Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 70

Chapter 70

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,325 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yana fadin "Barka da zuwa oga" qaramin murmushi ya saki,yana hangoshi ta madubin,mutum badai barkwanci,ya tsaida motar dai dai sanda ya qaraso gefan window dinsa. KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 45 "Barka da dawowa oga,tun wancan satin muketa zuba idanun dawowar ka,har mai gida yana tambaya" miskilin murmushi ya fita a fuskarsa "Naso dawowa,to amma ban gama shirye shirye bane,mun sameku lafiya?" "Lafiya sumul oga,ya hanya?,ashe an samu qaruwa?,to Allah ya sanya alkhairi,yasa abokiyar arziqi ce" bala mai gadi ya fada yana murmushi "Ameen"ya amsa masa a taqaice,sai ya zagaya da sauri ya soma budewa widad qofa yana fadin "Madam barka da rana" nauyi ya saukarwa abbas,da alama bala baisan qaramar yarinya bace yake gaidata,duk da ya bude motar bai damu ba yaga ta sake maimaita gaisuwarsa,sakato widad tayi cikin rashin sabo,wai yau ita ake gaisarwa?,ita da take gaida jama'a? "Ana magana" abbas ya fada yana cire belt seat dinsa,maimakon ta amsa saita maida masa gaisuwar,saboda rashin ganin dacewar ta amsa din,amsawa yayi ya kuma bisu da addu'ar zama lafiya da zuri'a ta gari,ita dai tana jinsa ba tare data amsa ba. Muqulli abbas ya miqa masa sannan yace "A shigo min da kayan qofar parlor bala" "An gama oga" ya fadi yana karba da hannu biyu "Muje" ya sake fadi yana duban inda widad taja ta tsaya,tana kuma bin gidan da kallon baqunta. Wata siririyar hanya suka bi,sai gasu qifar wata qaramar baranda mai kyau dake dauke da wata qofa mai dam fadi,yasa key ya bude qofar ya shige,ta bishi a baya,kamar za'a ce kettt ta zura da gudu. Madaidaicin falo ne amma ya qawatu matuqa,akwai qofofi guda uku a cikinsa na bedrooms guda biyu,daya qofar kuma ta kitchen ce sai dining area,sai qaramar qofar da zata fiddaka bayan gidan. Qarasawa yayi gaban daya daga cikin dakunan ya buda daya "Ki shiga nan kiyi wanka ki huta" bata iya amsa masa ba,sai gaba datayi zuwa qofar dakin tana raba idanu,turqashi,yau fa ake yinta,a wanann dakin zata zauna ta rayu ita kadai?,abinda yake nufi kenan?,ga gidan ta fahimci babu wadatar hasken rana,duk da cewa yammaci ne amma alamu sun nuna hakan,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta sanya kanta cikin dakin,dab da zata shige yace "Ki rubuta duk abinda kikeso,zan aiko a karba sai a kawo miki" sai a sannan ta samu daga masa kai,qwalla tana cika mata idanu,har yayi gaba ya dakata,ya juyo a nutse ya sanya idanunsa cikin nata "Me ya faru?"ya tambayeta yana kallonta,cikin jajircewa tayi qoqarin maida qwallar data cika mata idanu "Tsoro nakeji"ta amsa masa kai tsaye "Tsoron me?"ya tambayeta cikin mamaki, maimakon ta amsa masa saita maida dubanta ga dakin da ko qwan wutarsa ba'a kunna ba,saboda haka ya danyi duhu,gyara tsaiwarsa yayi,tana jin tsoro,to amma kuma baisan me zaiyi mata ba,hakan yana nufin saidai suyi sharing daki ita dashi?,kai ya girgiza kadan "NO" ya amsawa kansa,sai yanzu ya tuna da dan banzan tsoron da take dashi,ya manta the first time he saw her...ihun kyankyaso taketa yi,harda cire dankwali,takawa yayi ya matsa zuwa inda take tsaye,ganin ya nufota ta tuno da wani abu,tayi hanzarin jaa da baya a tsorace,har abun yaja hankalinsa,yadan dubeta kadan sannan ya dauke kansa,wannan bayan tsoron su kyankyaso hala harda tsoron mutane ma tanayi?. Qwan wutar dakin ya kunna,haske ua