Chapter 69
Chapter 69
bishi da kallo har sai daya kusa shigewa motar,ta taka jiki a mace ta isa gaban motar ta buda daya side din ta shiga. Wani baqon qamshi ne ya ziyarci hancinsa,ya soma shirin tada motar yana zuqar qamshin,sai daya tada ita sannan ya waiwaya ya kalli hafsat "Yaushe kika sayi wannan turaren?" Kishi ya kamata,bataso tace ba ita bace ya farga da yarinyar,idan kuma tace itace tayi qarya,duk da haka ta gwammace wa qaryar,sai tadan murmusa "Eh,cikin bikin nan na siya" "Yayi dadi sosai" ya sake fada yana dan waiwaya sashen da take,duk da baiji yana busowa daga nan ba,murmushin yaqe ta saki tana basarwa,zuciyarta na bugawa,tana addu'ar komai ya tafi dai dai. Sun dauki hanyan babban super market din suke siyayya lokaci bayan lokaci,motar shuru,bakajin komai sai muryoyinsu widad mimi da nawwara,a hankali muryarta ke shiga kunnensa,itama ta saje dasu abinta,zuciyarsa cike fal da tunanin ita din fa wai matarsa ce,sai kawai ya gyada kai qaramin murmushi yana qwace masa,saboda shi kansa yasan akwai jagwal,baisan kuma ya zata kasance masa ba. Murmushin da yaja hankalin hafsa,ta dan juya kadan tana kallonsa,sai shima ya kalleta ya basar yaci gaba da tuqinsa,ita sam irin hirar nan ta debe kewa don kana driving ma bata iyata ba,sai suyi tafiyar awanni amma saidai kowa yaci kansa,imma ya kunna radio imma ya zubawa hanya idanu kwanyarsa ta cika da tunane tunane har su iso inda zasu. Su suka fara yin gaba zuwa cikin super market din,cewa widad tayi ta tsaya dasu mimi zata dauko mata duk abinda ya dace,bata wani damu ba ta jasu gefe suka zauna,haka tayita zagaye,tana hada duk abinda ranta ya mata a kwandon data dauka,ba wani abun azo a gani take zaba ba,don ba iya zaben tayi ba,majority tare suke shiga da abbas din,shike zabar mata abinda yaga ya dace da ita,takanyi mita a fili da zuci "Wannan asarar kudine kawai,ni da kudin ka bani da yafi" dubanta kawai yakeyi "Abinda zaki sakamin din ko kimin amfani dashi na kalla naji dadinne asarar kudi?" Takan basar kawai,itama batasan tana wannan subutar bakin ba a wani lokacin. Sai data gama zane zabenta sannan suka hadu a wajen biyan kudi,yaga abinda ta diba,takaici ya hanashi cewa komai,ya biya kudin kawai suka fito,baisan yaushe zata koyi siyan abubuwa masu amfani ba,sa'annan kamar ita zata biya kudin,ta saka tsaiwa ta dauki kayan daya dace. Kai tsaye gidan hajiya ya wuce dasu,tunda hafsat taga titin da yahau tasan can zasuje,sai ta bata rai,amma dai batace komai ba,don batasan bata wasan nata. Yana tsaiwa a qofar gidan widad tayi zaraf ita dasu mimi suka fice,yadan bisu da kallo kafin ya dawo da dubansa kanta,itama shi take kallo,ranta ya sake baci,sai take ganin kamar widad din yake kalla "Amma zaka jiramu mu gama ne saimu wuce gida ko?,don inason nadan kwanta,bana jin dadin jikina yau" dubanta yayi kawai,tunda suka fito din batace masa bata jin dadi ba saida sukazo nan,saiya soma zare seat belt dinsa,har ya bude murfin motar sai kuma yace da ita ba tare daya waiwayo ba "You know what?.....idan zakaso saniya ka sota har qahonta,domin kuwa no matter what ba yadda za'a yi su rabu,mahaifiyata itace duniyata,silar nasarar rayuwata" a birkice ta juyo tana kallonsa,bataso ya fahimci emotion dinta ba,ta buda baki zata jefa masa tambayar rainin wayon ya buda motar ya fice ya barta a ciki. Katsam hajiya taga shigowarsu,farinciki ya cikata,murmushi ya wadaci fuskarta,tana marabtarsu tana duban widad,tare dason gano wani canji tattare da ita. Ta sake haske dai ta kuma sake fresh,amma girman da taso taga tadan qara babu shi,alamu dake nuna babu komai kenan daya wanzu tsakaninsu. Tana tsaka da wannan