Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 76

Chapter 76

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,333 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 49 Awanni kusan hudu kenan tana abu guda,baya ga kitchen din data yiwa kaca kaca kota ina,kamar wadda ke girkin mutum ashirin,sannan daga bisani ta samu ta kammala tuwon shinkafa miyar kubewa iya yadda taga latifa tana yi,ta zuba cikin sabbin warmer masu kyau da aka hado cikin siyayyar cefanen da aka kawosu jiya. Dafe bayanta tayi bayan ta kammala gyare kitchen din "Shi tuwo dama haka yake da wahala?"ta fada tana yatsina fuska,duk da can qasan ranta farinciki ne fal,wai yau itace da yin girki cikin kitchen dinta,ba kwaba ba hantara babu bakiyi dai dai ba,ta juya ta soma diban warmers din takai saman dining,ta jeresu da kyau,tana kallonsu tana murmushi,har cikin ranta dadi take ji idan ta tuna wai yau ance tayi girki. Dakinta ta koma tayi wanka,ta shafa powder a kyakkyawan fuskarta mai santsi da sheqi dauke da tambari na quruciya,dubai abaya wine color da tasha adon duwatsu masu walwali ta fidda ta sanya,ta daura dankwalin saman kanta,ta kuma shafa turarukanta kamar yadda ya taba gwada mata yadda ake sanyasu,tun daga ranar kuwa ta dauke tsaf,yadda ya kwatanta matan haka take sakawa,ita kanta sai taji tafi jin dadinsu. Sosai abayan ta haska jar fatarta,kamanninta suka fito sak na ainihin tushen yankin data fito,ta koma gefan gadonta bayan ta dauko wayarta dake saman madubi,ta bude ta shiga wata game da taketa daukan hankalinta ta fara bugawa cikin qwarewa. Hankalinta yayi nisa sosai a game din,har bataji qarar motarsa zuwa shigowarsa cikin gidan ya kuma tura qofar dakinta ba,sai ya tsaya riqe da handle din qofar dakin,zai iya lissafa adadin shigowarsa dakin,idanunsa saman fuskarta,tattausan siraran labbanta sunata qyallin lips balm,tana ta juyi saman gadon,duk sanda taci game din sai tayi dan tsalle kadan na murna sannan taci gaba. Idanunsa ya dauke sannan yayi gyaran murya kadan ya hada da sallama,daga idonta tayi daga kan wayar zuwa kansa,saita aje wayar gefanta tana masa sannu da zuwa,sannan a dabarance tana laluba maballan gaban rigarta taji sun rufu da kyau?,ta kuma tsareshi sosai da ido taga ko.yana kallonta?. Sarai yaga abinda takeyi,amma sai ya kauda kai ba tare da yakai idanuwansa kan qirjin nata da yake ganin basu da maraba da qirgar dangi a wajensa ba "Tare da baqo nake,ki kawo abincin" kai ta gyada masa,ya saki handle din qofar ya juya zuwa falon,yana duba wayarsa daketa ringing. Ba kowa ke kiransa ba sai hafsat,tunda satin ya wuce taga baizo weekend ba hankalinta ya gaza kwanciya,gaba daya zuciyarta cike take da wasi wasi da kuma fargaba,duk kuwa da bayanin da yayi mata na cushewar aiki da ya samu a kaduna fiye da dukka garuruwan da yake zuwa aiki,amma zuciyarta ta kasa aminta da hakan,duk inda yake baya wuce satin nan dai baizo bauchi ba ko don hajiyarsa,sai wannan karon?,sai wannan lokacin daya tafi da wannan sadakar yallan?,anya ba holewarsa yakeyi ba?,anya bai samu wani abu bane daga gareta?. A kullum kwanan duniya kira uku zuwa hudu ne sai ta yiwa widad shi,ta tambayi ya suka kwana?,ya suka tashi?,ya suka yini?,ya dawo gida kuwa?,me ya faru a tsakaninsu?. Sam widad din bata boye mata komai,rashin wayo da qarancin shekaru yasa bata dsuki wannan din a mazaunin komai ba,face ma qauna soyayya da kulawar da mommy hafsa din ke nuna mata,wannan yasa ta sake ganin kimarta,ta kuma sake ganin girmanta,hakanan taji tana qaunarta,shi yasa dukkan abinda zata umarceta dashi take aiwatarwa kanta tsaye,wannan dalilin ne kuma yasa tayi riqo da hudubarta yadda ya kamata,don ya zame mata