Chapter 61
Chapter 61
tuni yanzu suna falon ummu suna kallo da hirarrakinsu,da tuni yanzu ba cikin pillow take kwance ba,da tuni kanta yana kan cinyar ummu tana sosa mata kai,a hankali ya rage tsahonsa ya tsugunna a gabanta,saiya sarqafe hannayensa guri guda yana kallonta,ta takura sosai a kwanciyar da tayi,amma baisan ta yaya zai gyara ta ba,yana jin tashin sautin kukanta,amma baisan ta yaya zai fara lallashinta ba,idan nawwara ce ko mimi chocolate zai hadasu da ita,to amma ita din aita dara a rarrasheta da chocolate. Duk yadda ya kamo zaren lallashinta ya kasa daidaitashi da tunaninta,bayason qarya sam a rayuwarsa,kuma ba maqaryaci bane duk rintsi,amma a yanzun da aka hadashi da rainon yarinya dole sai ya hada da canza maganganunsa "Tashi muje" ya fada a hankali,abu na farko da yazo kanta shine gida zai kaita,don haka ta daga kanta da wani mugun hanzari,ta sauke manyan fararen idanunta da suka sauya launi saboda kuka tana dubansa "Gida zaka kaini wajen ummu?" Sai ya gyada mata kai,yana kallon yadda farar fuskarta tayi pink sosai saboda kuka,kafin ya gama tunanin sa tuni ta diro daga kan kujerar,ta nufi hanyar daki tana kiran sunan latifa ta dauko musu kayansu "Wait....zo mana kiji" ya kirata yana miqewa da sauri,saita tsaya cak,sannan ta saka hannunta tana maida gashinta baya,saboda ya rufe mata idanu bata ganinsa da kyau "Hijab kawai zaki dauko,kayan sai daga baya kinga suna da yawa,itama ki barta a nan zata biyomu" "To" kawai tace masa,saita qara wuta zuwa daki harda hadawa da sassarfa. Tafin hannunsa yasa ya dafe goshinsa,ya Allah.....a sanda kake buqatar ka huta......wannan wanne sabon raino ne ya sameshi?. Tunda latifa ta ganta afujajan ta kuma gaya mata me yace sai tayi murmushi kawai ta miqa mata hijab din tana cewa "Allah ya kiyaye hanya,saina taho" ta zura hijab din tayi gaba abinta. "Na shirya" ta fada a shagwabe tana karya wuya sanda ta dawo falon,kallon fuskarta sosai yayi,hijab din ya qara mata kwarjini,sai ya juya a hankali ba tare da yace mata komai ba ya soma ficewa,tuni tayi tsalle ta dafa masa baya,don kafin ya fice ma harta tarar dashi,jinta a gefansa ya sanyashi waiwayawa,dai dai sanda itama ta daga kai ta kalleshi,sai suka hada idanu,wani abu mai nauyi taji ya saukar mata,sai tadan dakata har sai daya gota mata da kusan taku uku sannan tabi bayansa. Da kansa ya bude mata seat din gaba ta shiga,sannan ya zagaya ya shiga shima ya tada motar,ta sauke ajiyar zuciya wadda ke hade da sheshsheqar kukan da tasha,sai taji hankalinta ya kwanta sanda suka hau kwalta,zata koma wajen ummunta. A hankali yake tuqin,ya rage speed na motar sosai,sai widad tayi relaxing sosai jikin kujera tana kallon yadda suke wuce titunan garin bauchi a hankali,kamar zata masa maganar cewa baya sauri,amma sai taga sannu sannu dai tunda sun fito zasu isa wajen ummun. Cikin nutsuwa da salo na janye hankali ya dinga bi tituna tituna da ita,tun tana zuba idanu taga sun dauki hanya dodar harta haqura taci gaba da bin unguwannin da suketa wucewa da kallo,wani waje ya burgeta,wani gurin taga kamar kano,wani gurin kuma taga kano tafi wajen kyau. Agogon hannunsa ya kalla,dai dai sanda ya nuna masa sha biyu saura na dare,saiya juya kan motar yayi reverse,ya koma asalin titin da zai maidasu gida. Tun tana zaune saman kujera tana chart su mimi na wasa a saman carfet,har bacci ya daukesu,sai a sannan ta lura da yadda lokaci yaja,to a ina ya tsaya?,ta tambayi kanta bayan ta gama kwantar da yaran,qirjinta ya buga sanda zuciyarta ta raya mata yana can da yarinyar yana neman hadin kanta qila kamar yadda ta samesu ran