Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 52

Chapter 52

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,318 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

a yadda kike ganin babu ita tayi qaura dake kwata kwata..... tashi kiyi abinda zai fishsheki,ki yiwa zuciyarki qarfa qarfa,kici galaba a kanta,don ki cimma muradinki" ta qarashe maganar tana watsa mata kayan data debo din,sannan ta juya ta fice tabar mata dakin don ta bata damar shiryawa. Bin anty ummee tayi da kallo harta fita,sanann taja gauron numfashi ta miqe ta soma daga kayan tana kallonsu,tana jin qirjinta na mata wani zafi,tana jin kamar ta cinnawa gidan wuta gaba daya,sauqi sauqi daya takeji a ranta,idan ta tuna qaramar yarinya za'a kawo mata,tana da ikon juyata duk yadda takeso,amma ta wani bangaren tana jin zafin yadda ya dauko yarinyar da ta kusa haifarta, tabbas banda gidansu ana zaman karatu ta haifi yarinyar,idan ta zauna ta lissafa shekarunta da nata. Bata damu da canza undies ba,tunda a nata ganin basa cikin abinda zaka damu da canzasu koda yaushe,ta riga data saba,sometimes abbas ke sakata canzawa,idan ta tarasu zaiyita fada sai ya tilastata ta wanke,idan kuma yana free ma baya jin qyashin wanke mata su. Tana gama shiryawa mimi ta shigo da gudu riqe da hannun nawwara,bin yarinyar tayi da kallo,tunda aka fara hidima a gidan taga jama'a taketa murna,rabonta da ganin mutane haka a gidansu tun haihuwar nawwara,a sannan kuma bata da wani wayau sosai "Anty jamila tace ki canza mana kaya,wai anty amarya tazo,yanzu motarsu ta shigo" gaban hafsat yayi mummunar faduwa,tabbas dirin motoci takeji daga harabar gidan,hakan yana gaya mata MUGUN IRIN ta shigo gidanta kenan,zuciyarta na wani irin zafi ta rufe mimi da fada "Anty amaryar ubanki,kike rawar qafa a kanta,ki cewa jamilan ba za'a canza miki kayan ba,tafi ki bani waje tun banyi ball dake ba" tsoro ya kamasu duka su biyun,bama kamar mimi da tayi tsilli tsilli da ido tana shirin saki kuka,dai dai nan anty ummeen tashigo,a bayanta kuma anty atika ce yayarta da suke uba daya "Yauwa,kin gama shiryawa ko?,maza fito gasu sun iso,fito" fuskarta tamkar wanda aka yiwa bushara da rasuwar wani makusancinsa "Na fita nayi musu me?" Kafin anty ummee ta amsa anty atika ta rigata "Ki tarbeta,ai haka akeyi" ta amsa mata tana shigewa toilet din hafsan,don fitsari ne ma ya shigo da ita,banda haka saitayi zuwa dari bata shigo dakinta ba,duk da dama bawai zuwan takeyi ba. Cikin wani madaukakin murmushi take takawa zuwa bakin motocin da sai yanzu suka gama tsaiwa,dai dai sanda anty deena ke tsaye a bakin qofar motar tana karantowa widad addu'o'i tana maimaitawa "Sannunku da zuwa,ma sha Allah" hafsat wadda ta lullube jikinta da kyakkyawan mayafinta kalar lace din jikinta ta fada,fuskarta wadace da fara'ar da takejin dai dai take da kukan mutuwa. Anty madina anty deena anty halima batulu da momma dake wajen dukkansu suka waiwaya suna duban inda maganar ta fito,hafsat din da mutum takwas dake tare da ita,anty ummee da anty uwani ne kawai 'yan uwanta,sauran duka 'yan uwan abbas ne "Yauwa sannunku" "Kun sha hanya barkanku da sauka" qanwar hajiyan abbas din mace mai yawan fara'a karamci da sanin ya kamata ta fada,don kwata kwata takun hafsatun bai mata ba,hausawa sukance wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi,sai ta matsa tana kamo hannuwan widad da anty madeena ta jawa mayafin ta lullubewa fuska sosai,banda kuma tayi mata hakan ita ba sanin anayi tayi ba,ba lallai ta kula da wannan ba "Lale maraba diyarmu,taso a hankali" ta sake fada tana tayata tasowar,ta cikin mayafi widad take mita ita kadai,kawai an qunshewa mutum kai?,wannan ai rashin gaskiya ne,ita me tayi daga zuwanta ba za'a barta bama taga hasken garin daga baya