kamar tishi ne akan tarbiyyar ummu,sai faduwa tazo dai dai da zama,tana nisantarsa iyakar iyawarta,tana kuma qauracewa duk wani abu da tasan mommy hafsa ta gargadi akai. Ta sani ta kuma fuskanta,sam qarya bata cikin dabi'ar widad,da gaske haka take tun a gida,duk da samun wannan tabbacin,hakan bai sanya zuciyarta da ruhinta sun aminta sun kuma kubuta daga zargin abbas ba, don haka taketa kiransa,tanason taji yaushe zai zo din. Ajiyar zuciya ya sauke,yau inda ace buqata ce da hafsat din dole.ya ajjiye dukkan abinda yakeyi yaje ya sauke mata ita,to amma yafi kowa sanin wacece ita,tana iya share wata guda koma fiye bata buqaci komai daga gareshi ba,saidai shi din ya nema,a yanzun ma.ya tabbatar ba wani qwaqwaqwaran dalili ne da ita ba na kafewar ya taho din,ya bata dukkan wata dama da zata fadi uzurinta amma amsa daya ce "Kawai son ganinka nakeyi" "Kiyi haquri,indai ba babbar buqata ce dake ba......akwai aikin da nakeyi a nan din,banason kuma na matsa daga kaduna sai na kammalashi,aikin yana buqatar sirri kula da kuma takatsantsan" amsar daya bawa hafsan kenan,ta furzar da iska dgaa bakinta,zuciyarta na raya mata ta shirya ta tafi Kaduna kawai,to amma sanin girman laifin data aikata masa wanda yayi silar haramata mata Kaduna kwata kwata yasa ta sake jaddadawa kanta wannan ba mafita bace,zata bi ta hanyar da tasan dole yazo gida koda baiso ba. Sai data nema yalwataccen mayafi ta yane jikinta dashi sannan ta wuce falon,idanun abbas din a kanta,hakanan yaji abinda tayin ta burgeshi,bai gaya mata ta yafa din ba,amma tasan ya kamata,ta tsugunna har qasa ta gaida ameen abokinsa,sannan ta wuce ta soma dauko warmers din tana jera musu bayan ta shimfida table mat a qasan. Ta tsara komai yadda ya dace,har cikin ransa yaji abinda tayi ya burgeshi,ruwan sha dana wanke hannu duka akwai a wajen,abinda hafsat bata taba yi ba,dai dai da tissue daya dace ko yaushe a sameta saman dining sai ya nema,ita kuwa ta koyo hakanne daga wajen ummu,haka taga tana yiwa alhaji. Har ta juya zata wuce daki,sai taga ana hasko wani cartoon da take mugun so,fasa shiga dakin tayi,ta dawo ta zauna fuskarta cike da fara'a,kadan abbas ya waiwaya ya kalleta,kamar zaiyi magana saiya fasa,ganin irin excitement din dake kan fuskarta na ganin cartoon din,ya maida kansa ga warmer din,ya bude ya sanya hannunsa ya dauko malmalar tuwon farko. Tun baikai ga budeta ba ya fahimci an samu babbar matsala,duk da haka bai fasa ba,ya wareta yana sakinta saman plate,take kuwa tuwon ya dare biyu,suka hada ido da ameen din,sai abbas din ya basar,ya bude warmer din miyar,koriyar kubewa shar,wadda aka qarantawa kayan hadi ta bayyana,bama kayan hadi ba,harda kayan dahuwa,wake yayi tsuru tsuru yaja gefe,ga danyan manja a sama ya hade rai. Serving spoon yasa ya kwaso musu ita da qyar ya zuba akan plate din,ya maidata ya rufe ya saka musu cokula yana cewa da ameen "Bismillah" dukka dauriyarsa amee din ya gayyato,ya matso ya dauki cokalin,suka sanya lomar farko a tare da abbas din. Spoon din ya ajjiye sannan ya miqe yana duban abbas "Kasan nayi mantuwa a office,zan koma,daga can gida zan wuce" yadda ameen din keta rattaba bayani ya bawa abbas dariya,amma sai.ya qushe abarsa,gulma ce da ganin qarshen mutum tasa yace zaya biyoshi "Okay....sai na fito" ya amsa masa,sai ameen din ya juya yana cewa "Amarya,ni zan koma ko,ina godiya sosai,sauri nake.ban samu naci abincin ba,amma...... next time" "Ka gaida gida" ta furta a sanyaye sanda ta kalli abincin taga kamar babu abinda ya dandana,idanunta nakan plate din har ya fice a gidan. Dukkan alamu sun nuna.girkin nan nauyi dadi ko ma'ana ba

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});