Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,302 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gaba,daqyar kamar wadda aka yiwa dole tace "Tom" saita maida dubanta ga yaran ba tare data wani damu da yi masa sannu da zuwa ba ko tambayarsa hanya "Kuka sani dafa muku indomie ashe ma ba yunwa kukeji ba kuka katsemin bacci na" sai taja dan siririn tsaki "Saiku tashi muje kuci,idan kuma bakwaci a bayar da ita" mimi ce ta maqale kafada "Nidai mommy banason indomie" ta hasala sosai,dama ga fadan da yayi mata "Baki isa ba tunda na dafa sai kunci" "Ji mana" ya dakatar da ita,saita waiwaya tana dubansa,ya ritsata da idanun nan nasa dake kassarata,bata buqatar ta sauko don haka ta kauda kanta "Babu lallai yaro sai yaci abincin da ya riga ya ginsheshi,ki deba musu cikin abinda kika dafa min,sauran ki kawomin shi falo na" fuska ta bata,cikin jin shakka murya ciki ciki tace "Ni ban dafa maka komai ba" ya zuwa yanzu mamakin hafsat ne ya kamashi,cikin son danne bacin ransa yace "Saboda me?" "To ai bakacemin ka taho ba" "Bakisan yau zan dawo bane?"ya jefa mata tambayar cikin salo na tsitsiye,saita rasa amsar bashi,saboda wayar qarshe da sukayi bayan sun gama ya tura mata tex na date da time na dawowar tashi,kawai ta share ne saboda tana jin haushinsa,tazo kuma ta raba dare tana kallo,shi yasa da safen ta dinga barci kamar matacciya,sai da yaran suka dameta da kukan yunwa sannan ta rarrafa ta dora musu indomie,ta rage wutar ta koma baccinta bayan ta zuba komai da komai,da nufin ta sake matsewa kafin ta dahu,a wannan tsukin ya shigo,kuma har ya kwashe yaran bata snai ba,uwa uba ma kuma manta shaf da batun dawowar tashi. Idanunsa ya lumshe yana jinjina kai,ya taka zuwa gaba kamar bazaice komai ba,sai kuma ya dakata ba tare da waiwayo ba yace "Ki gyaran sashe na,sannan ki dafa min abinda zanci kafin na gama" daga wannan ya wuce bandaki. Da kallo ta bishi har ya kammala wucewar ya rufe qofa,janye idanunta tayi tana sauke gauron numfashi,sai kuma tsaki ya biyo baya,bata dauka zai dauki abun da sauqi haka ba,duk da tasan halinsa,yakan iya share laifi yayi kaman ba'ayi masa ba,amma horonsa kuma sai yafi miki ciwo fiye da komai,a duniya babu namijin da ya taba yi mata abinda abbas din yake mata,batasan wanne irin so take masa ba daya samu dama da yawa yake juyata har haka ba,saita dakata da tunanin ganin bata da isashen lokaci,ta tarkata kan yaran ta sauka dasu zuwa sashenta,ta juye musu indomie din duk da sunce ba zasu ci,ta kunna musu kallo ta wuce kitchen tana tunani me zata dafa wanda bazai jaa mata lokaci ba. Sai data kwashe mintuna kusan biyar tana dawurwurar abinda zata dafa masa cikin kitchen din,daga bisani ta yanke dafa masa jallop din taliya,duk da tasan cewa kwata kwata bata cikin lissafin abincinsa,hasalima saboda ita da yara yake ajjiyeta,banda haka tasha zamanta,to amma kuma bata da wani sauran option,hakanan bata da idea din wani abu me sauqi da sauri baya ga taliyar,kuma koma meye dai oho,indai ta dafa ta bashi ai ta fita ko babu sabulu. Sai data wanke tukunyar da zata dafa abincin a ciki,saboda tun jiya datayi baqi qawayenta ta bata su gaba daya,ta kuma jiqasu sa zummar yau idan ta tashi aiki ta tsaftacesu,sai gashi kuma yayi mata dawowar ba zata. Tana hada girkin tana mita cikin ranta,taja tsaki yafi a qirga "Dole ne ma na samo 'yar aiki gaskiya,haba dame zaka ji?,kashe kanka zakayi?" Ta dinga gunaguni ita daya,tuntuni takeson daukar mai aiki,amma saboda wani banzan ra'ayi nashi da kuma kafiyarsa yaqi aminta,alhali kuma aiki yayi mata yawa,ga yara gashi karan kansa. Sanda ta