Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 141

Chapter 141

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,310 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

maqale kafada "Alright" ya amsa mata yana miqawa hafsat nawwara da nufin ta riqeta "Ajjiyeta mana" ta fadi cikin zafin zuciya, ganin yadda ita yakewa maganar,amma duka hankalinsa na kan widad din,baice komai ba ya juya da nawwara a kafadarsa ya daukar mata luggage din yana biye da ita a baya har zuwa sassanta. Da idanu ta rakasu,wai me yake faruwa ne?, yaranta ma farinciki suke da zuwan yarinyar ne?,ga wani abu me girma data lura yana gilmawa cikin idanuwansu shi da ita. Ko kafin ya dawo tuni ta tsufa cikin falonsa,tunani yayi mata katutu,koda ya shigo falon ta daga kai ta dubeshi sai taji gaba daya ta raina kanta,ga laulayi daya sanyata ta kwantsame ta fita hayyacinta,gefe guda rashin gyaran da bata daukeshi a bakin komai ba shima ya taka rawa wajen lalacewar tata. Kusan yinin ranar cikin qunci ta yishi,tana aikace aikacen da ba kasafai ta fiya yinsu ba sai abbas din yazo tana fama da qunci,itakam widad koda ta isa sashenta zagewa tayi ta gyarash fes,yaran na biye da ita har ta gama,ta kama yaran bisa radin kanta tayi musu wanka,tana jin dadin yadda yaran ke qaunarta,a nan falonta ta barsu bayan ta dora aninci mai sauqi,ta shiga itama ta sake wanka. A gaban madubi ta tsaya daure da towel tana kallon kanta,ko ina na jikinta ya fara cika,abinda yaketa bata mamaki kenan,hasken data qara ya ninka nata nada,tasan bata canza mai ko sabulun wanka ba bare tace ko sune suka saka,don kanta ta gaji da kallon kan nata,bata kuma gano dalilin wannan canjin ba saita tabe baki kawai taja manta ta fara shafawa. Hafsat din na gyaran sashen shi kuma yana gyaran closet dinsa,duk da yasan zaiyi wahala gobe widad din bata gyara ta ba,amma kuma yana tausayinta,yana ganin kamar aikin yana mata yawa,don sanitation irin wanda yakeso take a sassan nasa bayan hafsat ta gama jiqa jiqarta. Baisan ma ta gama ta fice ba sai daya gama wanka yana neman wasu qananun kaya nashi,ya tuna suna cikin akwatin widad din,dole ya dora jallabiyya saman towel din dake daure a qugunsa ya wuce sassan nata don ya ciro kayan. A falo ya tambayi su mimi antynsu,sukace tana ciki,ya wucesu bayan ya sake canza musu channel zuwa mbc 3. Sanda ya buda qofar dakin nata ta zame towel dinta tana saka brassiere,tsaf ya qare mata kallo ta cikin mudubin yana jin numfashinsa yana sauyawa,don komai ya fito masa muraran,komai na widad din sake daukan hankalinsa yakeyi kowacce rana,sai yaji ya kwadaitu da son jin duminta cikin jikinsa,don haka ya taka a hankali har ya isa gareta,yayi caraf ya riqe towel din sannan ya fincikota a tausashe zuwa jikinsa. Tare suka sauke ajiyar zuciya shi da ita,ya zaci zata nema qwacewa ko zame jikinta,sai yaji tayi luf cikin qirjinsa,qamshin sabulun wankansa yana mata dadi sosai har zuciyarta,wannan ya bashi damar aiwatar da abinda zuciyarsa ke kwadaita masa hankali kwance,har sai da taji yana niyyar zarmewa sannan ta zare jikinta tana tuna masa su mimi dake parlor. Da jirkitattun idanunsa da suka sauya launi yake dubanta tare da tayata daura towel dinta da ya zame,daurin gaba yayi mata,ya cukuikuye towel din a tsakiyar qirjinta yana duban wajen,sai tasa hannunta guda daya ta rufe,daya hannun kuma ta jawo hijab dinta dake gefe ta soma yunqurin sakawa,ya saki siririyar dariya yana cewa "Please mana,minti kadan fa zan dan kalla saiki rufe". Ya soma kicin kicin qwacewa ita kuma tana nade kanta a ciki tana dariya,da wannan har ta sake komawa jikinsa. Ganin aikin take kamar zai kasheta,ga laulayi gaba daya jikinta babu cikakken qwari,don haka ta tsame