Chapter 64
Chapter 64
yanayin da scent din yake son samu daga jikinta ba.......zaya so ace tana fidda kalar launin qamshin daya daga cikin turarukan da yafi so,yake kuma siya ya ajjiye mata komai tsadarsu "Wai kin daina kishina ne?" Ya fada da wata irin cool voice,ita kadai tasan abinda ya saukar mata a zuciya,inda yasan yadda takejin zuciyarta a duk sanda yake magana kawai da wata macen,da wala'alla har ya mutu bazai sake kallon kowacce diya mace ba baya ga mahaifiyarsa "To amaryar taka ce naga bata iya komai ba,kaima kuma baka iya rainon da aka kawo maka ba" yadda tayi maganar yadan sansano sautin kishi a ciki,duk da yaso jurewa amma saida murmushi ya subuce masa,sai ya saketa kamar yadda taketa kiciniyar qwacewa daga hannunsa,yasan zata ce masa kada yara su gansu "Tunda gaki basai ki tayani rainon ba" baki ta tabe "Saboda ni ka aurowa ita?,yanzun ma......" Maganarta ta yanke sanda ta fuskanci gangancin da take shirin aikatawa,saita waske "Yanzun ma tausayinta nakeji,an aura mata tsoho" ta qarasa fada tana yin gaba,taku uku ya cimmata,sannan ya bata amsa "Tsohon ashe yayi.kasuwa,tunda har ya samo qaramar yarinya ko?" Cikin Zuciyarta sai taji kamar.magana ya gaya mata,don haka taja bakinta ga tsuke,bata sake saka.baki.akan magabar ba,gudun kada ta tafka shirme tana samu tana tsallakewa da qyar. Yana shiryawa yana mata magana cikin hikima akan ya kamata ra gyara dakin yaran dama nata dakin da kyau,baki ta tura,shi kome qoqarinka me yasa sai ya cika gyara?,sai yayi challenge naka?,duka ba hidimar dafa masa abinci ke cinye mata lokacin ba?,ita sai taji har ta qagu ya koma Kaduna,ta yadda zata samu ta miqe qafarta da kyau. Tana gama sallar isha'i ta shiga wanka saboda tuna alqawarin data daukarwa anty deena,data fito ta shirya cikin kayan bacci kai tsaye,wasu riga da wando ne kalan pink da suketa burgeta cikin kayan lefanta,dama Allah Allah take ta sakasu,tana gamawa ta maida hijab dinta tabi lafiyar gado tana hamma,yau ma a nan dakin zata kwanta tare da latifa,idan suka kwana tare sai tayita jin kamar ummu. Dai dai sanda take rufe bakinta sabida doguwar hammar bacci da taketa saki latifa ta turo qofar dakin,shigowarta kenan bayan ta maida kwanukan da sukaci abinci daki "A'ah,me zan gani?,yauma?" Ta fada tana kama baki,sai widad din ta waiwayo tana dubanta "Me nayi?" "Ke da zaki wuce ki tafi dakin mijinki?" "Dakin miji kuma umma latifa?,kamar wata 'yar iska?" Tayi maganar tana maida kanta saman pillow ta dora da cewa "Yanzu da kanki kike cewa ma naje dakin wani" dariya taso qwacewa latifan,lallai da gasken gaske wauta da quruciya sun yiwa widad din yawa,saita qaraso gefan gadon ta zauna tana qoqarin fahimtar da ita. Sam widad din ta gaza kai hankalinta kan abinda take nufi,sai ma tubure mata da tayi kan babu inda zata,dai dai lokacin hafsat tazo kiranta tazo suci abinci,nan ma tace ta qoshi ba zata ba,ran hafsat din ya mata dadi,amma duk da haka a gaban latifa dashi kansa abbas din saita nuna bataso haka ba "Rabu da ita,yi serving dina" ya fada kansa tsaye sanda yake dan diban abincin kadan kadan yana baiwa nawwara a baki,wadda tayi dare dare saman cinyarsa,saita soma zuba masa abincin,amma bata rabu da zancan ba,don lallai ta nuna masa ita ba'a son ranta ba,har sai da yace "Will you keep quiet madam?,ko sai na saka gum dina na rufe miki bakin?" Ya fada yana jifarta da hararar wasa "Kai bakasan na fika farinciki da haka ba" ta fada cikin ranta,amma a zahiri bakin nata taha ta rufe,bata sake tashin zancan ba. *********sannu a hankali kwanaki suka fara tafiya,widad cikin gidan har a sannan tana matsayin baquwa,baquwar dake ganin kulawa da damuwa daga