Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 59

Chapter 59

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,315 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

a bayanta, yanayin qirar jikinta kadai abar kallo ce,sai kace wata babbar budurwa,tun a yanzun coca-cola shape dinta ya fita sosai,kallo dayan data mata ya kusa tafiya da numfashin ta,ta dinga qoqarin riqe kanta da kyau,kada ballinta ya watse a wajen. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 38 "Don Allah ki dauramin,na kasa wallahi" tayi maganar tana miqawa latifa dankwalin ba tare data lura da hafsa dake zaune a gefe ba,tana jin kamar ta mutu,abbas ya gama cutarta,yaje ya auro yarinyar data kusa haifa?, sannan kumata fita komai da komai na siffa?,duk da tana qoqarin qaryata kanta da kanta,tana qoqarin gayawa kanta idonta ne yake ganin hakan "Kawo,Allah ya gyara min ke,bansan sanda zaki koyi daura kallabi ba" dariya tadan saki "Ni nauyi Allah,banda anty deena ta takura" "Ga antynki nan baku gaisa ba" latifa ta fada bayan ta karba dankwalin tana lanqwasashi. A sakarce ta waiwaya ta dubi hafsa din da irin kallon da takewa kowa,ba tare da ta bawa matsayinta muhimmanci ko matsar dashi gaba daga matsayin da take bawa kowa data fara saninsa ba "Ina kwana?" Ta furta cikin girmamawa kamar yadda ta saba gaida dukkan wanda ya girmeta "Lafiya lau qanwata,ya kwanan baqunta?" Hafsat ta fadi da wani murmushi da takejin kamar na sossoka qayoyi ne cikin bakinta. Murmushi ta danyi tana maida dubanta ga latifa,saboda batasan amsar da zata bayar ba,don batasan amsar da ake bayarwa din ba,ta dan ranqwafa kadan latifa ta soma daura mata dankwalin. Cas ya zauna a kanta,ta daga kai latifan tana kallonta "Ehen.....yauwa,yanzu kikai dauri" latifa ta fada cikin tsokana. Idanunta hafsa takai kai,cikin sakanni taji ba zata iya ci gaba da zama tana kallon yarinyar ba,wani irin mugun kyau da kwarjini daurin yayi mata,saita miqe cak tana cewa "Bari na koma,yau jiki yayi nauyi ban samu dafa muku komai ba,kuyi haquri" murmushi inna laila tayi "Lah,babu komai fa,yaran ma suna gab da kammala dafa abun karyawan,ai ansha hidima wallahi,mun gode,Allah dai ya qara hade kanku,ya kade fitina,gata nan sai ayita haquri da ita,har yanzu akwai quruciya sosai a tare da ita,sai ana yi mata nuni,ana kuma gyara mata inda tayi kuskure,ayi haquri da ita don Allah" ta fada zuciyarta na danson naqaltar mata fuskar hafsatun "Aiba komai wallahi" ta fada a taqaice,can wani sashe na zuciyarta yana jin kamar ya zundumawa inna laila ashar,babu zancan quruciya uzuri ko daga qafa ga duk wadda ta aurar mata miji,koda kuwa widad din qyanqyasar yau ce,tunda har ta iya sanin meye so?,ta banbance tana sonshi,ta kuma iya sanin meye aure ai magana ta qare,babu daga qafa babu ragi babu kuma rangwame,haka ta dinga jefa qafarta zuwa sassanta idanunta basa gani sosai,fatanta Allah yasa abbas ya wuce sashensa,ya kamata ta rage kukan dake damunta a qirji. Cikin awannin da suka biyo baya suka sake shiga qalqale sassan nata da kyau,duk sauran abubuwan da ba'a gama kintsawa ba suka kammalasu,sun gama kuwa da wuri,saboda wadanda ke presidential lodge din da aka kaisu motoci sun kwasosu sun dawo dasu gidan,nan da nan sashen ya dan qara cika,anata hira da barkwanci,kusan kowa gidan widad djn ya tafi dashi,saboda babu ce kawai babu. Duk da wannan jikinta ya mata wani mugun sanyi,babu wannan hayaniya ko kazar kazar din,tana lafe a waje daya kusa da inna laila,itace ta zame mata kamar ummun nata,mugun