hannunta daga yankan salad da takeyi ta nufo sassan widad din. Tun a hanya take kwatanta da yadda zata fuskanceta do kada ma taga sassauci a fuskarta ta nema kawo mata wargi. Bin ko ina na falon ta dinga yi da kallo,ko ina fes kamar yadda abbas yakeso,ya koya mata kenan,tsinanniyar tsaftar nan tasa,taja mugun tsaki tana tambayar su mimi widad din "Tana daki,yanzu abba ya shiga kiranta" wata mummunar faduwa gabanta yayi,abbas kuma?,me yakeyi a dakin?,bayan yau din kwananta ne?,ta gama masa wahala daga kaucewarta har ya baro sassan?,cikin mamaki zafin zuciya da kuma kishi ta doshi dakin,batayi wata wata ba ta murza handle din ta tura da qarfi ta shiga,shigar da batayi mata dadi ba sam,shigar da sai da taji kamar kanta zai tarwatse,abbas dinta widad din kwance a jikinsa suna qyalqyala dariya,duk sun yiwa shimfidar gadonta squeezing. Tare suka daga kai suka dubeta,saita kasa jurar ganinsu ta soma girgiza kai,ga widad kuwa mo gezau batayi ba,tadai ci gaba da janye hijab dinta daga hannunsa tana cewa "Laaa,mummyn mimi wallahi bamuji sallamarki ba,uncle ne,yana nan yana......." Ido ta runtse da sauri taja baya,ta kuma buga qofar da kyau,gudu gudu sauri sauri ta fice daga sassan kuka yana kubce mata. "Yana nan yana me uncle din?" Abbas ya fadi yana jefa mata hararar tsokana,can qasan ransa a bace na yadda ta kutso mata har bedroom dinta ba tare da sallama ko neman izini ba, dariya ta qyalqyale dashi,duk.da qasan ranta taji haushi,ta riga ta saba da dabi'ar yin sallama kafin ta shiga waje,amma ita hafsat din qatuwa da ita batasan tayi ba? "Ba komai" ta amsa masa tana dariya,saiya tsaya kawai yana kallonta yanajin wani farinciki yana wanzuwa cikin rayuwarsa,tsahon seconds sannan ya miqe yayi kissing goshinta,ya qarasa akwatin ya dauki kayansa yana tsokanarta ya fito. Yana dosar dakinsa ya jiyo sautin kukanta,ya girgiza kai kawai yanajin takaicin hafsat din,yana saka kansa cikin dakin ta daga kai tana dubansa,idanunta sharkaf da hawaye,tasan halinsa sarai,miskili ne na qin qarawa yaso,ganin yayi.kamar.bai ganta ba ya nufi dressing mirror dinsa saita buda baki a zafafe "Na gode,na gode sosai da cin fuskar daka yimin,yau kacal amma harka fara satar kwana na kana kai mata?" Kamar bazai.amsata ba har ya gama fesa turarensa bayan ya fidda jallabiyyar jikinsa,sai a sannan taga towel kawai yake daure dashi, zuciyarta ta sake fusata qwarai,ya juyo ya dubeta "Ina kwanan yake?,ina cewa rana ce yanzu?,da kika shiga kuma wani abun kikaga munayi?" Tambayoyin nasa sai taji gaba daya na rainin wayo ne "Kayi laifi amma kana yin kamar bakayi komai.ba abban mimi?" Ta fadi tana nuna qirjinta da yatsanta,zare towel din ya qarasa yi yana sanya kayansa,sai da ya gama tsaf har sannan tana zaune tana dubansa,ya dawo gabanta ya tsugunna yana kallon qwayar idonta,ya sauke idanunsa zuwa ga hannuwanta da farcenta ya dan soma taruwa,ga 'yan qananun datti nan sun fara shiga qasan farcen,sun nuna kansu ne saboda yadda hannun da farcen suka kode dalilin rashin digon lalle ko kadan a jikinsu,abinda yafi tsana kenan ya gani,shi yasa sanda yake bauchi da kansa yake daukarta ya kaita gidan qunshu ya ajiyeta ya kuma bar mata kudi masu dan yawa akan ayi mata,amma da wahala idan ya kaita sau goma ayi sau uku saita kawo uzuri tace layi yayi yawa bata samu ba,wani lokaci ma kafin yazo daukarta ta hayo motar haya ta dawo gida,yasan kuma tabbas kudinta kawai take karbewa daga wajen mai qunshin,a yanzun yanason kama hannun nata amma yanajin wani iri,tun daga ranar da widad ta fuskanci me son lalle ne bata sake zama hannunta haka ba,hasalima bata rabo da sargen da take sawa yatsunta idan bata samu

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});