idanun hafsat,harma taje ganin matuqar kirkinta fiye dana ja'afar,yadda su mimi ke kiranta da mommy haka nan itama take kiranta dashi,tana mata kallon da takewa anty madina ne,tana kallonta a matsayin uwa ko wata babbar yayarta,gefe guda kuma sabo ne ya shiga tsakaninsu dasu mimi da nawwara,musamman mimin,a nan sassanta suke kusan yini. Idan ka samu widad din dasu mimi zakayi tunanin yayace da qannenta,kusan ko yaushe suna tare,sosai suke debe mata kewa,idan lokacin da zasu shiga kitchen yayi ita da latifa zasu shiga tare,to amma kusan fiye da rabin hankalinta yana kan yaran,don haka ba wani abun arziqi take tsaiwa ta koya ba. Ta bangaren abbas shima tana masa kallo daya ne,matsayin uncle muhsin take kallonsa,saidai wani bangare na zuciyarta haka kawai yake cika da tsoronsa,ta kasa sakewa dashi kwata kwata,babu fashi,a kullum zai shigo da safe yaji basu da matsala,ya sake dawowa da dare ya tabbatar da komai lafiya,zaman cin abinci dasu kuwa ko sau daya bata taba yarda ta zauna din ba,hakan yana yiwa hafsat dadi matuqa,yadda yarinyar je tattare kanta waje daya,take kuma dari dari da komai nasa,wannan shike haska mata lallai komai zai tafi mata a sauqi. To hakanan duk yadda latifa zata lallabata taje sashensa kona awa daya ne sai ta dawo taqi,sai tayi mata kamar bata ji ba,ta kwanta ta hau barcinta,tare suke kwana da latifa din a daki daya,gado daya,wannan yana debe mata kewar ummu qwarai da gaske. *******A nutse cikin takun nan nashi dake nuna zallar karsashi da lafiya da tsiyayyar qirar jikin da yake dashi yake takowa zuwa harabar gidan,kunnensa maqale da waya yana amsa kira,hannunsa daya riqe da key din motarsa. Sanye yake wani yadin kuftan mai kyau da daukar ido,anyi masa aikin hannu mai tsadar gaske,sosai kayan suka zauna masa,abbas din ba daga baya ba wajen iya saka manyan kaya,kowacce shiga daukansa takeyi,saika gaza tantance wadanne kaya ne suka fi masa kyau. A hankali ya zare wayar daga kunnen nasa yana katse kiran, hankalinsa yana kaiwa kansu, suna daga gefan farfajiyar gidan,mimi ce da widad,widad din na daga zaune gefan wata tukunyar fulawa,sanye take da wata doguwar riga mai santsi mai dogon hannu,tana hade da hula ne daga bayanta,bata saka hular ba,tadai saketa,lallausan gashinta mai santsi da tsaho yana matse cikin qaramin band,jelar ta buya ta bayanta,fararen qafafunta na slipper blue din slippers,color din dake matuqar fidda hasken fatarta. Mimi kedan garo mata ball,itama tana daga zaunen sai ta sanya qafarta ta maida mata,yau din tunda ta tashi bata da wani cikakken kuzari,shi yasa ma tace wa latifa ba zata shiga kitchen kallon girkin yamma ba,itama bata matsa mata ba,ta barta suka fito da mimi din,wadda hafsat ta tafi unguwa ita da nawwara,ta barta a nan,don qememe taqi binta,ba kasafai ta fiya damuwa da bin hafsat din unguwa ba,tafison zama da widad. Idanunsa ya janye dsga kanta ya nufi parking space,yana hangosu har sannan ta cikin mirror din,shi kansa a yau sai yaga babu wannan kuzari da kazar kazar din daya santa dashi,idanunsa ya kuma daukewa yana rufe motar ya tayar da ita ya fice daga gidan a hankali. A nutse yake tuqinsa kamar kullum,yana tafiya yana lura da abubuwan dake faruwa saman hanya,gidan hajiya ya nufa kai tsaye,don dama a yau din can yayi niyyar zuwa,sai dare kuma ya tsara zai fita daga unguwar. A hanya ya tsaya ya siyama hajiyan abubuwan da yasan tana sha'awa kamar yadda ya saba,sannan ya wuce,mintuna qalilan ya iso unguwar tasu. Tun daga farkon layinsu matasan da suka ankara da shigowar tasa suka biyo bayansa, mutum ne shi mai matuqar kirki tausayi da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155