Chapter 68
Chapter 68
hada kaya harta fara murna,ta dauka zaya ce gida zasu,amma sai taji yana kiran wata kaduna,ta fiddo manyan idanunta waje da suka fara hada hawaye "Kaduna?....."sai ta kasa qarasa maganar,kai ya jinjina mata yana nazartarta,ta fiya tsoro, tsoronta yayi yawa,kuma ya lura maza kawai takewa haka "Eh,gobe da safe" shuru tayi tayi qas da kanta qwalla na zuba,bai lura kuka take ba,yamiqe yana cewa "Bakwa buqatar komai?" Saita jinjina masa kai kawai,ya taka a hankali ya fice,cikin ransa yana ayyana yadda zasuyi rayuwa a kaduna da ita ahaka a yadda take,itama din bata wuce raino ba. A haka latifa tazo ta tarar da ita,ta sata a gaba da tambaya,sai ta gaya mata,sannan ta dora da cewa "Ni gida zan tafi ba wani kaduna,wajen ummu zamu tafi" zama sosai latifa tayi tana kwantanta mata lamarin aure,ta kuma gaya mata gaskiyar ta taho kenan,ita da gida saidai ziyara,saita rude mata,ta dinga rusa mata kuka tana lallashinta,daga qarshe dai sai data kai ga kiran alhj mahmud. Cikin hikima irin ta d'a da mahaifi ya dinga bata baki,tare damata alqawurin zaizo can din,kuma ta fadi kome takeso zaisa a kawo mata "Ni banason komai,kawai komai a gidan,kullum shima sai ya tambayeni idan inason wani abu" wannan magana tata ta sake kwantar masa da hankali,ta kuma qarawa abbas martaba da bayyana asalin nagartarsa,abban nata bai barta ba har sai da ta sake sosai sannan sukayi sallama. Tsaf latifa ta hada mata kayan da dukka tasan ya kamata ta tafi dasu,itama ta faka nata kayan a boye. Bayan fitarsa sassan hafsat din ya wuce don yaga yaransa,a falon yayi sallama,sunata wasa da kayan bacci a jikinsu,babu alamun an musu brush da alwala ba bare wanka,fuskarsu duk jirwayen bacci da sauransu. Tana tsaye a dining area tana gyara kayan breakfast din data hada tun safe,bayan ta hana idanunta barci. Satar kallonsa takeyi,ya mata wani irin kwarjini da kyau,wani irin annuri ke fita daga fuskarsa,abinda ke qara mata soyayyarsa kenan da kuma kishinsa,kome ya sanyawa jikinsa karbarsa yakeyi. Cikin nutsuwar nan tasa ya duqa yana tarbar yaran nasa,suka shige jikinsa kowa a cikinsu yana son masa hira shi kuma yana biye musu,ta gaji da tsaiwa ganin baiko waiwayota ba,ta soma baro wajen zuwa inda suke tsugunne "Ina kwana" ta fada ranta yana suya,a dakeka a hanaka kuka?,wanne irin al'amari ne wannann "Lafiya"ya amsa a taqaice,ranta ya sake sosuwa,halin nasa ya motsa kenan,shi duk abinda ya faru kenan bai ga nasa laifin ba sai nata?. "Ga abincinka nan an gama" "Am okay alhamdulillah" ya bata amsa yana miqewa dauke da nawwara,sai itama ta miqe,zuciyarta na tafasa amma tana yunqurin danneta "Amma kada ka yimin haka,tun dazu na tashi saboda kai fa?" "Nace na qoshi" ya amsa mata bayan ya zube mata manyan idanunsa,abinda ya sage mata gwiwa ta koma baya ta jingina da kujera "Abinda ya faru jiya ne kenan har yanxu bai wuce ba?" Waiwayawa yayi yana sake kallonta,shi take ma tambaya kenan?,bai amsa mata ba sai ta baiwa kanta amsa "Kayi haquri,inasonka dole nayi kishinka,kishin ne ya sanya idanuna suka rufe,amma ya riga ya wuce,Allah ya tsare hanya" ta qarashe maganar tana jin kamar ta saki kururuwa,ita kadai tasan me takeji a zuciyarta,wani irin kisan mummuqe ne takewa zuciyarta,wadda bata saba da boye boye irin haka ba,komai nata gaba gadi take yinsa. Lokaci daya xuciyarsa yaji zuciyarsa ta karye,ta kuma sassauto,amma baiji gamsuwa akan lamarin hafsat din ba,ya