Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 136

Chapter 136

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,310 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

cikin qarfin hali yana dubanta "Bari nayi alwala.na fito" "Na rakaka uncle?" Ido ya zaro "Bakyason alwalar tawa ta tsaya kenan?" Saita saki qaramar dariya tana kwantar da kanta a hannun kujera. Kafin ya dawo ta gama sallarta itama,haka kawai yau ta tsinciki kanta cikin zumudin kasancewa tare dashi,wani irin sabo kullum zuciyarta ke sake yi dashi,saita miqe ta hada masa ruwan wanka,ba'a dade da.idar da sallar isha'i ba ya sake shigowa. Zaman cin abincin yayi bayan ya gama wankan,ya shaqi daddadan qamshin da miyar ke bayarwa,take tsohuwar yunwarsa ta tash,sanda yakai abincin bakinsa kansa qarasa kuncewa yayi,kamar kullum qarawa hannunta zaqi akeyi "Ki zabi dukka tukuicin da kikeso na baki na dafa min abinda nafiso da kikayi" murmushi ta saki "Kace Allah yayimin albarka,haka ummu ke yimin idan nayi mata wani abun kirki" kai ya jinjina yana sake samun gamsuwa da yarinyar a ruhi da gangar jikinsa gaba daya,tun daga tarayyarsu zuwa yau ya tabbatar ta samu cikakkiyar tarbiyyar da irinta tayi qaranci ga yaran yanzu,shikam zai iya cewa ya tsincik diamond ne a cikin tarin duwatsu marasa daraja can can. Cikin lallausar muryarsa data karye ya fara mata addu'a,addu'ar data dinga amsawa tana murmushi,saboda da gaske tayi mata dadi sosai. Karar sautin wayarsa ya katse musu daddadan yanayin da suke ciki na wata irin hira me tafi da hankali da tunani,daya duba sai yaga hafsat ce,ya danyi mamaki kadan,duk da dazun daya shiga ya sameta tana sallah,sai kuma bai qara komawa ba,ya bari sai yazo rufe gidan,ransa bai kawo komai ba ya jawo wayar ya daga. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 89 Sallama yayi sannan yayi shuru na wasu seconds "Okay' taji yace,ya sauke wayar yana sakin ajiyar zuciya sannan ya kalli widad "Baby.....ina zuwa" kawai sai taji ranta yayi mata babu dadi,a sanyaye ta gyada kai,ya sunkuya a hankali yayi kissing goshinta sannan ya fice. Tashi tayi ta tattara kayan abincin da ya gama ci,ta gyara wajen sannan ta dawo saman kujera ta kwanta tana maida idanunta ga tv,saidai kuma fiye da rabin hankalinta yana kan abbas,ko yaya taji motsi sai ta daga kai taga ko shine. Tun tana kallon agogo da marmari har ta sare,tun tana danne zuciyarta har ta kasa ta fara sharar hawaye ganin sha daya ga sha biyu itama ta gota an tafi qarfe daya na dare,saita fashe da kuka tana curewa cikin kujera,tsoro haushi da takaici hadi da baqinciki suka mamayeta,me yasa uncle zaiyi mata haka?,daga cewa gashinan yanzu yanzu?. Hada kai da gwiwa tayi tsakanin cinyoyinta ta saki kuka sosai,zuciyarta na wani irin tafasa,ya tafi wajen mummyn mimi ya barta ita kadai?,bayan shi yayi mata alqawarin a nan zai kwana yau. Tun tana kukan da qarfinta har ta soma jin babu dadi,zuwa uku na dare kukan ya isheta ita kanta,a hankali kuma wani wahalallen bacci mai hade da bacin rai ya dauketa nan cikin kujerun falo. Cikin mamaki yake saka kanshi cikin falon,wayam babu kowa,sai tarkacen kwanukan da suka gama cin abinci da sauran datti wanda dama falon baya rabo dashi,haka ya dinga tsallake shirgi har yakai qofar dakinta. Yana murda handle tana sakin wani irin nishi,abinda ya sanyashi buda qofar da dan hanzari ya saka kai ciki. Male male ya sameta,kwance qasan tiles tana juyi daga wannan bangon zuwa wancan,tana ganinsa ta dago masa hannu,idanunta jagab da hawaye. "Subhanallah" ya fada yana qarasowa da sauri inda take kwancen,ya saka hannu yana dagota,gaba daya jikinta sharkaf yake da gumi,ya dorata saman cinyarsa yana tambayarta "What's going on?,me yake damunki?" "Cikina abban mimi......cikina