Chapter 124
Chapter 124
yasan zancan gizo baya wuce na qoqi,bataso ya shiga yaga ba dai dai ba ya gyara mata ko yayi mata fada,ko shi din yasan idan ya shiga babu lallai ya samu sashen a yanayin da zai iya zama,so no need ya matsa sai ya shiga din,don haka ya juya da yaran suka wuce sashen nasa. Tun daga qofa yaga abinda aka saba,a yau dinma sashen nasa babu gyara,yadda ya barshi kusan wata guda haka yake a yanzun,sai ya basar,ya ajjiye yaran ya zauna shima saman kujerun falon,ta yiwa jakarsa mazauni sannan ta juya tana kallonsa "Bari na fara dora maka wani abun sai nazo na gyara nan din" manyan fararen idanunsa ya daga ya kalleta "No,a bani abinda kuka dafa kawai da rana". Da sauri tadan kalleshi,sannan cikin yanayi na rashin gaskiya tace "Ba zaka iya ci ba,infact ma inajin sun cinye....." "Eh daddy,indomie ce mommy ta dafa mana,kuma saida nawwara ma tace tana jin yunwa s......" Yarinyar bata qarasa ba saiji kake fafff ta doke mata baki,take kuwa bakinta ya fashe "Shegiyar maganar tsiya,muna magana uban waye ya sako bakinki a ciki?" cikin bacin rai abbas ya kama leban yarinyar yana dubawa,sai da ya gama ganin iya wajen da ya fashe din,ya goge mata wajen ya dorata kan cinyarsa yana lallashi sannan ya dubeta cikin bacin rai "A gabana zaki fasawa yarinyata baki?,kece me abun duka ba ita ba,amma waye ga dakeki?,na rantse da Allah kinyi na farko kinyi na qarshe,bance kada ki hukuntasu ba,amma ba ta irin wannan hanyar ba". Ranta ya baci sosai,ta dinga jefawa yarinyar harara,tanason bata mata budget gaba daya,amma tasan maganinsu,tattarasu zatayi kaf kwanakin wajen widad. Saboda tana da plan sai bata tanka masa ba,illa bata fuska sosai data yi,ta juya tana ficewa daga sassan ranta a bace. Kai tsaye ta nufi sassan widad,gwara ta fito da ita tun yanzun ta kama mata ayyukan,saboda yau aikin nata suna da yawa,ko gyaran sassansa zuwa abuncinsa aiki ne babba a wajenta,ga nata sashen da tasan zaici tsintsiya ruwa da klien,saidai tun kafin ta qarasa taga kaman babu mutum a sassan,kasa gasgata idanunta tayi,ta dinga ganin kamar gizo,har dai data taba qofar,takuma yi knocking taji shuru. Sak tayi,ta tsaya yana jinjina kanta,baizo da ita bane?,ko kuma ta wuce gidan hajiyarsa yadda ta tsiri wannan iskancin wani lokacin?,bata da amsa,don haka sai ta wuce sassanta,ta dauki wayarta ta kira muneera. Tambayar farko tace mata gatacan ita da hajiya a falo suna hira,ta zuqi iska ta fesar,lallai kan yarinyar ya fara wayewa,ita za'a mayar 'yar iska?,aqalla wata guda da wani abu kenan bata saka yarinyar a idonta ba,ko zuwanta na qarshe kwana guda kwata kwata tayi a gidan suka koma. Sake fitar da iska me zafi tayi daga bakinta,maganganun anty ummee suka dawo mata,ai kuwa ba zata bari hakan ta faru ba,tare ta karantawa yarinyar karatun manya,dole tabi da ita,dole tabi hanyarta,dole ne kuma ta fara gane banbancinta da ita,sai ta fara dora abinci sannan ta kwashi kayan shara ta wuce sashen nasa tana sake saqa abubuwa da yawa da take da shirin aiwatarwa. *_W A S H E G A R I_* Karfe goma na safiya ya fito tsaf dashi,cikin lallausan yadin filtex na maza mai asalin kyau da tsada,komai yana yinsa ne a wani kasalance da rashin kuzari,duk kuwa da cewa a jiyan ya samu yadda yakeso daga hafsat din,to amma sai yakejin wani irin mugun banbanci mai tazarar yawa,banbancin da zai iya kiransa kwatankwacin nisan dake tsakanin sama da qasa,gaba daya ma zai iya cewa wani irin bacci yayi mara dadi cije da kewar widad din,duk juyin da zaiyi sai ya dinga ganin kamar itace a gefansa,amma dole ya tattara dukka wadan nan ya danne can qasan