Chapter 33
Chapter 33
sosai,kasancewar yana saya daga cikin jama'ar da suke nuna mata qauna da kulawa "Akwai wani abokina,sunanshi abbas,yacemin yana son yarinya mai hankali da nutsuwa zai aura,nasan widad dina nada hankali da nutsuwa,ina kuma alfahari da ita,wannan yasa nace masa yazo ya ganki kema ki ganshi" gabanta ne yadan fadi,saita dan rage fara'a kadan,uncle muhsin din ya karanci haka,don haka yayi murmushi "Kada ki damu,indai kika ganshi baiyi miki ba shikenan,babu wanda zai takura miki kinji ko?" Kai ta gyada "To uncle" "Yauwa,Allah yayi albarka widad" "Ameen uncle" ta amsa masa tana miqewa,jikinta yayi wani irin mutuwa,kamar zata daki sai kuma ta fasa tabi bayan nujood data tsaya a kitchen. Wanke wanke ta samu tana shirin yi,saita tsaya gefenta nujood din ta waiwayo "Menene?,na dauka zan ganki kina tsalle zaki gida,ko abban cewa yayi an fasa tafiyar?" Kanta ta girgiza "Wai wani abokinsa ne zaizo gobe ya ganni yanason yayi aure" murmushi nujood tayi "Ke wanne irin farinjini ne dake,amma abokin abba?,na sassan abokansa,wa yace miki?" Idanunta tadan juya alamar tunani na wasu sakanni sannan da sauri tace "Wai abbas" "What?" Nujood ta fada tana ajjiye plate din hannunta "Wai uncle abbas abba yake nufi?" "Oho,inajin shi dinne ko?" Ruqunqume widad nujood tayi,tana dan ihun murna "Wayyo widad,don Allah kada kice baki sonshi, uncle abbas yayi mugun haduwa,saima idan yasa uniform din nan nasa,ga miskilanci ga tsafta ga gayu,idan yazo gidan nan har ya tafi qamshin turarensa yana nan,don Allah kice kin yarda" ture nujood widad tayi tana tura baki "Dalla malama,ni ba wani nan,na barmiki ke ki cewa uncle kina so" dariya sosai nujood ta qyalqyale da shi tana cewa "Ni ai babana ne,banda haka ni abba zai bawa,tunda kika ga bai bashi ba kuwa babana ne din" ita dai widad bata sake cewa komai ba,sai ta hau saman kantan kitchen din ta zauna,tana sauraren nujood nata bata labarin uncle abbas din. Musaddiq ne ya shigo yayi kiran widad bayan kaman awa daya,yace tazo hajjaa nason magana da ita,ta sauko.tabi bayansa. A bedroom dinta ta sameta tana daga wasu kaya "Shigo mana widad" hajjaa ta fada ganin widad din ta dan rab'e,qarasa shigowar tayi,hajjan ta dan tsokanarta kan kayan tafiya kano take hada mata,don ta samu ta sake sosai tayi maganar da ta sanya aka kirata din dominta,ganin ta sake din sai tace da ita "Kinji abinda abbanku ya fada ko?" Kai ta gyada mata ba tare da ta amsa mata ba "Karki damu,abbas nada matuqar kirki,sannan shi din dan hajiya ne,hajiya dai wadda kuka zauna gidanta wancan satin" maganar data fada na cewa dan hajiyan ne ya sanyata sakin jikinta sosai,cikin dabara hajjaa keta janta da zance har ta saki jikinta,sai a sannan ta sallameta. Da yamma lis ta kama widad din duk rashin son kitso irin nata ta sake wanke mata kai,tana ta qi tana turjewa,sai data sanya su musaddiq suka dinga yi mata dariya ,tare da waqar me kukan kitso sannan ta nutsu,ta raba kanta tayi mata manyan kalaba da suka jelarsu masu tsaho zubo gefe da gefan fuskarta,saura kuma suka sauka a bayanta,kasancewar ba kasafai ta fiya kitso ba saboda qin da take masa,sai kalbar ta haska fuskarta tayi mata kyau sosai,hajjaa ta qawata qarshen kowacce jela da duwatsun kitso masu yawa da suka qarawa kalbar kyau suka taimaka kuma ta kwanta mata sosai a fuskar da bayanta. Itakam widad gaba daya murnar tafiya gida ya sanya ma bata damu ko ya dauki batun zuwan abbas da muhimmanci ba,siyayyar da uncle muhsin yayi mata taketa shiryawa abinta,tana ta zancensu Aafiya da sauran 'yan uwanta,da wannan batun ta kwanta bacci. ************Washegari a