Chapter 36
Chapter 36
tafi,za'a biyaka koma nawa ne" "To shikenan alhaji" sai daya tabbatar ta shiga gida ita da kayanta sannan ya juyo ga mutumin "Me ya faru?" Gyara tsaiwarsa yayi yana sake riqe qugunsa "Tun daga tashar kawo na daukota alhaji ita kadai qwallin qwal da sunan shata tayi,mukayi ciniki ita akan dubu sha biyar,sai da mukazo nann sannann zata hadani da dubu goma,wai nayi haquri bata da kudi,kudinta basu kai ba" cikin matuqar bacin rai ya fara laluba aljihunsa "nawa ne cikon kudin naka?" "Dubu biyar ne ranka ya dade" mai motar ya fada cikin matuqar jin dadi ganin hakkinsa zai fiti,sai ya irga ya miqa masa,yasa hannu ya amshe yana godiya,ya juya yana komawa motarsa "Lamarin mata sai haquri,tun dazu muketa qoqarin raba rigimar mu bashi kudin amma taqi saurararmu,Allah dai ya kyauta" maqotan nashi suka fada,gaba daga kunya ta gama baibayeshi,kamar shi matarsa tana fada dame mota akan cikon dubu biyar,bayason tsaiwa bare suja wata doguwar magana,duk da sunyi qoqari kuma alkhairi sukayi masa,sai ya basu hannu sukayi musabaha yana musu godiya,ya juya ya shige cikin gidan,xuciyarsa da rayuwarsa na wani irin quntata,wannan wanne irin kwance zani ne a kasuwa tayi masa?,me ma takeyi a bauchi?,wa ya bata ikon tahowa?,da wadan nan tambayoyin ya saka kai cikin gidan,kai tsaye ya zarce sassanta. Yana sallama cikin falon su mimi suka taho da gudu suka rungume qafafunsa,ya duqa ya daukesu gaba dayansu yana musu oyoyo,ba tare da ya zauna ba yake qarewa falon kallo,bata a ciki,saidai kayansu da suka taho dasu watse a falon,yawan kayan ya tabbatar masa gaba daya kayansu ta debo daga can,ya jinjina kai ya sauke yaran yana kunna musu tv "Ku kalli cartoon ina zuwa" ya fadi yana shafa kansu,mimi dake da wayo ta gyada kai ya wuce ciki. Daya shiga tana toilet,don yaji motsin ruwa,sai ya harde hannayensa a qirji ya jingina da jikin madubinta yana qarewa dakin kallo,a hargitse dakin yake,babu kintsi kwata kwata,da alama tun sanda zasu tafi kadunan haka ta barshi. Tana motsa qofar ya mayar da dubansa kai,sai gata ta fito da alama alwala ta daura,ko sallar la'asar dinma bata samu yi ba kenan,suna hada idanu ta daure fuskarta da kyau,batason ta karaya ko yayi mata kwarjinin da zata kasa fadin maganganun dake cikinta,ta dauke kai kamar bata ganshi ba tana nufar inda abun sallarta yake a watse a qasa zata dauka "Yaushe kika nemi izinina da har kika baro kaduna kika taho bauchi?" Dagowa tayi,tanason dubansa kai tsaye amma tasan tayi qarya,a kaikaice take duban gefansa "Saina nema izininka?,tunda bani da amfani ai ya kamata na shaida hakan,na baka waje,mutumin da bashi da kimar da za'a bashi sabuwar mota kaga wacce daraja gareshi?" Idanunsa ya lumshe yana ambatar sunan Allah,wani abu ya tsaye masa a wuya,tabbas inda shi madokin mata ne yau din nan sai ya tsitsinkawa hafsa mari,banda tsabar hauka a yanayin da ake ciki na matsalar tsaro da aka fara fuskanta tana matar ASP zata debo yara har guda biyu su kamo hanya ita kadai?,sannan duka ba tare da wata hujja mai qarfi ba illa dai kawai yaqi canza mata mota?. "Kinsan abinda kikeyi kuwa?" Ya fada bayan ya bude idanunsa yana dubanta "Na sani mana" ta amsa shi kanta tsaye,sannan ta dora "Ai babu dole,yadda ban maka dole ba nima bazakamin ba,kowa yayi abinda ransa yakeso,Kaduna ne bazan zauna ba,ka nemo wadda zata zauna da kai cikin wadanda kake baiwa kyautar" sosai maganar ta dakeshi,wani bacin rai ya lullubeshi,ya bude bakinsa a zafafe mimi ta turo qofar riqe da.hannun nawwara,dole ya hadiye abinda ke taso masan,sannan yabar jikin madubin yana dosar qofa "Hakane,kiyi abinda ranki yakeso,nima