Chapter 134
Chapter 134
da nake namiji ai gashi ina gani" ya fada yana nuna dakin baqin da ya hada qura sosai,sai kawai ta saki kukan takaici,kawun ya qara da cewa "Duk qoqarin da abbas yakeyi babu wanda bai san dashi ba,don bai taba kawo qararki ba tsahon zamanku tare sai yau,kuma bazai taba tiwuwa ace shekarun duka da kuka kwashe ke dashi baki taba yi masa laifi ba,saidai kece d baki gani" "Nima kawu ai yana yimin" "Rufen baki,me ya hanaki ki fada" ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,yayi mata fada sosai ya kuma tursasata ta bashi haquri. Kamar wadda aka cusawa tsumma a baki kanta a qasa haka ta furta kayi haquri,gaba daya ma abun sai ya jishi banbarakwai,don zaiyi mugun mugun wahala kaji kalmar ban haquri daga bakinta,daga qarshe dukansu kawun ya hadasu yayi musu nasiha sannan ya wuce gida,abbas ya fita ya rakashi har bakin mota sannan yayi masa alkhairi,duk da cewa da qyar ya karba. Daya dawo tana ta kumbure kumburenta sai ya watsar yayi kaman bai gani ba,ya tattara ya fita sallah,bai kuma dawo ba sai bayan isha'i,don ya tsaya ya saurari karatun da ake a masallacin duk bayan sallan isha'i zuwa qarfe tara na dare. Silk sleeping dress ce a jikinta baby pink mai gajeran hannun net,duka tsahonta iya qaurinta yake,ta lullube kanta da wata qaramar hular net mahadin kayan,ta cusa duka gashinta aciki,idan kayi mata kallon farko saika dauka batasan ko zo na kasheka da hausa ba,dakin babu wadatar haske sosai,sai na screen din wayarta dake hannunta. Gaba daya bata jin dadin chart din da takeyi,zuciyarta duka babu dadi,wani irin kewarsa ce take taba zuciyarta a hankali,tun dazu daya shigo yace zai fita bata kuma ganinsa ba,kuma dazun taji shigowar motarsa,taji mimi tana masa oyoyo,amma bai shigo ya sake ganinta ba?,wani abune da bata saba dashi ba,duka sai taji qirjinta da zuciyarta sun quntata,wayar ma ta fita a kanta,ta maidata gefa ta ajjiye tana zamewa ta kwanta,idanunta suna hada ruwan hawaye. A gajiye yake jinsa,don haka ya nufi sashen widad yayi mata sai da safe,ya murda qofar ya jita a kulle "Sarkin tsoro" ya fadi yana sakin murmushi,ya saka nasa key din ya bude ya shiga. Falon nata neat kamar ba'a zauna ba,qamshinsan nan yana nan,amma akwai qarancin haske,da alama ta gama shirin kwanciya. Lumshe idonta tayi sanda taji sallamarsa,sai taji wani abu da ya tokare mata a qirji yana sauka,ta bude idonta tana amsa masa sallamar,dai dai sanda ya shigo dakin,ya saka hannu ya kunna fitilar haske ya gauraye ko ina. A kanta idanunsa suka fara sauka,suna hada ido sai taji zuciyarta ta karye,ta sake narkewa tana jin idanunta suna tsatstsafo da hawaye "Bakiyi bacci ba?" Ya tambayeta yana takowa inda take,maimakon ta amsa masa saita cusa kanta cikin pillow tana sakin kuka,yaji a jikinsa kukan take,saboda haka ya tako da sauri ya iso inda take "Wuud(qauna/soyayya,sunan da ya kuma fara kiranta dashi kenan)" sake cusa kanta a pillow din tayi,sai ya haura gadon gaba daya,ya birkitota jikinsa yana leqen fuskarta "Me ya faru?,kuka?" Gaba daya ta saki kukanta,ta kuma qanqameshi tana saka kanta a qirjinsa,cikin narkakkiyar muryar kukan tace "Ba kaine ba?" "Nine?,nayi me?" Ya fada tana fidda idanunsa "Tunda ka fita baka sake shigowa ba kayi tafiyarka,kuma daka dawo ka shiga wajen mommyn mimi ni kuma sai yanzu ka shigo,bayan ma a can zaka kwana" "Kishi?!" Ya fada a zuciyarsa yana zaro idanunsa waje,wani lafiyayyen murmushi kwance saman fuskarsa,maganarta dai dai take da albishir a gareshi na rainon da yakewa zuciyarta ya fara kaiwa ga gaci,albishir ne a gareshi na zai fara tarbar