kewar ummun take,gaba daya zuciya da jikinta babu dadi,duk da yadda suketa qoqarin janta da hira da kuma wasanni. Qarfe sha biyu har sun fidda jakankunansu harabar gidan,sun kuma fito waje,zuwa sannan idanun widad fararen nan sun fara kadawa suna tara ruwan hawaye,hakanan ta riqe hannun inna laila gam. Sanda suka fara shiga motocinsu dai dai lokacin ya iso,shi ya fara qarasowa wajen sannan hafsat wadda keta yashe baki tana sake binsu da murmushin yaqe. Cikin nutsuwar nan tasa yake tsaye gaban motocin,yana sanye da wani soft yard na maza gray color da yayi matuqar kwantawa a lafiyayyar fatarsa,jikinsa na fidda soft scent mai kwantar da hankali. Tsaf kowa ya shige,saura inna laila da latifa,a sannan tuni ruwan hawaye ya gama wanke mata fuska tsaf,zame hannunta da inna laila ta soma yunqurin yi ya sanyata fashewa da kuka sosai "Don Allah inna zan koma,karku tafi ku barni" ta fada tana sanya hannunta saman fuskarta,saita karya zuciyar kowa,inna lailan ta dubeta "Ga latifa nan widad,zaku zauna tare kafin wani lokaci,kiyi haquri" daga haka sai ta matsa gaba,ta kuma shige motar da sauri,gaba tayi zata matsa hafsat ta rigata,ta kuma riqota,a zuciyarta tana jin kamar ta rufe widad din da duka sannan ta hadasu su wuce kanon tare,amma sai ta shanye ta kuma hadiye wannan,cikin sigar lallashi tace mata "Haba mana widad,kiyi haquri,ai saiki karya musu zuciya,ba gani ba?,ga yayanki ma,sannan ga latifa an bar miki,kome kikeso ki gaya mana kinji,babu mai takura miki, kiyi shuru mana haba,yanzu inda su nawwara na nan ai sai su tsaya kallonki antynsu tana kuka" ta fada tana rungumota jikinta,ta rintse idanu tana jin kamar ta kara wuta ne a jikin nata. K'asa k'asa take kukan har zuwa sanda motocin suka gama ficewa a gidan,shikenan sun tafi sun barta.....shikenan sun rabata da ummun ta...... shikenan bata da kowa.....haka zuciyarta ta dinga gaya mata. Hafsat dince ta matsa gaba da ita wajen latifa tana miqa mata ita "Ki kaita ciki ta zauna ki lallasheta" sai latifa ta gyada kai tana kama hannunta tare da jawota jikinta suka fara barin wajen tana yiwa widad din magana qasa qasa,saidai da alama ba zata iya jurewa ba,saboda qarfi da kukan nata ya fara yi. Da kallo hafsat ta bisu har suka shige,tsinuwa da zagi kaka kala cikin zuciyarta akan widad din,sai data tabbatar sun shige din sannan ta matsa gaba inda abbas ke tsaye suna magana da rabi'u yaron gidan dake musu 'yan aike aike da aikace aikace na filin gidan. Hannunsa zube a aljihun wandonsa har ta qaraso Inda yake tsayen,musayar murmushi sukayi,wanda murmushin dake kan fuskar hafsat din tasa ma'anar ta dabance "Sannu da qoqari madam" ya fadi har cikin ransa,don duk abinda je faruwa kan idanunsa ne yana gani,sai ta saki qaramin murmushi tana jin yadda zuciyarta keta mata ciwo "Yauwa sannu,amma kaima ya kamata ka shiga ka bata baki fa,kuka taketa yi,abun tausayi" ta fada tana canza yanayin fuskarta zuwa kalar tausayin. Da ido ya kalla sashen sannan ya maido kanta "Tunda kin rarrasheta aikin wakilceni" wani sanyi yadan sauka a ranta,ta juya idonta kadan "A'ah,ai matsayinka daban,inaga kaje din da kanka sai yafi" baice komai ba,sai ya kalla agogon hannunsa kawai sannan yace "Zan dan fita,inajin zan iya kaiwa magariba kafin na dawo,rabi'u zai kawo cefene komai da komai,ki duba abinda babu saiki gaya masa ya hado dashi" fuskar ta a wadace da fara'a,duk da sanda take ita daya ba haka takeyi ba,duk sanda yace za'a kawo cefene

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});