Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 113

Chapter 113

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,303 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yafi komai bata mata rai a yanzun,don bata dauki widad din a wata matsala da zata kasa saitata ba,wannan kuma sai yazo ya hadu da rashin shigowar widad din ya qara tunzurata. Widad din nayin sallama ta watsa mata wani irin kallo mai hade da harara "Sai yanzu kikaga damar zuwa?" Ido widad din ta dauke yana qarasowa cikin falon "Gefen uncle na fara gyarawa tukunna" miqewa zumbur tayi,har batasan ashar ta subuce mata ba "Kina nufin dakinsa kika shiga kika gyara?,waye ya baki wannan izinin?" Kallonta take danyi da mamaki,sai kuma ta janye idanunta,saboda bata saba kallon babba haka kai tsaye idan yana mata fada ba "Shi yace nazo na gyara" maganar ta sake tunzurata,ba bata lokaci ta nufi qofa ranta na suya,wannan wanne irin zubda mata da mutunci yayi shirin yi?,me ya hanashi kiranta ita tazo ta gyara masan,kawai sai ya kama ya kira yarinya taga makwancinsu?. Har takai qofa kuma ta dakata,saboda tunawa da tayi ita din me laifi ce,sai tayi qwafa ta dawo ta zauna,koma meye akan widad din yau zata saukeshi "Me kika tsaya kina kalla da baki wuce kin kama aikinki ba?,ki fara da kitchen idan kin gama ki wanke bandakina,akwai kayan nawwara data bata a toilet dina,saura kiyimin ha'inci" idonta ta bude a hankali daga rufesun datayi tun sanda tayi mata tsawar farko,bata ce mata komai ba ta doshi kitchen,tana jin wani abu me kama da bacin ran da bata taba ji ba yana son fara tana zuciyarta,me tayi mata da zata dinga binta da irin wannan tsawar?. Tana ta cika tana batsewa ita daya a falon tayi baquwa,baquwar kaman customer a wajenta,tana siyan pieces na laces da hafsat din ke kawowa daga Lagos tana siyarwa,dadewarsu tare ya haifar da qawance a tsakaninsu,ta jima batazo gidan hafsat din ba,saboda dama ba kowa bane yakejin dadin ziyartar gidanta ba,saidai idan cikinka a cike yake da abinci,hakanan baka da qishirwa. Already ta gaya mata idan ta shigo bauchin zata qaraso taga wasu lace,tasan kudi zata samu a jikinta,wannan yasa ta karbeta da fara'arta,ta kuma ajjiye duk wani bacin rai dake damunta. Suna tsaka da gaisawa talatu ta dawo dasu mimi ta koma "Ma sha Allah,mimi ta fara girma" baquwar me suna hajiya habiba ta fada "Wallahi,aikin kwana biyu baki shigo ba,saidai aike" "Bari kawai,abubuwa ne suka cushemin" daidai lokacin da mimi ta matso kusa da hafsat din tana gaya mata zatayi toilet "Sarakan saka mutane aiki,baiwar taku ai ta dawo" sai ta sanya baki ta qwala kiran sunan widad din har sau uku. A lokacin tayi nisa cikin tunanin dabi'un hafsat din,me yake damunta da take tara wanke wanke haka ba zata iya kintsawa ba?,ko ina na gidanta bashi da dadin shaqar qamshi har sai sanda tazo?,muguntar zatayi mata ne?,ko haka dabi'arta take?,itadai tunda ta taso a rayuwarta bata tana ganin kalar qazanta irin wannan ba. Yadda take kiran sunan nata ya fargar da ita,ta ajjiye plate din hannunta da sauri,garin saurin wuqar dake ajiye a wajen tadan yanketa a dan yatsa,ta runtse ido tana jin zafin yankan yana ratsata,ta yarfe hannun tana bude idon nata sanda muryar hafsat ta sake iskarta cikin wani amo na gigitar kira. Dukkansu su biyun suka zuba mata idanu,hafsat din ta jifanta da wata muguwar harara,yayin da hajiya habiba ke mamakin ganin widad a gidan,tunda bata santa ba "Me kikeyi kina jina ina kiranki?" Ta fada cikin nuna isa taqama da gadara,tanaso ta yarfata sosai gaban hajiya habiba "Banji ba sai daga baya" "Kin fara canza hali ko?,indai kuwa hakane zakisha