santa,kamar hawainiya take akan wasu al'amuran,bashi da tabbacin ta fada din da gasken gaske "Kaji?,nace kayi haquri" ta kuma fada,a wannan karon duk yadda taso tare qwallar baqincikin dake idanunta sai da suka sulmiyo,abinda ya qarasa karyashi kenan,son sam baya qaunar kuka,sai ya sauke nawwara yacewa mimi taja nawwaran suje dakinsu su dauko brush dinsu. A tausashe ya sanya hannunsa ya jawota zuwa jikinsa,tun baice komai ba ta saki kuka mai nauyi,wanda ke dauke da saqonni da yawa da zuciyarta keson fesarwa,baki da ruhi sun gaza amintuwa da hakan saboda burin cikar wani buri. Baice komai ba sai hannu da ya sanya a bayanta yana dan bubbuga wa kadan kadan,har zuwa wani lokaci,ya dagata yana duban fuskarta "Is okay,wipe your tears" ya fada bayan ya miqa hannu ya yago mata tissue din dake kusa dashi,bata musa ba ta karba ta fara goge fuskarta ta,saidai zuciyarta har yanzu tana jinta kamar an fusgeta daga qirjinta an jefa gidan bread. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 44 "Ma sha Allah" shine abinda latifa ta fada bayan ta gama feshe widad da turaruka masu taushin qamshi "Duba ki gani" ta fada tana matsar da ita gaban madubi,murmushi ne ya subucewa widad bayan ta kalli kanta da kanta ta madubin,tayi kyau irin yadda takeso,yau latifan tana da nutsuwar data mata ado haka "Gaskiya nayi kyau" ta fada tana dariya hadi da kallon latifa,sai dariya ta kama latifan "To sai a bani tukuici ai" "Duk kudin da uncle yake ajjiyewa ki dauka" ta fada tana murmushi,girgiza kai latifa tayi "A'ah,ba ruwana da kudin miji da mata,tashi kije qila sun fito,sai kun dawo" tana murmushin maganar da latifa ta fada da kuma farincikin yadda tayi kyau a saman fuskarta ta fita zuwa farfajiyar gidan. Dai dai lokacin da gafsat ke tsaye gaban motar abbas,sanye da baqar doguwar riga mai sulbi da jan mayafi babba data yafawa kanta,fuskarta kamar ko yaushe,babu alamun kwalliya ko d'is,sai maiqo maiqo da takeyi,don tana tsaka da barci mimi ta tasheta akan ta fito inji abbansu zasu wuce shopping. Sam bata ankara da widad ba sai data kusa gab dasu, qamshin ta dake kadawa cikin iska shine abu na farko daya fara jan hankalinta ta gane akwai baqo a wajen,sosai ta zuba mata idanu,sai taji gabanta ya fadi,wanne irin kyau yarinyar nan ke dashi?,ta tambayi kanta da kanta,take taji gaba daya ta muzanta,duk da cewa dama ba wani ado tayin ba,rigar da ita ta kwanta baccin,ganin bata jima da sanyata ba kuma a motar gida zasu fita su dawo yasa batayi wani sha'awar canzawa ba. Kafin ta dawo daga duniyar tunanin data lula widad ta iso wajen,sunata kakaci ita dasu mimi suna qyalqyala dariya abinsu "Ina yini momy" ta fada fararen jerarrun haqoranta suna bayyana,sautin siririyar muryarta ta karade kunnenta,ta kuma dawo da ita hayyacinta "Lafiya.....lafiya lau" ta fadi tana bude bayan motar da sauri "Ku shiga ku zauna,mimi ku shiga" ta fada tana duban idanun widad,kama hannunsu nawwaran tayi,ta fara saka mimi sannan itama ta shiga tana ci gaba da jansu da wasa. Wata ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke,har yanxu qirjinta bugawa yakeyi,kyawunta yana damunta,yana kuma son ya zame mata barazana,tafi yarda dari bisa dari kyawunta na daya daga cikin abinda ya fusgi hankalin abbas dinta,ta yaya zata gusar da wannan abu dake shirin zame mata barazana?. "muje ko" ta tsinci muryarsa dab da ita,sai ta dan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155