tunanin yayi sallama da muryarsa mai zurfi ya shigo,idanunsa suka sauka a kanta sanda take zaune gaban hajiyan hankalinta kwance kamar tana gidansu,fuskarta ta wadata da murmushin da zai iya cewa tsahon satin biyun da tayi gidansa bai taba ganinsa ba,ba wani alamun surukuta a tare da ita,yo ina ta gama saninta ma. "Maraba lale,saiga baqin yamma" hajiya ta fada sanda yake duqawa gabanta daura da widad din yana gaida hajiyan,dai dai sanda hafsa ta sanyo kai cikin falon,sai idanunta suka qara kusancin dake tsakanin widad din da abbas,bugun zuciyarta ya dadu,wani abu ya kama wuyanta,tayi ta maza ta kauda kanta tana zuqar numfashin wahala,sannan ta qaraso falon tana sakin sallama da shaqaqqiyar muryarta. "Ah,kacemin tare kuka?" Ta fada har cikin ranta tana jin dadin ganinsu gaba daya "Eh munje sunyi siyayya ne,saboda gobe in sha Allah zamu wuce" "To yayi kyau,ma sha Allah" hakanan ta duqa itama ta gaidata don ganin idanun abbas din,ba komai a fuska ko zuciyar dattijuwar ta amsa tana tambayar ta yara,bayan lafiya lau data ce bata sake cewa komai ba,taja gefe daya ta zauna ta tsuke bakinta,amma idanunta yana kan komai dake wakana cikin falon. Yadda taga hajiyan ta maida hankalinta gasu widad din ya qona ran hafsat sosai,ta yita mutsu mutsu cikin kujera cikin bacin rai,tana jin kamar ta tashi ta fice tabar musu falon,sauqinta daya harda yaranta take ja da wasa,don su mimi suna kan cinyarta suna ta harkokinsu,amma ita wannan sam baiyi mata ba,daga qarshe ta buge ta amsa waya ta fice harabar gidan. Huci ta dinga yi tana fidda iska mai zafi daga bakinta,zuciyarta kamar zata fito,bata iya jurewa ire iren wadan nan abubuwan,akan abbas zuciyarta na gaya mata komai zata iya yi. Ana idar da sallar magariba suka baro gidan,a hanyar komawa ma tamkar kurame,shi ya riga ya saba da irin wannan zaman,uwa uba kuma dama shi din ba mutum bane mai son magana,yayin da hafsat din keta cin daci,gaba daya zuciyarta babu dadi. Qaramar leda ta dauka ta debi wasu abubuwa d'ai d'aiku ta bawa widad,bata damu ba don ba damuwarta din bane,tasa hannu biyu ta karba tana godiya,shi kuwa baisan me ya faru ba,an masa total dai ya biya kudi,yana tsammanin kowa ya dauki abinda ransa keso. ***********Kuka take sosai tsahon awa guda cur da sukayi suna tafiya bisa hanyar bauchi zuwa kaduna,duk yadda zai mata tayi shuru yayin amma kamar ma bata san yana magana ba,har ransa ya baci ya shareta taci gaba da kukanta. Tun sanda motar samuel ta daga da latifa kano,su kuma tasu ta dauki hanyar kaduna ta birkice da kuka,bata taba tsammanin latifan tafiyarta daban da tasu ba. Sai data kusa rufe awa biyu sannan kukan ya fara ja baya,jikinta ya fara saki,sanyin yammaci gajiya da kukan data sha suka saukar mata ds bacci,a hankali ta langabe kanta gefe tana sauke ajiyar zuciya mai nauyin,alamun taci kuka ta godewa Allah. Dubansa yakai gareta kadan kafin ya dauke kansa yaci gaba da tuqinsa,cikin ransa yana sauke ajiyar zuciya,wannan aure ne ko rigima sabuwa ta sameshi?,ya tambayi kansa. Karo na biyu ya sake maida dubansa gareta,sai ya rage speed na motarsa ya gangara gefan titi ya tsaidata,ya miqa hannunsa a hankali ya sauke mata kujerar yadda zata ji dadin kwanciyar,ya koma seat dinsa ya zauna dai dai,sannan ya sake kunna motar suka ci gaba da tafiya. Yammaci lis suka shiga garin kaduna,kofar wani babban gida ya tsaya,ya danna hon,babu jimawa mai gadin ya iso ya bude gate din,fuskarsa cike fal da murmushi,da alama farincikin ganin dawowar abbas dinne,aiko yana sako hancin motar zuwa parking lot na gidan ya biyo bayan motar da sassarfa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155