mamakina,zaki kuma sha wahala ne kawai,ki dauki mimi ki dorata a poo tayi toilet,kafin sannan ki kawowa baquwa ruwa" batace mata komai ba sai kama hannun mimin da tayi,tuni dama yarinyar ta iso wajenta tana mata sannu da zuwa,ita kanta yarinyar cikin walwala take,saboda me basu kulawar da mahaifiyar data haifesu ma bata iya basu ta dawo,surutan mimi ya rage bacin ran da a yau taji tana jinsa har cikin zuciyarta. Sai data dorata a poo din sannan ta shirya ruwan da lemo a tray ta dora cup a kai ta fito Parlor din. Sai da widad ta bace hajiya habiba ta dauke kallonta daga kanta sukaci gaba da cinikinsu,amma kuma maganar dake ranta tana ta cinta,har ta kasa Shuru "Wai nace ba.....me aiki kikayi ne?" Ta jefawa hafsa tambayar,dai dai sanda widad ke fitowa dauke da tray din. Duban widad din hafsat tayi,bata kuma tashi bada amsar ba sai data iso tsakiyarsu tana ajjiye tray din "Tayi kama dame aiki ko?" Ta fada a wulaqance tana tabe baki,amsar hajiya habiba shine ko daya babu kama da 'yar aiki a tare da ita,amma data fuskanci akwai magana a bakin hafsat din sai bata amsa mata ba,har zuwa sanda tace "Wai nan haka kishiyace aka yimin" "Kishiya?!" Ta amsa da amo mai qarfi tana sake bin widad data juya zuwa kitchen da kallo "Wallahi hajiya" "Kan ubancan....ah banga laifinki ba,amma ke kuma kina meye har aka miki kishiya?" Wannan shine iya abinda widad din ta iya ji. Ko data koma dakin hafsat din,tsaye tayi a gaban mudubi kalmar 'yar aiki tana dukan ranta,meye tayi da tayi kama da 'yar aiki?,tasan meye 'yar aiki,amma har yanzu bata fuskanci ainihin ma'anar kishiya ba,a cikinsu wanne yafi zafi?,ta samu kanta da tambayar kanta da kanta,kunnuwanta na iya jiye mata yadda hajiya habiba ta maimaita kalmar kishiya da wani irin nauyi da girma,me yasa kalmar kawai tayi girma haka?. Kallon hafsat hajiya habiba taci gaba dayi tana sauraren bayanin da take mata,da irin qoqarin da tayi take bautar da widad din "Kinyi qoqari qwarai,amma kuma ina jiye miki ranar da maigidan zai fuskanci bautar da ita kikeyi,ina mai tabbatar miki yana son kayarsa,saidai wala'alla yana ganin tayi qanqanta ne kawai shi yasa.mautara bata fito fili a kanta ba,ke.....baya ga haka ma mijinki me kamewa ne,idan wani ne ko jaririya ce yadda take da wannan mugun kyau wallahi tuni aikin gama ya gama,waima kina kallon fuskar yarinyar nan da kyau kuwa?"tayi tambayar tana kama haba,idanunta akan fuskar hafsat data bawa hajiya habiba dukka hankalinta "Girma ya fara zuwa mata fa,duk da dai ban santa a sanda aka kawota ba,kuma ke kin sani,ko makaho idan ya shafa ki ya shafata yasan ta fiku kyua nesa ba kusa ba,ta fiki diri,ke koni bazan yarda mijina ya dinga kallon wannan surar ba wallahi tallahi....." "Yanzu me kikeso kice?" Hafsat ta katseta daga yadda take kuranta kyan widad,saboda a yanzun a duniya babu abinda ta tsana irin taji an fada ko an yabi kyanta,ko tunawa ta fita kyau bataso tayi tsakanin ita da zuciyarta bare har a furta mata "Yauwa,idan kana da kyau ka qara da wanka,kudi zaki saka ki shiga malamai su sake kauda idonsa da zuciyarsa daga kanta,sannan a sake kama miki ita sai abinda kika ce" shuru hafsat tayi tana nazari,nan fa daya,an kuma zo wajen,ita indai zancan ta fidda kudi ne to babu ita a wajen,sannan ma kuma me take da buqata wai,komai da anty ummee ke tsara mata yana tafiya yadda ya kamata,ko canzawar da widad din ta fara yi hakan baya rasa nasaba da raga matan da takeyi kwana biyu qila shi yasa ta fara sakewa,kuma ko yadda anty umnee ke gudanar da gidanta ya isheta ishara,babu boka ba malam,amma ko meye

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});