Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 96

Chapter 96

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,329 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gaji sosai" "Aikin gama,sauranki wanka,ki dauko kayanki na zuwa gidan biki ki saka,yau duka kayan kwalliyarki ki juyesu a fuskarki" ido widad ta zaro tana dariya "Kai anty....suna da yawa fa" dariya itama tayi "Ai wai ina nufin ayi kwalliya da kyau,a saka turaren gida dana jiki ako ina" dan turbune fuska tayi "Wai anty duk uncle akewa haka?" "Kai,ai yafi gaban haka ma,ba kinje min litattafai kika samu kina karantawa ba?,bakiga yadda akeyi bane?" Batason tacewa anty deena din eh,saboda wasu guraren cikin litattafan kunya suke bata(tsarkakakkun litattafai wadanda babu batsa a ciki sai qaruwa),kai ta gyada mata a kunyace "Good,maza kije ki shirya to" cewar anty deena,daga haka suka katse kiran,ta dauki wayar ta wuce bedroom dinta,tana tafe tana hangen dining din kamar wani zai bata mata aikinta,saidai murmushi kawai takeyi najin dadin yau ta qure adaka tayi abinci,gidan kansa yadda yau ta gyarashi ita da kanta yana bata mamaki. Sai data bata lokaci a daki tana zaben kayan da zata saka,anty deena dai tace mata atamfa,ita kuma babu abinda tafiso irin doguwar riga abaya,don kusan kullum itace shigarta,kamar kuma sunsan zabinta sun sakota da yawa sosai a lefenta,tana kallon abayar ta haqura,ta ciro atamfa riga da skert,blue black mai adon maroon,sannan ta shige bandakin ta hada ruwan wanka ta fara wanke jikinta. Tana wankan tana 'yan waqe waqenta qasa qasa,saboda yau din nishadi takeji cikin ranta,ta gama cuda jikinta ta shige asan shower ruwan yana ratsata,saita tuna gida,ummu na hanata shiga shower saboda wasa takeyi da ruwa, kuma tana jiqewa har kanta ne,sumarta nada tshao da yawa,yawancin lokaci saidai a saka hand Drayer a busar mata da ita,saita saki murmushi,tana jin ba dadi cikin ranta,ko sai yaushe zata ga ummu?,bata tabq zato a rayuwarta zatayi nesa da ummu har haka ba ta kuma haqura ba. °°°°"alhamdulillahi" hajiya ta fada tana fitowa daga motar bayan tsaiwar motar tasu a farfajiyar gidan,murmushi abbas yayi "Yau gaki a kaduna dai" sai tayi murmushi "Eh nufin Allah kenan" yana janye da trolly dinta, muneera na dauke da jakar hannunta suka doshi sashensu. "Assalamualaikum mutan gida" hajiya ta fada tana murmushi idanunta cikin falon,wani boyayyen ajiyar zuciya abbas din ya sauke,saboda hango warmers da yayi saman dining din,uwa uba yadda fakon yake a tsaftace ya qawatar dashi,duk da dama bai tana ganin wani abu na qazanta ko qanqani a tattare da ita ba,hasalima yana mamakin yadda bata son taji ta taka datti "Ki zauna hajiya,inajin tana daki" ya fada yana janye mata pillow din kujerar,tayi bismillah ta zauna,haka kawai taji ranta yana mata dadi,ya juya ya dubi muneera "Ki samo muku ruwa da lemo" "Aah,bari dai matar gidan ta fiti tukunna ta shaida xuwanmu ko?" Murmushi abbas yayi "Peace maker" shine sunan da sau tari yake kiran hajiyarsa,bata qaunar tashin hankali ko kuma husuma ko kadan. Kayan daya gani baje saman gado yasa hankalinsa yadan tashi,bai kuma ji motsinta ba,ba tare da tunanin komai ba ya murda handle na bandakin ya tura ya sanya kansa. Dai dai lokacin da take tsaye babu komai a jikinta,sai towel a hannunta tana tsane gashin kanta,mugun zabura tayi ta kuma tsorata matuqa,saidai data waiwayo suka hada ido sai taji kamar zata narke a wajen,saboda tsorata saita jefar da towel din,ta kuma sulale a wajen ta duqe tana cure jikinta waje daya,ko ina na jikinta rawa yakeyi,take ta fash da kuka. Shi din ma kamar an jona masa lantarki haka yaji,ganinta a hakan ba qaramin al'amari bane a zuciyarsa da kuma gangar jikinsa,ya rintae idanunsa ya koma baya days saut yana mayar da qofar yadda ya ganta,saidai