Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 150

Chapter 150

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,305 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sai na daketa naga abinda zakayi" dab da zata qarasa ya isa gabanta yana nuna mata hanya,amma burinta ta qarasa ta bude qofar ta fiddo widad "Ka matsa ka bani waje azzalumi kawai" "Kibar wajen nan hafsa na gaya miki" "Saina shiga,saina shiga azzalumi" wani lafiyayyen marin ya sake sauke mata hagu da dama,gaba daya sai wuta ta dauke mata,taci burki tana kallonsa kamar wata zararriya riqe da kumatunta "Don kina iskanci da rashin mutuncinki kina ganin kamar bazan iya daukan mataki a kanki ba kin yaudari kanki,sassauci na da dauke kan da nake miki inason na zama mafi alkhairi ne ga iyalinsa,amma ke gaba daya tosashiyar kwanyarki ta kasa gano miki hakan,to wallahi wallahi kinyi na farko kinyi na qarshe,bazanci gaba da dauka ba,ki bacemin daga wajen nan tun ban bi ta kanki ba!!!" Ya fada da wata irin rugugin tsawa,ba hafsat dake tsaye a wajen ba,hatta da widad dake daga cikin falon saida cikinta ya juya, tsoron sosai ya kamata,ta koma ta zauna saman daya daga cikin kujerun dake dab da qofar,karin farko da taji sautin fushi da bacin rai daga gareshi kenan. "Ko meye zaka ce, kuma ko me zakayi bazan fasa fadin cutata da kakeyi da cin zarafina ba,yarinya qarama ta mallakeka sai yadda tayi dakai,sai abinda tace,kanata zalunta ta,bazna yafe ba wallahi,sai Allah ya sakamun,kai da ita dukanku bazan yafe muku ba" cikin fushi ya sake daga hannu sai kuma idanunsa suka sauka kan cikinta,ya janye hannun yana qoqarin hadiye fushinsa,bai taba dora hannu a kanta ba sai yau,sai ya kama hannunta ya saita mata hanya yana gaya mata cikin tsawa ta bace masa a wajen. Jinta take kamar ba'a tsaye take saman qafafunta ba kamar akan iska take haka ta juya ta fara barin wajen, hannunta har yanzu akan kuncinta,idanunta na malalar hawaye masu zafi da quna,yau ita abbas ya mara?,wannan shine mummunan abun tarihi na farko daya faru a iya zamansu da ba zata mance dashi ba. Ido ya zuba mata cikin fushi har ta bace a wajen,sannan ya juya ya bude qofar,wanda tuni widad dake zaune saman kujera ta miqe tana dakon isowarsa,saidai zuwa yayi ya wuceta abinsa yana wani irin huci,kaman zai zauna akan kujera amma sai ya kasa,ya dinga kai komo widad din tana kallonsa tana kuka qasa qasa "Shut up" ya fada mata da wata irin tsawa data sakata qanqame jiki waje daya hadi da runtse idanunta,bayason jin kukanta ne kwata kwata,tana qara hasala masa zuciyarsa ne ba tare data sani ba,a cikin yanayin da yake kuma a yanzun bazai iya lallashinta ba,sai kuma ya koma ya zauna bayan ya sakar mata tsawar,jikinsa yana mutuwa,qaramin sautin kukanta yana sake ratsa falon. Kusan minti talatin suna a haka,ta kasa shuru shi kuma ya kasa lallashinta,sai da suka doshi minti arba'in sannan ya miqe ya fice,ba jimawa ya dawo dauke da hijab dinta da wayarta ya miqa mata,sannan ya isa gaban freezer dinsa ya ciro ruwan gora mai sanyi ya bude ya miqa mata,tasa hannu ta karba tana satar kallonsa,idanunsa ba'a kanta yake ba,wani gurin daban yake kalla,sai takai ruwan bakinta ta fara sha,ya fara sauka cikin cikinta yana ratsa qirjinta dake suya,yana kuma rage mata radadin da takeji. Kusan rabi tasha sannan ta miqa masa,sai ya sake saka hannu ya karba ba tare daya kalleta ba,bakinsa yakai ya shanye sauran yana yin gaba,ya cillar da robar yana cewa "Wuce muje" bayansa tabi ba tare da tasan ina suka nufa ba,motar sa ya bude tun kafin su qarasa da remote control,ya isa seat din gefan driver ya bude mata ta shiga ya mayar ya rufe,sannan ya zagaya shima nasa