sai a rufe mata kan,da wannan tunanin tabi bayan gwaggwo mero qanwar hajiyan zuwa cikin gidan,duka sauran jama'ar suka bi bayansu. Kusan hafsatun ce a qarshe qarshe,tana biye dasu, idanunta da zuciyarta kamar zasu fado,sai data cewa anty ummee ba zata fito ba ta tilastata,ta fuskanci akwai munafukai cikin 'yan uwan abbas dake murna da wannan auren,amma koma meye zatayi maganin kowa,bata ta yarinyar,don kallon farko tun bataga fuskarta ba ta tabbatar yarinyace din sosai kamar yadda akace. A babban falon hafsat da abbas yasa aka gyara mata shi duka don ya danni zuciyarta aka fara yiwa widad masauki,hafsat din ta shigo sai idanu sukayi kanta,wasu nason ganin launin fuskarta ne,yayin da wasu ke mamakin shigowar ta a qarshe,tayi ta maza ta aro dakiya da juriya tana sake musu sannu da zuwa da kuma sannu da hanya. Duk da cewa AKWAI WATA A QASA amma SANIN GAIBU sai Allah,hakan sai ya yiwa su anty deena dadi,ya kuma dan sanyaya musu zuciya,ko banza awajensu tayi abinda mata dubu suka gaza yi,a irin wannan lokacin wasu suke fara rabar da halinsu. Kanta tsaye ta wuce daura da inda aka zaunar da widad tana murmushi,tana zama sassanyan qamshin da fata da kuma sutturar widad din ke fitarwa ya ziyarci hancinta "Sannunku da hanya" ta sake fadar kalmar da tun dazu ita take maimaita wa,sannan ta dora "Sannu qanwata" idanunta nakan fuskar widad ta cikin mayafi,don har yanzu bata samu nasarar kallon fuskar tata ba,bata amsa ba kamar yadda bata motsa ba,anty halima data gama qarewa hafsat kallo a fakaice ta motsa,tace ayi salati ga annabi. 'yan addu'o'i aka yi sannan suka gabatar mata da amanar widad din. Wani murmushi ta saki,inda ace ba akan plan take komai ba....ashar shine abu mafi dacewa ga wadda tace ta riqeta amana,amma babu komai,akwai lokaci,a juri zuwa rafi... "Ai Allah ne ya hada zamana da ita,ita din koda baku fada bama ai tamkar qanwa take a gareni,ai babu komai,in sha Allah,zaku yaba,Allah dai ya bamu aron rai" ta qarashe fadi tana kuma fadada murmushinta,cikin zuciyarta tana ayyana kwana nawa zata gudu da qafarta,ko su dawo su kwashe ragowarta. Addu'a aka sake rufewa da ita,sanann suka dunguma sassan widad,sassan da a lokacin aketa kaya kayan shigar da kayan jerenta,wanda motoci uku ne manya suka iya daukesu,irin kudin da ummu da alhaji suka fitar basu tana fidda makamancinsa ba akan bikin jika,gefe daya kuma ga abbanta shima da yayi tasa bajintar,abun da ya bugar dasu batulu sosai,suka kuma sake tabbatar da cewa hae yanzu yana qaunar fatima,daga yadda ya aurar da autarta cikin girma,saboda bai taba irin wanna hidimar ga sauran yaransa ba,da sukayi qorafi sai.ya gaya musu,ita din nesa za'a kaita,duka yaransa kuma babu wadda aka taba kaiwa nesa,bugu da qari duk wata dama da wani alfanu da mutumin dake kusa da gida zaya samu ita banda ita,sunyi mita sunyi qorafi har suka gaji suka godewa Allah. Babban falo ne dake dauke da dakuna guda biyu,sai kitchen dining area da kuma ventilation ta baya,ginin yayi kyau sosai gwanin qayatarwa,komai kuma a wadace babu matsi. Basuyi minti talatin ba hafsat tasa aka kai musu coolers din abinci da tasa akayi musu,suna fara ci kusan suka ajjiye,nujood wadda aka taho da ita tace kuma sai 'yan kano zasu koma zata wuce gida ta ajjiye nata plate din itama "Nifa wallahi dana sani masauki nabi su na'eema,wannan abinci haka?" Ta fada tana yatsina fuska,harararta hajjaa tayi "Bamason abun magana daga zuwa baqunta malama,idan zaciki kici,idan bakici ki ajjiye musu kayansu" "To nima dai shuru kawai nayi,abun dai to....." Latifa ta fada yana yatsina fuska,duk sai aka kwashe da dariya,ashe kowa shuru kawai yayi yake kaiwa cikinsa,kada ya fara magana aga gajen haqurinsa,musamman

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});