sabuwar rayuwar daya raina,sabuwar zuciya da jaririyar soyayyar data fara ginuwa. Rungumeta yayi gaba daya a jikinsa,cikin taushi da laushin harshe ya fara gaya mata wasu kalamai da suka sata jin kunya,tun tana ya bari yana qi har kunya ta sakata ta shige jikinsa gaba daya,sai daya tabbatar ta nutsu sannan ya sakata ta kwanta,ya rufeta da duvet da kyau,ya saita mata sanyin ac dana fanka guri daya,ya kuma rufe mata dukka windows dinta dama sashen gaba daya. Tana jinsa yana fita kamar tace masa ya dawo,to amma ta samu dakiyar zuciya tunda ya gaya mata goben a nan zai kwana,ta rufe idonta tana sake bawa kanta qwarin gwiwa,duk da zuciyar dai babu dadi. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 88 *W A S H E G A R I* Ture plate din da ya gama cin chips din yayi gefe guda bawai don ya qoshi ba,a'ah sai don babu wanu taste a tattare da dankalin,salam dashi,yakai dubansa ga yaransa daketa cin abinsu hankali kwance,saboda rashin sabo da kuma rashin sanin dadin bakinsu. Kallonta yayi itama tana ta cin abinta kamar yaran,tun kayan daren jiya ne a jikinta,duk da tayi wanka a hakan,ya danyi gyaran murya "Yau din ba sai kinyi shirin komai ba,zan kwana wajen qanwarki,jibi sai na dawo wajenki,idan mun koma jibin shikenan,idan bamu koma ba sai a dora da haka" maganar taxo mata a mugun ba zata,ta daga kanta da sauri tanason ganin da gaske abbas ne ke mata zancan rabon kwana tsakaninta da widad din,tsabar mamaki da tsorata sai kuwa ta qware,dankalin ya shaqe mata wuya,tahau tari babu qaqqautawa,take idanunta duka suka firfito,ya tsiyaya ruwa da sauri ya miqa mata yana mata sannu. Ko data gama shan ruwan numfashinta ya dai daita sai taji kamar ta kurma ihu,abbas din yayi wani mugun baqi a idonta,duk qoqari da jarumtar da tayi a jiya bai gani ba?,shine da safiyar Allah zai zo da wani zancan na daban,banda rainin wayo da rainin hankali,su gama satittikansu a can,sannan a nan ma a cinye mata weekend dinta?. Bala'i ke cinta sosai tana kuma son ta saukeshi akan abbas din,amma kuma batason tayi wani abu da anty ummee zata ce ta bata plan din gaba daya,duk da haka ta kasa haqura,ta kafeshi da ido sosai tana kallonsa "Abban mimi.....ni kake cewa zaka yiwa rabon kwana da widad diyar cikina?" Cikin second uku kacal ya gama qare mata kallo,a nutse ya jingina jikinsa da kujerar da yake kai sannan ya gyada mata kai yana lumshe ido hadi da budesu,sai ta janye nata idanun,ranta yana qoqoluwar baci,daya daga cikin yanayin da zaka gane hankalinsa a kwance yake,kuma ransa bai baci ba kenan idan yayi maganarsa,kuma sign dake nuna tabbatacciyar magana ce da babu canzawa,sai kawai ta miqe da sauri ta nufi daki,batason hawayen da suka taso mata su zubo a gabansa yaga rauninta. Tana kuka tana kiran anty ummee,wadda tuni ta saba da ganin kiranta,kiranta babu alkhairi kamar yadda kiran nata ba samuwa bace damuwa ce,haka siddan idan bata da matsala ba zata taba nemanta ba,tana dagawar kuwa taji sautin kukanta "Anty ummee ni yau abbas ke gayawa wai kwanan widad ne?" "Abbas din?" Anty ummeen ta fada abun yana girgiza ta itama "Eh,shifa" shuru tayi mamaki na ratsata,wanne irin kafaffen namiji ne abbas din,duk hanyar da aka bullo masa sai ta warware?,tsahon minti biyar suna kan wayar hafsat na mata kuka,taja dogon numfashi tana cewa "Kinga,kiyi shuru da bakinki,inaso kiyi kamar baki damu ba,kada ma ki bari ya gane kinyi kuka,amma yau bai isa ya kwana a dakin yarinyar nan a gaban idonki ba,ke har su koma wallahi,ki kwantar da hankalinki,indai kinbi abinda zan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155