare daya lura ba,saita tsugunna inda take ajjiye takalmanta ta fara daukansu suma daya bayan daya tana masa ruwansu. Miqewa yayi cikin zafin nama da mazantaka ya isa gareta,ya kama dukka hannayenta ya hade cikin hannunsa guda yana kallon fuskarta,ransa ya soma baci,ya dubi sashen dasu mimi ke a kwance,Allah yasa babu daya cikin abinda take wurgowa daya samesu "Ki nutsu hafsat!,ki nutsu!"ya fada shima da murya sa mai kaifi da zurfi,saita dakata din ta kece da wani irin kuka "Macuci azzalumi,Allah ya isa tsakanina da kai,kuma wallahi wallahi baka isa kayi wannan auren ba,idan ba haka ba sai na baka mamaki nima dakai da munafukar da zaka auro,ka fita ka barmin dakina,ka fita bana son ganinka!" Ta fada da mugun qarfi,saiya sakar mata hannaye,ya kuma taka a hankali zai fice,sautin amon muryarta ya dakatar dashi "Kazo ka kwashesu,suma bana son ganinsu,ka debesu daga gabana!" Dawowa yayi a nutse yadan tsaya gabanta yana kallon yadda ta birkice gaba daya,jikinta banda tsuma babu abinda yakeyi,yasa hannu ya kwashe dukkan yaran ya fita dasu. Ya jima yana mamakin baqin kishi it n na hafsat din,ashe abun ya wuce yadda take tsammani?,wanne irin hauka ne wannan?. Bai lura da hannunsa dake zubar jini ba sai daya kwantar da yaran saman gadonsa yaga stains na jinin a jikin blue bedsheet din nasa "Ya salam" ya fada sanda yake duba wajen,sai yaga ya yanke sosai,don haka ya koma dakin yaran dake sassanta don ya dauko first aid kit. Tun daga falonta yana iya jiyo gunjin kukanta,irin kukan da mutum yake zama dirshan ya bude dukka muryarsa yayishi,tausayinta sosai ya saukar masa a rai,sai ya kasa wucewa ya sake komawa ta dakin,sai biyu yana murda handle din yana jinsa a riqe da alama ta kulle ne daga ciki,ya sassauta murya yana kiran sunanta "Open the door please, don't hurt yourself fa" "Ka tafi ka bani waje abbas,na tsaneka,banason kallon fuskarta,ka tafi nace tun ban bude na lahantaka ba!!" Duk yadda yaso ta bude din taqi,sai ma wasu miyagun kalmomin da zagi da yake antayo masa,hannunsa nata digar jini,dole ya haqura ya dauki kit din ya koma dakinsa ya gyara wajen. Daren ranar baccinsa ragaggene,haka yayita kai kawo tsakanin dakinsa zuwa sassanta,yasan halinta da muguwar baqar zuciya,yana fargabar kada ta illata kanta ita daya kulle a dakin,saidai duk sanda yaje din zaiji motsinta,wannan ke bashi 'yar nutsuwa kadan. *Arewabooks: Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 27 Washegari yaran da suka tashi suka gansu wajen babansu sam basu damu ba,murna suka dinga yi abinsu,shi ya dinga tiri tiri dasu,ya shiga kitchen da kansa ya hada musu breakfast mai kyau,da yake ya iya abubuwa masu sauqi hakanan cikin abinci,saboda yanayin karatun da yayi. Sunci kuwa sosai kamar ba gobe,sai ya zauna yana kallonsu,zuciyarsa na gaya masa basa samun kamarsa,duk da store dinsa cike yake da cima kala kala,wani abun har ya rube ko ya lalace batayi amfani dashi ba bata kuma bayar ba saboda baqar rowa,yayi nasihar yayi nasihar har ya koma fadan amma a banza,mutum ne shi mai bajintar wadata iyali tun samunsa baikai haka ba,tun rank dinsa bai kai haka ba,baya son iyalinsa suga wani abu a wani gidan da babu shi cikin gidansa,to amma kusan duk wannan qoqarin nasa a yawancin lokuta a banza yake tashi. Ruwan tea kawai ya iya sha bayan ya tabbatar sun qoshi,duk ransa a jagule in yake,saboda har sanann hafsat bata bude qofarta ba,yayi knocking yayi har ya gaji,ya ajjiye mata nata breakfast din bakin qofa amma baiga ta bude ta dauka ba. Bayan duka sun gama ya maida kwanukan kitchen,ya zage kamar yadda ya saba yawa yawan lokutta ya soma gyaran sassan nasa,yayi masa qal yadda yakeso,ya canza bedsheet da sauransu,ya hada duk abinda ya cire da kayansu mimi da yayi musu wanka cikin laundry basket,ya aje inda mai wankinsu zai dauka,sannan shima ya shirya kansa sannan suka dawo falon hafsat din,koda wai zataji motsinsu ta bude qofar. Saidai har suka gama zamansu ba ita babu dalilinta,a taqaice dai har zuwa azahar bata fito ba,yanason fita masallaci sallah amma kuma bazaiyiwu yabar yaran su biyu cikin gidan ba,don ita mimi din ma ba wani cikakken hankali ne da ita ba,dole ya hada kansu suka wuce sassansa,acan yayi sallar,sai la'asar daya dawo dora musu abinci yaga babu plate din daya ajema hafsat din,da alama yunwa ta korota,ta bude qofa ta dauka kenan,sai ya saki qaramin murmushi ya wuce kitchen din. Har dare suka kwanta babu wanda yaga qyallinta,a taqaice dai washegari kusan abinda aka maimaita kenan,don haka a kwana na ukun ya shirya yaran da kayansu ya wuce gidan hajiya dasu. Kallon farko data masa tasan hatsaniya ke tashi a gidan,ta kuma san bata rasa nasaba da batun aurensa,bata matsa da jin ba'asin kawo yaran ba,saboda tasan shi da zurfin ciki,zaiyi wahala ma ya iya zama yana fadin cikinsa,ta daiyi murna da zuwan nasu,don ba zata iya tuna lokaci na qarshe da hakan ta faru ba. Ya jima a gidan,sai yammaci sannan ya wuce,a sannan tuni nawwara tayi bacci a jikinta,ta baiwa muneera ta kwantar da ita,sai data dawo ta zauna gefan hajiyan "Hajiya da alama anty hafsat fa......" "Na sani muneera" hajiyan ta katseta,saita rausayar da kai "Shima uncle,ya haqura kawai hajiya suyi zamansu mana,irin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155