gida yayi breakfast wajen hajiya,ya kuma shaida mata yau din suraj zai rakashi gidan muhsin din. Har cikin zuciya da ruhinta take jin farinciki,tayi addu'a sosai tare da fatan samun dacewa da albarka mai yawa cikin lamarin. Sai Azhar ya wuce gida bayan yayi salla a nan,yana komawa bacci ya kwanta,bai farka ba sai gab da la'asar,tun bai tashi daga kan gadonsa ba ya janyo waya yana sake lalubar number hafsa,saidai yau din ma har tayi ringing ta gama bata dauka ba,a qa'ida idan yayima mutun kira daya baya qarawa,amma wannan karon ita din sai daya kira sau uku bata dauka ba,sai ya maida wayar ya ajjiye ransa yana baci,ya miqe ya shiga toilet ya daura alwala ya wuce masallaci. Yana dawowa dakin kira na shigowa wayar tasa,suraj ne yana dagawa ya soma zolayarsa "Sabon ango,Allah dai yasa ka shirya" ido ya lumshe yadan saki murmushi,surja badai zolaya ba "Haba duk zumudin na meye?,bayan la'asar fa mukayi dakai,kuma yanzun nan ma aka gama sallar" dariya suraj din yayi "Na qagu ne naga wacce mai sa'ar ce zata sake samunka,bama ni kadai ba,kaga zainab a nan ita kanta so take naje na dawo na gaya mata wacece" "Ita da hafsat kuwa" "To sai me?,kayi qoqari ka shirya,gani nan fitowa,abinci kawai zanci" "Saika qaraso" ya fada yana katse wayar,dole ya fidda hular da ya sanya ya aje,ya shiga bandaki ya don yin wanka. Yana tsaye yana tsane ruwan da yayi lumm cikin gargasar jikinsa yana duban madubi,karo na barkatai ya sake kallon wayarsa yana tuna adadin wayar da ya yiwa hafsat din bata dauka ba,sai ya jinjina kai yana qiyasta yadda zai fita daga bauchi jibi da sassafe zuwa kaduna. Ya gama shirinsa tsaf yana gaban mudubi yana kallon kansa,hannunsa riqe da hularsa yana karyata,yana jin wani banbarakwai,wai yau shine a karo na biyu zashi zance,zancen ma wajen wadda baisan wacece ba,ya dora hularsa sannan ya dauki sassanyan turarensa dake fallasashi a duk inda ya shiga ya feshe jikinsa dashi. Kiran suraj da ya shigo ya shaida masa isowarshi,saiya kara wayar a kunne ya tallafeta da kafadarsa saboda takalman da yake sanyawa a qafarsa bayan ya zauna kan dressing chair yana fadin "Ka qaraso ciki mana" "A'ah,ina cikin mota fito kawai" bai musa masa ba,ya zame wayar ya qarasa sanya wasu rufaffun takalma masu kyau da asalin tsada da wasu sake fidda shigarsa,ya dauki wayar ya mayar aljihu ya dauki keys din gidan suma ya saka sannan ya fito. "Kai mutumina,kamar yau ne zan rakaka wajen maman mimi?" Harara ya watsa masa bayan ya rufo murfin motar sannan yace "Kunna mota mu wuce,so nake muyi mu dawo,ina da wani uzuri" "Yanzu kuwa yallabai" ya fadi yana dariya,sai ya tada motar suka wuce. Suraj nata jansa da hira amma shi hankalinsa ya rabu kashi kashi,dubansa yayi sanda yaga yana qoqarin parking qofar wani qaramin mall "Bari mudan samo abinda za'a kai mata,ai bama shiga hannu rabbana ba" "Share kawai suraj mu tafi please" "A'ah,nikam ba za'ayi haka dani ba,ko banza fa ta zama matarka,tunda an riga an tambaya an kuma baka" maganar sai yaji tayi masa nauyi,bace komai ba har suraj din ya fice,bai kuma dade ba ya dawo da tarin alawoyi da chocolates masu tsada da dadi,ya ajjiye ledar ya kunna motar sukaci gaba da tafiya. ~~~~~ "Kai,tubarkalla ma sha Allah,diyata din nan badai kyau ba" hajjaa ta fada bayan ta gama shirya widad,cikin wata sabuwar dark blue din super vilisco,dinkin doguwar riga,ta fidda jelar kalbarta tayi ta fito ta qasan daurin dankwalin data yi mata,ya zauna das a kanta,sannan ta bata siririn mayafi da ya dace da atamfar. Murmushi widad kawai keyi tana kallon kanta a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155