nan,tunanin da ya sanyata fara neman spare key din gefen nasa,wanda ta jima rabon da tayi amfani dashi,jikinta har rawa yake,bata ankara da rigar jikinta ta bambanta da zanin jikinta ba ta zaqulo muqullin ta fito da wani irin sauri. Cike da qwarin gwiwa ta sanya key din ta buda sashen nasa,wayam ba kowa a falon,wata zuciyar ta gaya mata suna can kan gadonsa yana cin amanarta,saita qara hanzari ta cusa kai bedroom din nasa,nan ma babu kowa,ta tsaya jim tana tad'i ita da zuciyarta,sai taji ranta yana raya mata qila yana sassanta acan suka yada zango,ta sake juyowa a birkice tana fita a sassan nasa. Tunga taja ta tsaya ganin alamun qofar falon na kulle ta ciki,wannan ya sake tunzurata,zarginta kuma ya fara hauhawa,ta fara bugun qofar da qarfi. Da hanzari latifa ta taso,wadda tuni bacci ya dauketa,gabanta ya dinga faduwa din irin qarfin bugun da akewa qofar "Allah yasa lafiya,Allah yasa ba wani abu bane ya faru" ta dinga fadi cikin zuciyarta sanda take kan hanyar zuwa ta bude qofar. Kallon kallo suka yiwa juna na sakanni kafin latifa ta tuna wace,saita sake fuska "Barka da dare" ta fada tana duban fuskar hafsat,bata amsa ba illa cewa da tayi "Tana ciki ne?" Kai ta girgiza "Sun fita,tun dazu kuwa,nima su nake tsimaye" saura kadan tayi subutar bakin sako ashar,Allah ya taimaketa ta danneta can qasan ranta,wani abu mai zafi da quna ya soma mata suya a qirji,wata mace abbas ya saka a gaban mota suka fita?,me yake nufi?,zai daidaita matsayinsa da yarinyar da ita take mata kallon bata da maraba da babu?,don cin fuska tana can tana zaman jiransa,bai gaya mata ma cewa ya fita din ba saidai taji a bakin wata?,saita juya ba tare da tace mata komai ba ta fara barin wajen,latifan ta bita da kallo ranta cike da tambayoyi,daga bisani ta maida qofar ta sakayata,ta koma falon ta zauna saman kujera tana hamma tare da duba lokaci,bataso ta koma bacci suzo kuma suyita bugu. Dab da zata isa sashenta qarar bude qofa da kuma hasken motarsa ya risketa,saita tsaya cak tana motar,kafin ta fara takawa zuwa wajen,tanason taga idanun abbas,da wanne baki zai mata bayani kuma?. Yana kashe motar tana isowa saboda saurin data kwaso,ya sauke Glass din motar a hankali yana dubanta kafin yace "Bakiyi bacci ba?,inata so na kiraki kuma saina sha'afa" hakan daya fada ba abinda yayi mata illa sake tunzurata,ya manta ma kenan da ita?,takai dubanta ga widad wadda jikinta ya gama yin la'asar,ta kwantar da kanta a seat din motar,bacci gaba daya ya cika mata idanunta,duk da haka ta hadiye "Qanwarki keta rigima nadan fita da ita" sosai tayi namijin qoqarin danne wani mulmulallen abun daya taso ya tsaya mata a wuya,bataso sam ya tabata da niyyar dagata ko taimaka mata ta fito,don haka tayi saurin zagayawa side din ta bude mata qofar tana cewa "Ayyah.....haba widad?,banda abinki da haka kowa yake sabawa, kowacce mace a matsayin baquwa take zuwa gidan aure,amma yau da gobe sai kiga ta saba" ta qarashe maganar tana bude murfin,tana jin kamar ta fincikota,amma hakanan ta tsaya harta fito din "Ka wuce ka huta,bari na rakata" ta fada tana kallonsa. Wani narkakken kallo yake binta dashi,gaba daya ta gama bashi mamaki ta kuma kwance masa kai,hafsat dinsa ta sauya fiye da yadda rai da zuciyarsa suke raya masa zata iya sassauta kishinta,kodon tana duba qananun shekarunta ne?,yana nan a tsaye har sukayi nisa,tana riqe da hannunta tana lallashinta da bata maganganu,saiya maida murfin motar ya rufe,ya sanya key din a aljihunsa ya soma takawa zuwa sashen sa yana jin gajiya nabin dukka gabbansa,babu abinda yafi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155