gama ta juye masa a plate ta sanya wani ta rufe ta fito,a falon ta samu su mimi duka sun sheme barci ya daukesu,bacci dama sukeji,amma yunwa da rashin kyawun tsaftar jikinsu ya hanasu yin baccin,ga indomie dinta nan sunci wadda zasuci sauran sunyi wasa da ita sun sake d'aid'aita falon,sai a sannan ta lura da wankan da yayi musu,baki ta tabe "Kwado sarkin tsafta,ni wallahi bazan kashe kaina da wannan shegen son tsaftar taka ba" daga haka ta sanya kai tana ficewa zuwa sassansa. Zaune ta sameshi saman kujera riqe da remote yana kallon labarai,armless white shirt ce a jikinsa da three quarter wine color,ya miqa dogayen qafafunsa saman center table din yana kadasu a hankali. Kallo daya yayi mata ya amsa sallamarta yana maida dubansa ga tv,ta qaraso dab dashi ta janyo daya table din ta dora plate din abincin ta matso masa dashi,a gajiye take jinta tubus don bata sanyawa ranta wannan aikin ba,don haka ta koma kan daya daga cikin kujerun ta zauna "Sannu da zuwa" hankalinta ya bata tayi masa a sannan,sai daya sauke qafafunsa qasa ya zauna sosai sannan ya isa amsa mata,ya bude abincin yana kallonsa yayin da ita kuma take kallonsa tana jiran me zaice,kamar bazaici ba,sai kuma ya sanya fork a ciki ya debo yakai bakinsa. Idanunsa ya ragewa girma yana tauna taliyar cikin bakinsa,kamar mai tauna mutuwa haka yaji,baisan ya zaima hafsat ba,baisan sai yaushe zata nutsu ta gyara tukunyarta ba,kudade da yawa ya kashe wajen ganin ta iya abubuwa da dama saboda inganta rayuwar aurensu amma har yau babu riba,tana sane?,mugunta ce ko kuma meye?,idan kishi ne da nuna masa zallar soyayya a baki ita din tana kan gaba,amma ya rasa abinda yake damunta. Salin alin ya maida murfin ya rufe sannan ya miqe ya wuce bedroom dinsa,binsa tayi da kallo tana jiran taji me ya faru?,ba jimawa ya fito sanye da jallabiyya mai santsi dinkin qasar morocco mai gajeran hannu "Ina key din mota ta?" Ya tambayeta yana sanya qaramar hula saman kansa,maimakon ta amsa masa saita miqe ta wuce gaba zuwa dakin nasa,ta jawo locker inda ta zuba muqullan ta dauko ts miqa masa,saiya karba "Banaso na dawo na samu wajen nan a haka" ya fadi yana yin gab,tana son tambayarsa ina zashi amma bai bata damar wannan ba,tun daga fuskarsa har yanayin yadda yayi mata ya fice ba tare daya bata hanzari ba. *_ASSALAMU ALAIKUM_* _Barkanmu da dare da fatan kowa yana cikin qoshin lafiya_ _Akwai abinda muka turo tallansa na WOMEN EMPOWERMENT PROGRAM(KUDI KE KIRA),so please duk wadda batayi pyment ba ta jira tukunna kada tayi,akwai wani CONFIRMATION da mukeso mu samu a kansu_ *Idan komai ya daidaita zamu sanar muku* *_idan kikaci gaba da pyment kuma bada yawunmu ba_* *Muna godiya sosai* *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 12 *Widad* Dole qanwar naqi ta fara sakin jikinta,duk da cewa gaba daya hankalinta yana kan gida,abu daya ke mata burki ya sanya mata ko kwanto da kuma qaunar komawa idan ta tuna case din data bari a gidan. Satinta guda uncle muhsin ya maidata makarantar dasu nujood ke zuwa,baiyi shawara da kowa ba,hakanan bai gayawa kowa ba,yayi dai karambani ne,yana fatan karambanin nasa ya samu nasara. Makarantar boko ce hade da islamiyya,qarfe hudu ake tashi zuwa biyar yawanci duka yara suna gida,sosai widad tayi murna,don ita dinma akwai son karatu,cikin sati guda ta sake sosai abinta,zaka dauka tsohuwar daliba ce. ********** K'arfe takwas da rabi na dare ne,bayan su widad sun gama cin abincinsu su wuce daki,daga hajjaa sai uncle muhsin kawai a falo din,ta qaraso tana ajjiye masa zobon

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});