ya kasa sakin hannun qofar,yayi tsaye riqe da handle din yana maida mumfashi. A hankali yaci gaba da sauke jumfashun nasa ta baki data hanci,ya bude idanunsa a hankali yana jiyo sautin kukanta,yasan yau kam ya taro match,sai ya matsa jikin qofar cikin kasala yace "Am sorry" shuru bata amsa masa ba,sai ya sake daga murya "Am very sorry" cakin muryar kuka tace "Kana sane ka budeni,ai kasan wanka nakeyi" murmushi ya saki tsigar jikinsa na sake zuba a,daga dawowarsa ta masa wani irin kunnawa da yasan bashi da maganinta "I swear bansan kina ciki ba.....am sorry.... please kiyi shuru mana" "Allah tunda ka ganni tsirara bazan yadda ba" ta fada bayan ta miqe tana daura towel dinta da sauri,tana tsoron kada ya dawo. Murmushi mai kama da dariya ne ya kubce masa,shagwabarta tana kasheshi ainun "To shikenan,let me come inside,sai na cire kayana kema ki rama,kinga shikenan anyi one one" "Wayyo ummuna....Allah karka shigo,idan ka shigo saina gayawa ummu" ta fada tana gunjin kuka jin yana taba qofar kama zai bude,dariya sosai ta kamashi har sai daya dan sunkuya "Alright.....alright,shikenan,khalas.....ya isa,am sorry,ki qarasa ki fito,hajiya na falo tana jiranki" ya danja da baya har yanzu fuskarsa murmushi ne kwance akai ya baro dakin,gaba daya bacin ran daya taho dashi babu kaso hamsin cikin dari. Da sauri ta miqe ta qarasa wankan jin cewa hajiya ta qaraso,ta shirya a gurguje,bata saka komai kan fuskarta ba,saisai jikinta ya wadata da turare,sanon turare ne ta bude cikin kayan lefenta. Rungume hajiyan tayi abinta tana jin dadi,sai take ganin kamar ummunta ce tazo,ta ma mance dashi a wajen,suna gama gaisawa ta gabatar mata da lemuka da ruwa "Hajiya na kawo miki abinci?,ni na girka da kaina" ta fadi tana murmushi,ta qagu taci taji me zata ce,dariya tayi "Bari nayi sallah tukunna widad,nunan bandaki" Dakinta ta kaita ita da muneera duka harda kayansu,sukayi sallah sannan suka dawo falon ta fara zuba musu abincin,a sannan abbas daya fita salla masallaci bai dawo ba. Hankali kwance suke cin abincin suna hira,duk yau sai widad takejinta free kamar a gida,babu wanna kadaicin ba komai,har suka gama bai dawo ba,sukaci gaba da hirarsu hajiya na jinsu,yanayin da taga widad yayi mata dadi sosai,saboda ta qara wani irin haske akan wanda take dashi,hakanan ta murje sosai,duk da ba qiba tayi ba,amma fatarta tayi kyau. Yamma liqis ta sake shiga kitchen ya gwada yin tuwo miyar kubewa,tanata taraddadi kada tayi kwaba,cikin ikon Allah sai gashi tayi shi fes,abinda ya faranta mata ranta,ta gama suka gyara kitchen din,muneera tayi mata wanke wanke sannan ta gabatarwa da hajiya bayan sunyi sallar magariba. Farincikin da hajiyar ta tsinci kanta a ciki ba dan kadan bane,zata iya cewa kaf rayuwarta bata taba cin.abincin gidan abbas din ba sai wannan karon,karamcin da yarinyar ta nuna mata ya qara dad'ad'a abincin a bakinta,ya kuma qara mata qaunar widad din a zuciyarta. Tana ta so tayi wanka amma kuma sai takejin nauyin hajiyan, saboda ba zata iya tube kayanya cikin dakin ta shirya ba,sai ta basar kawai sukaci gaba da hira abinsu. Ana idar da sallar isha'i dukka suna falo,a sannan yayi sallama ya shigo,hannunsa dauke da leda,dukkan alamun gajiya sun bayyana a tare dashi. Kusan a tare sukayi masa sannu da zuwa,ya amsa yana zubewa gaban hajiyan yana mata barka da dare "Ina ka shiga haka?,tun dazu nake taraddadi" "Wallahi na leqa office ne,akwai ayyukan da nakeso na rufe file dinsu kafin mu wuce,kuma zan dauki excuse ma.na tafiyar tamu".kai ta jinjina "To Allah yayi.jagora ya dafa" "Ameen ameen hajiya,kunci abincin dare?" Sai da tayi murmushi sannan ta amsa "Munci abinci kuwa,tuwo ma,mun qoshi kuma alhmdlh" "To ma sha Allah" ya fada ransa na masa fari,bai

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});