zuciyarsa da qarfin gaske gudun shiga hakkin me hakki. Yana daura links a hannunsa tayi sallama ta shigo dakin,hannunta dauke da plate din data soya plantain wadda ta qone tayi baqi abinta,yadan bita da kallo kadan,tana nan gayanta,bayan wankan ibada da tayi kafin sallar asuba babu wani abu data qara,koda da turare kuwa,wanda zuwa yanzu zamansa da widad hancinsa ya saba da shaqarsa. Yana yiwa turare wani mugu mugun so,amma ita nata ra'ayin sunyi hannun riga da ta'ammali dashi,sai randa ranta yaso,ko kuma aka taki sa'a ranar tana da ra'ayinsa. "Fita zakayi kenan" ta fada tana zama gefan gadon da har yanzu ta kasa gyarashi,don tuni dama yayi sallama da kwana a sashenta "Eh,akwai wani abu?" Ya fada yana takawa gaban mudubi,ya dauki cup din coffe din da yace ta hado masa dashi yakai bakinsa. "Aah,inason zuwa gidan hajiya ne" dire mug din coffe din yayi saman madubin bayan daci ya ziyarci bakinsa,sannan ya zarce da dubanta yana nazarinta. A ka'idarta zaiyi wahala taje gidan hajiyan haka siddan,shi yasa maganar ta bashi mamaki ko a yanzun ma,amma taqi yarda ta kalleshi bare ya karanto gaskiyar abinda ke cikin zuciyarta,har ya gama kallonta,ya jawo qonanniyar plaitain din ya fara kokawa da ita "Saikin dawo" ya amsa mata daga baya,yana tsame hannnunsa daga plate din,yaja tissue yana goge maiqon daya bata masa hannu. Sarai taga yadda ya cakali abincin,abu na farko da ya kamata tayi taji dalilin da yasa bai maida kai yaci ba,tunda fita zaiyi,amma inaaaa,ba wannan bane a gabanta,sai kawai ta kwashe kwanukan bayan fitarsa,ta hada da kudin cefanen daya ajiye mata,duk da babu abinda zasu siya,ta soke a lalitarta,sannan ta shiga bandaki tahau shiryawa a gurguje,don tana da tabbacin zaiyi wuya idan ba gidan hajiyan ya nufa ba,tanason kuma ta cimmasa a can ayita ta qare. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 82 Qwafa taja sanda ta gama parking motarta kusa da tashi,ranta ya quntata sosai,duk sauri da taga yana yi dama nan ya nufa,tafison hakan dama,gwara ayi komai a gabansa,ta kashe motar, saidai kafin ma ta zare key din daga jiki tuni mimi ta bude murfin motar ta fice abunta. Da harara tabi bayan yarinyar,ta tsani yadda take rawar qafa akan wannan tsohuwar,amma tana qara wayo zataci ubanta ne,ba zata dauka wannan ba. Da gudunta yarinyar ta fada falon tana kiran sunan anty widad da hajiya,abbas ya bita da kallo yana hade ransa "Koma kiyi sallama" da sauri ta koma tayo sallamar ta sake shigowa,saidai hakan bai rage mata karsashinta ba,tana shigowar ta fada saman cinyar hajiyan,kafin su sake cewa komai hafsat tayi sallama ta shigo "Ikon Allah,ashe tare kuke" hajiya ta fada tana ma hafsat din sannu da zuwa. Idanunta akan kwanukan daya gama cin abinci, qamshin abincin yana nan daram a falon,kana shigowa kuma zai buwayi hancinka,haushi da kishi suka cikata,abind aya sassauta ma abinda takeji a ranta rashin ganin gilmawar widad din kwata kwata. Saman kujerar dake daura da hajiyan ta zauna,a maimakon zama a qasa kamar yadda ta samu abbas din "Hajiya ina kwana?" Ta gaidata tana sake qarewa falon da kwanukan abincin kallo,a mutunce ta amsa mata cikin nuna kulawa gami da tambayarta yara da kuma gida,duka ta amsa mata da lafiya lau,sai kuma shuru ya biyo baya,dai dai lokacin da baba usaina tayi sallama ta sako kai "A'ah yau kece a gidan?" Baba usaina ta fada tana zama itama,fuska hafsat din tadan saki,saboda saboda alaqar dake tsakaninsu ta amsa mata tana gaidata,suna tsaka da gaisawan mimi ta dami hajiya da batun anty widad "Tana daki,leqa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155