zai fashe.....wayyo Allah" ta sake fada da qarfi tana wani irin murdewa. "Relax,ya isa" ya fada yana riqe hannunta dake saman cikin nata "Mutuwa zanyi,mutuwa zanyi,ciwo yakeyimin" ta sake fada tana riqeshi da kyau "Ba abinda zai sameki,ki nutsu,bari na fiddo mota sai mu wuce asibiti" gan ta riqe hannunsa cikin nata "Don Allah kada ka tashi,wallahi kana fita zan iya mutuwa" "Just a minute......yanzu zan dawo,saina kira widad ta kwana da yaran kafin mu dawo" kai ta jijjiga masa tana fashewa da kuka "Don Allah nidai kada ka tafi,ka mayar dani kan gado,sanyin wajen nan kamar zai fasamin qashi" duk yadda zai motsa ta hanashi,ko waya da yakeson kira taqi bari,haka ya miqe ya dauketa ya azata saman gadon,tana ajjiyeta ta kanainaiyeshi da hannuwanta tana ci gaba da matagugun ciwo. Da qyar ta bari ya saka hannu ya kade shimfidar gadon saboda datti datti da yake ji akai,ya jawo mata pillow dinta da pillow case din ta gaji da haduwa da dattin dauda,sai tasa hannu ta kare "Ka barni a jikinka please,ina samun relief" ta fada tana hawaye,hakanan ya zauna jingine da makarin gadon yana fatan ta samu sauqi,duka hankalinsa akan agogo yana mamakin yadda lokaci yaja haka,widad na ransa,ya dauki wayarsa ya fara kiran layinta. Har wayar ta qaraci ringing dinta ba'a dauka ba,ya sake kira nan ma ba'a daga ba,ya danji relief,saboda ranshi ya bashi cewa bacci ne ya dauketa. Jin shuru abun ya lafa sai yadan motsa da nufin sa mata pillow yaje ya duba yaran ya wuce sassansu,ji yayi tayi caraf ta riqeshi,cikin kuka kuka tace "Yanzu ba zaka iya zama dani ba daddyn mimi?" Tayi maganar tana sake riqeshi d kyau "Ya isa shikenan,yara zan duba,kuma.nabar qanwarki batasan me ake ciki ba" banza tayi taci gaba da sharba kukanta kamar ma bataji abinda yace ba. Duka duka baccin minti arba'in yayi aka qwala kiran sallar asuba,ya zame jikinta ya kwantar da hafsat dake baccinta sosai,har ya buda toilet dinta yaji bazai iya shiga ba,ya koma ya buda dakin yaran. Sai daya duba lafiyarsu sannan ya shiga nasu bandakin dake da sauqin qazanta yayi alwalar ya wuce masallaci idanunsa akan sassan widad. Tun kiran sallar farko ta tashi,ta farka tana sauke ajiyar zuciya na kukan data sha,ta kalli agogo saiga wasu hawayen,ranta ya motsu qwarai,kawai sai ta miqe ta wuce dakinta tana jin bacin rai yana cikata. Alwala ta daura,ta dawo cikin dakin ta jawo akwatinta guda daya ta fara sauke kayanta kaf tana lodawa a ciki,tana yi tana sharar qwalla,itakam yau ta gama kwanan bauchi. Akwati biyu ta shirya cike da kaya,ta jawosu falo sannan ta koma dakin tayi sallah,sai ta shiga wanka kawai,bayan ta fito ta shirya cikin atamfa dinkin riga da skert,ta zabi hijabin daya dace da atamfar jikinta ta dawo falon riqe dashi tayi zaune kusa da akwatunta tana share qwalla lokaci bayan lokaci,jiran shigowarsa kawai takeyi. A gurguje ya kammala azkar dinsa ya baro masallacin,gaba daya hankalinsa yana kan widad din,key dinsa yayi amfani dashi ya bude qofar falon,ya tura a hankali yana mamakin ganin qwan wutar falon a kunne "Subhanallah" ya fadi sanda yayi tuntube da akwatin widad,sai yaja baya yana kallon akwatunan guda biyu dake maqare da kaya,sannan ya maida dubansa ga widad din. Fuskarta a dinke tsaf,sai qananun qwalla da take sharewa,ta dauke kanta daga gareshi gaba daya,sam taqi yarda su hada ido,ya fahimci laifi ya tafka a jiyan,kuma da alama laifin babba ne a wajenta,ya zube hannayensa a aljihun rigar jikinsa yana qare mata kallo gami da sakin murmushi,wata qauna da soyayyarta mai kaifi tana hudashi,sai ya fara takawa a hankali zuwa gabanta. Yana isa ya tsugunna saman qafafunsa yana qoqarin leqa fuskarta,amma kuma ta hana hakan faruwa,mamakin

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});