Chapter 4
Chapter 4
ya sanyata fara tattara kayan cikin hanzari,tana gudun ko abba ne ya fito zaya tafi,ta tabbatar idan ya ganta a wajen fada zata sha. Wanda ta gani a wajen yana niyyar fitowa daga motar tasa ya sanyata sauke ajiyar zuciya,tasan cewa kome zatayi ba kulata zaiyi ba bare ya hanata,don kuwa tsahon tasowarta ta sanshi amma ba zata iya tuna rana daya da magana ta taba shiga tsakaninsu ba. Kamar yadda ta zata din kuwa,ko a yanzun ma dauke kansa yayi ya soma rufe motarsa sanna ya jefa key din a aljihu ya kuma soma takawa yabar wajen. Da kallo ta bishi tana tabe baki gami da jifansa da harara,har sai da ya bacewa ganinta sannan ta dauke dubanta daga wajen,a hankali take tattare kayan tana maidawa cikin ledar,qasa qasa take magana ita daya "Wallahi banaso,bayarwa zanyi,ni ba wani aurensa da zanyi,dan iska kawai" dif maganar tata ta yanke,sai kuma tahau zaro idanu cikin tsoron kada wani ya jita,sai data tabbatar babu motsin kowa sannan ta qarasa kwashe kayanta ta kuma fito. Isowarta farfajiyar gidan yayi dai dai da budewar gate din gidan,qaramar motar qirar 406 ta danno kai ciki,sai ta dakata daga yunqurin isa sassan anty madinan tabi motar da kallo,sai kuma ta saki murmushi har dimple din dake kwance saman kumatunta hagu da dama ya lotsa,saita cilla da gudu gudu sauri sauri zuw wajen motar,cike da zumudi da kuma murna. Sanda ta isa daura da motar tuni mamallakiyar motar ta kasheta tana yunqurin fitowa "Anty dina sannu da zuwa" waiwayawa tayi sashen da widad din take tana niyyar dauko jakarta daga back seat na motar "Widad rigimammiyar ummu,ya na ganki a gida kuma?" Murmushi tayi tana leqen cikin motar da alama akwai abinda take nema "Anty secondry zamu tafi fa,muma mun zama manya kin manta?" "Au anyi haka fa,kice zamu sake samun qarin 'yammata cikin gidan namu....." "Anty wai ina aysar ne?" Ta tambayeta cikin katsar numfashinta "Gashi nan a daure" ta fada tana nuna mata shi a kujerar dake kusa da tata cikin baby car seat,zagayawa tayi da hanzari "Don Allah anty kwantomin shi" "A'ah widad......ke kanki yaushe ummu ta daina goyaki?, barshi yanzu zan fito na kunceshi" bata rai tayi,wai me yasa kullum suke maidata baya,bayan ita kanta tasan girma take?,to idan ma har yanzu yarinyace ita a wajensu me yasa suke mata zancan uncle mahfood?,dole daga bisani anty dina ta ciro yaron ta miqawa widad shi,sannan suka nufi sassan mahaifiyarta tana ankare da widad din. "Ke kuma wanne tsautsayin ne ya sanyaki daukar yaronki ki bawa wannan yarinyar?" Cewa momma mahaifiyar anty dina bayan shigarsu babban falon sassan nasu. Kafin anty dina tace komai widad din ta rigata magana "Momma Allah na iya fa,gash.i nan ma ni na daukoshi tuyn daga parking space" ta fadatana turo baki,wanda ke sake nuni da zallar quruciyarta,abinda ya sake batawa momma rai,taja tsaki tana miqa hannu gami da yunqurin karbar yaron "Miqomin shi nan,me kika iya?,yarinyar da ko pant dinta har yanzu batasan ta wanke ba" momma din ta fada tana jifanta da harara,zallar quruciya ya hana widad fahimtar kuma,bugu da qari kuma,akwai wata irin wankakkiyar zuciya da take da ita,ba kasafai ta fiya damuwa da abubuwan da suke faruwa cikin gidan ba,duk da ta soma girma,hankalinta ya fara fahimtar wasu abubuwan "Allah na fara koya momma" "Naji,jeki da Allah" ta fada tana sake harararta kamar idanunta zasu fado,sai dauke dubanta daga fuskar momma