gaurayeshi,abinda ya rage mata tsoron dakin kenan,ya fita a dakin ya bata waje yana cewa "Sai anzo an share dakin,akwai qura" saboda sanda hafsata ta tashi tafiyarta a birkice ta barshi,shi kuma takaici yasa ko takan dakin bai sake bi ba tunda ta fita daga ciki. Sai data tabbatar yabar wajen sanann ta saka kai cikin dakin,ta tsaya tana duban komai,a hautsine yake,ji take yi ba zata iya zama ba,don kafin tafiyar latifa ta koya mata yadda ake gyaran bedroom xuwa falo,kuma babu laifi hannunta yadan fada,ta janyo jakarta zuwa tsakiyar dakin tayi mata waje. Zama tayi tana qarewa dakin kallo,idanunta fal hawaye,ta rasa qwarin gwiwar gyaran dakinma gaba daya,tana jin kamar an dauketa daga duniyar ta an kawota wata duniya ta daban. Bata tashi ba sai da aka kira magarib,ta miqe tana kame jikinta waje daya,saboda dakin ya mata datti,kasancewar bata taso ta saba zama cikin dauda haka ba,koda yaushe zaka samu sassan ummu qal qal,ko tsinke bata bari ya sauka,shi yasa basa shiri da jikokinta,don da zarar kazo ka zauna ta fuskanci kai dan bata guri ne yanzu zata koraka,widad dince kawai keyin yadda takeso a sassan ba tare data hanata ko tace mata komai ba. Toilet din ta shiga tayi alwala,tazo ta shimfida dankwalinta ba tare date nema abun sallah ba ta tada sallah,ko da ta idar tana zaune a wajen,har zuwa sanda aka turo qofar dakin,ta waiwayo a tsorace,saita zuba masa ido sanda yake shigowar,tsoro na kamata,a yanzun ya canza shiga,shirt da trouser ne a jikinsa da suka dace da jikinsa,suka fidda qirar jikinsa dake tafe da tsaho da murjewad jikin kadan,don ba zaka kirata qiba ba. Ido ta lumshe,tana jin dadin qamshin turarensa har qololuwar ranta "Kinyi sallah ne?" Kai ta gyada masa ba tare data iya kallonsa ba,sai ya dauke idanunsa daga kanta ya kalli agogon hannunsa "Zan dan fita....." Tun kafin yakai qarshe ta daga manyan idanunta ta watsa a kansa,haka kawai yaji nashi idanun suna lanqwashewa zuwa lumshewa,kafin ya budesu ya azasu a kanta,har zuwa sannan manyan fararen idanunta suna kanshi,ta yaya zai fita ya barta a wannan gidan ita kadai?,duk da bata da tabbacin ita daya ce cikin gidan gaba daya,amma itakam ko dakin ummu bata yarda ta zauna ita kadai,inaga gidan gaba daya "Bazan dade ba zan dawo,za'a knocking za'a kawo abinci,saiki bude ki karba,idan kuma wani abu ya taso ki kirani a waya" wani mugun tsoro ne ya shigeta sanda ya juya yana ficewa,kuka sosai yazo mata,ta cure waje guda tana cusa kanta tsakanin qafafunta "Wayyo ummu"ta fada muryarta can qasa wadda ke cike da kuka,sun kawota inda bata da kowa,kamar basa sonta,itakam meye tayi musu?,sai taci gaba da rera kukanta a hankali,har zuwa sanda taji kiran sallar isha'i ta miqe ta bada farali,ta sake komawa yadda take. Tana jin anata knocking kamar yadda yace amma ko yunwa zata kasheta bata jin zata iya miqewa zuwa falon har ta bude,tana jinsu har suka gama bugunsu suka tafi,saita sake sakin kuka tana takurewa waje daya. Lokaci lokaci tana duban agogo tare da fadin "Allah kasa ya kusa dawowa" saita sake maida kanta tana sharar hawaye,har kusan awanni uku babu shi babu dalilinsa. A karo na barkatai ta sake daga kanta don kallon agogo,saidai hasken farfajiyar gidan ya hasko mata mage dake tsaye jikin window din dakin nata tana kada jela,wani mugun tsoro da razani ya shigeta,take jikinta gaba daya ya fara rawa,hawayen idanunta suka ninku,ta fara karanta ayatul kursiyyu a rarrabe saboda yadda bakinta yake rawa,a

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});