bangaren ya shiga ya tayar da motar suka bar gidan. Lamo tayi cikin motar,ta kwantar da kanta a makarin kujerar tana 'yar sheshsheqar kuka,idonsa ya dinga runtsewa,sautin kukanta yana qonashi da yawa,basarwa ya dinga yi yana zaton zai iya daurewa amma sai ya kasa,tausayinta ya lullubeshi,yadan daki kan motar,sai ya gangara gefan hanya yayi parking ya juyo sosai ya zuba mata ido yana hadiye bacin ransa da qyar "Why widad.....why.......me yasa kika biye mata?" Idanunta dake jiqe da hawaye ta daga ta kalleshi "Amma uncle.....itace ta fara fa" kai ya jijjiga "Na sani,amma kina zaton zan tsaya ne a wajen ina kallo ta cutarmin dake?" Kai ta kada a hankali alamun a'ah "So kike ki koyi irin abinda takeyi?,kinaso na daina samun walwala gaba daya?" Kai ta girgiza nan ma sabuwar qwalla na sauko mata "Kayi haquri uncle......am sorry" a hankali ya lalubo hannunta da hannunsa guda daya ya hadesu waje daya yana hadiye wani bacin rai daya tsaya masa "Am sorry too baby,na miki tsawa,it was not intentionally.......hankalina ne a tashe,raina a bace,banason kema ki koma wani abu daban" "Bazan sake ba uncle" ta kuma fada hawaye na sake balle mata "Kina qonani baby doll,kina qona zuciyata,ki daina wannan kukan" ya fadi yana kamo fuskarta cikin hannunsa,tare da zaro handkerchief dinsa ya soma goge mata fuskar cikin wani irin salo na tausasawa da nuna zallar qauna,hausawa sukance gaida mai gaidaka ko bazai amsa ba,ko meye zai mata idan tana cikin bacin rai bai fadi ba,widad ce kadai ke fahimtar ransa a bace yake ko yana fushi,saita tabbatar tayi abinda zai samu sassauci kota saukeshi daga fushinsa,duk da kusan ba itace sila ba. Saida suka shiga unguwar ta fahimci gidan hajiya ya kawota,bashi da wani solution illa hakan,saboda yasan kwana zatayi kuka ita kadai,babu lallai ta saki jikinta,a nan ne kawai zata sake tayi baccinta. Mamaki ya kama hajiya lokacin data gansu tare,baice ma hajiyan komai ba ya barta a nan ya koma setting room din qofar gidansu suka shiga meeting din da suka shirya yi din. Itama batace komai da hajiyan ba,saidai hajiya ta fuskanci sanyi jiki kadan tattare da ita,tanata kallon widad din,canzawar da tayi tayi yawa,ta kasa cinyewa wannan karon bayan sun gama meeting din ya shigo gidan,widad din ta tafi kawo masa abincin da bai samu ci ba tace dashi "Anya abbas ba juna biyu yarinyar nan take dashi ba?" Ido yadan lumshe yana sakin qaramin murmushi,hasaso 'yar rigimar tashi da ciki kawai yakeyi,inda hakan zata kasance da yafi kowa farinciki,amma fa yasan daru ne za'a shashi "Banjin haka hajiya" "Bata amai bata yawu,ba zazzabin dare?" Dan jim yayi sannan ya girgiza kansa "Babu hajiya" "To ma sha Allah,Allah ya kawo nagari masu albarka" "Ameen ameen" ya fada cikin dan jin nauyi. Muneera ya nema yace ta gyara daki daya widad din zata kwanta a ciki,ba jimawa muneera ta gyara din,don dama ba dakin da hajiyan ke barinsa da dauda. Yana zaune ta wuce dakin,hajiya tace taje ta kwanta,taga kamar tana alamun bacci a idanunta,ta yima hajiya sai da safe,ta juyo zata masa sallama suka hada ido,sai ta basar tace "Sai da safe" "Allah ya bamu alkhairi" ya amsa ta yana binta da kallo,inda suna kaduna waye zai shiga tsakaninsu a irin wannan lokacin,kaf rayuwarsa yana qaunar dare yayi,saboda lokacine da zai rabi jikinta sosai ya kuma kwana yana jin duminta hadi da shaqar tattausan qamshinta. "Ba yanzu zaka wuce bane" hajiya ta tambayeshi ganin goma da rabi na neman gotawa,agogo ya kalla sannan yadan dubi hajiyan "Wannan program din nake jira su gama saina wuce" ya bata amsa yana maida dubansa ga tv din,saidai a zahiri gidan

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});