din tana nufar hanyar kitchen dinta. Wata tsawa ta kwatsa mata,wadda sai data sanyata ta kusa tuntube da kujerar dake gefanta "Ina kuma zaki?" Ta fada tana fidda idanu "Wajen Aafiya zani" "Kiyi mata me?" Ledar hannunta ta daga tana nuna mata "Kayan kwalliya na kawo mata ta zaba" "Uhnnnn,salon kije kisa ta bata aikin dana sakata,to zauna nan har sai ta fito,kada ki shiga ku hadu ayimin shirme" narkewa tayi tana duban momma din,da alama tanason ta roqeta ne ta barta ta shiga,tana kuma tsoron tsawarta,don ba abinda ta tsana sama da tsawa da kuma fada. "Ki barta mana momma,idan yaso tana shiga saita fito kada ta zauna" dina ke fada qasa qasa,saboda tausayi da widad ta bata,waiwayowa momma tayi ta kalleta tana dan juya aysar a hannu kamar zata masa rawa "Wannan yarinyar?,tsab zasu iya barnatar min da guri,kuma baka da damar yi maya fada balle duka,tunda tana da uwa a bakin murhu" "Kiyi haquri momma,yanzu zata fito" "Naji,amma indai ta shiga din duk barnar da tayimin ke zaki biya" "Na yarda" sai.anty dina din ta daga kai ta dubeta "Shiga kikai mata kizo na aikeki sassan anty madina" "Tohm" ta amsa da zumudinta tana shigewa,deena ta bita da kallo,bata fiya yin fushi ba don mutum ya bata mata ko ya tsangwameta,bata sani ba ko tsabar quruciya ce?,ko sai nan gaba zata fahimta komai idan hankali ya gameta?. *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 *_A RUBUCE TAKE!!!_* (k'addara ta) Page 03 *MAAB LUXURY HOME* *_idan kaji gangami akwai labari_* *_SABUWAR DUNIYA CE_* *ALFAHARIN UWAR GIDA* *FARINCIKIN AMARYA* *MAIDA TSOHON GIDA SABO* *DUNIYAR QYALE QYALE* *KAYA NA ALFAHARI DA TAQAMA* *_Ba iya kyawun idanu suka tsaya ba,harma da ingancinsu da kuma qwarkonsu,ka dade kana mora kana kece tsara a tsakanin tsararraku da sauran mutane_* *nasan zaku tambaya ina ne nan?* *MAAB LUXURY HOME* 😊 *Kai daga jin sunan ma babu tambaya* *_duniyar qawata muku gidajenku ku ganku kamar a wata nahiya ko wata duniyar_* *Suna kawo kayan kitchen rankatakaf manya da qananu* *Kayan gado dana parlor* *Kai...suna kawo kowanne nau'in kayan ado na cikin gida* *Karkiyi qasa a gwiwa kuma kada kiyi sake ma dafe,maza garzaya ki nemesu a* _adress dinsu dake No 22 Ahmadu bello way,kano state_ *Ko kuma kuyi order din kayanku kuna daga gida ta shafinsu na instagram* @maabluxuryhome *Facebook* @maabluxuryhome *Ko ku nemesu ta lambar wayarsu kamar haka* 08034631010 *Kyau inganci da rahusa shine takenmu*😊😊🤝🤝🤝🤝 ____________________________ Koda ta shigan bata zauna ba kamar yadda anty deena tace tayi sauri,ta sameta tana yankawa momma albasa,sai zabga gumi taje gami da hawaye,duk da cewa kitchen din kitchen ne irin na zamani,da ya wadatu da iska da manyan windows,dukka a qoqarin momman na koya mata girki,kada ta tashi kamar widad,wadda bata cas bare as a gidan,abinda ya damu wasu cikin gidan,yake kuma basu haushi sosai,suna gajun gatan da ummu ke nunawa widad din yayi yawan da ya kamata ta rageshi ta sanwa wasu cikin jikokinta. Budewa Aafiya kayan tayi tana cewa "Zabi duk abinda kikeso a ciki" kanta ta leqa cikin ledar tana cewa "Ummm,yar gatan ummu,inda nice nace mata ta siyon kayan nan qi zatayi,sai tace naje na tambayi yayuna maza" "Yaaya mahfood ne nima ya kawomin" daga kai tayi ta kalli widad,dududu itama Aafiyan ba zata wuce sa'ar widad din ba,saidai ta danfi widad din
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155