zanyi abinda raina yakeso,zan baki mamaki tabbas wannan karon hafsa kamar yadda nasha fada,zan kuma nemo mai zama dani din" daga haka ya fice ba tare da yaja mata qofar ba. Da kallo ta bishi,haka kawai cikin jikinta taji jikinta yayi sanyi,yadda yayi maganar kamar he's serious,amma kuma data tuna ya saba fada dama sai ta tabe baki kawai,tasan ya fada ne kawai saboda yayi mata barazana,don haka ta karkade abun sallarta ta shimfida tana cewa "Mu bawa juna mamaki dai" ta sanya hijabinta ta tayar da sallar. Sanda ta idar yaran nata mata rigimar yunwa "Ba uban da zai sakani wani shiga kitchen na kwaso gajiya" saita laluba jakarta ta fito da biscuit da lemon roba guda daya ta miqa musu,maimakin ta tashi ta gyara koda dakin nata ne daya cika da shara da qura,sai ta koma saman gadonta ta miqe abinta,ta dauki wayarta ta fara chart. Hankalinta kwance take chart dinta,yaran nata basu qoshi bama babu wanda ta kula,ba jimawa kira ya shigo wayarta,data duba sai taga yayarta ce,ta gyara kwanciyarta tana saka wayar a kunnenta. Bayan sun gaisa take ce mata "Ana hada gudunmawar bikin nafisatu ne,nace bari nayi miki magana,don an kusa gama hadawa" take ranta ya baci fara'arta ta janye,bata qaunar abinda zai sanyata fidda kudi,itafa abu indai ba abbas bane zaiyi mata shi to ta gwammace ta haqura da yinsa koda ita zata amfana,a yanzun kuwa da suketa uwaka ubaka dashi ba zata ma dosheshi da wata buqata ba,da sai ta lallaba ta karba wajensa,ta zabge rabi ta basu rabi "Nifa gaskiya anty shamsiyya bani da kudi" takaici da haushi ya kamata,suna ganin yanzun mijin hafsatun ya fara danshi danshi amma ko daya yarinyar bata banbaruwa "Ke dama kullum cikin babu kike,to ba kyauta nace ki bani ba,contribution ne na biki,idan zaki bayar ki bayar,idan baki bayarwa ki fada ki daina batan lokaci" murya a cunkushe tace "Nawa ne kudin?" "Dubu goma goma ce ba wani kayan gabas ba,kuma ko atika da bata da wani qarfi tuni ta bada nata" "Shikenan zanyi shawara,zan kiraki idan sun samu" bata amsa mata ba ta kashe kiran,hafsa taja tsaki tana gyara kwanciyarta,gaba daya sunbi sun dameta ba gaira ba dalili. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 24 Kai kawo ya dinga yi cikin dakin,ransa na masa suya,me zaiyi ya huce takaicin hafsa?,yasan dai tabbas bazai qyaleta ba,anzo gabar da dole ya koya mata lesson kamar yadda yasha fada. Idanunsa suka sauka akan wayarsa,sai ya jawota da hanzari ya fara kiran layin hajiya,bugu biyu ta daga "Abbas ya akayi?" Ta tambayeshi da mamaki,ganin bai wani jima da barin gidan ba,qoqarin dai daita muryarsa yayi,don bayason ta fuskanci akwai wata matsala ne ta tashi hankalinta "Lafiya lau hajiya,cewa nayi zai yiwu a gabatar da neman auren cikin satin nan?" Kai ta jinjina cike da mamaki,anya babu walakin goro a miya? "Eh to,saidai na nema kawunnanka naji" "Idan zaiyuwu hajiya kawai ayi,na shirya" tana saurin gano damuwa da kuma fushinsa,yadda yayi maganar a jikinta taji akwai damuwa,amma zata tambayeshi a hankali "Shikenan,zanyi magana dasu,duk yadda ake ciki zaka ji" "To hajiya na gode,gobe da yamma zan wuce,zan shigo ta nan kafin na wuce din in sha Allah" "To ba damuwa,Allah yakai mana rai" daga haka sukayi sallama. Cikin mamaki take sauke wayar,saidai kuma ta samu kanta da sakin murmushi tare da fadin "Alhamdulillah" zuciyarta na gaya mata wataqila akwai alkhairi mai tarin yawa a abun,shi yasa Allah ya kawo komai a kurkusa haka ya sauqaqe matsala da damuwa. "Tofa,ta samu kenan hajiya?" Faccalarta da suke tare a falon,ita da yayar abbas din mai suna mabruka suna
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155