Chapter 131
Chapter 131
kasan ba haka ka auroni ba,kuma ba haka nakeyi ba tun farko ba,yanxun yarane da hidimar gida ta yimin yawa" ransa ya baci sosai,a qalla tunda taga laifinta quru quru ko accepting ai ya kamata tayi ko?. "Ina yaran suke?,ni ban gansu ba,yara qwaya biyu kacal?" Ido ta fidda "Aikai raina hidimarsu kekeyi?" "Eh na raina,tunda koni ija iya hidimarsu,meye bana iya musu?" Baki ta tabe tana riqe qugunta,shikam ya fiya jidali da daga hankali,batasan meye damuwarsa ba da rayuwarta,yanzun nan ta gama gyaran sashensa ko hutawa batayi daga wahalar aikin ba ya tasota a gaba yana son tozartata. Wani bacin rai dake taso masa ya hadiye,cikin danne fushinsa yace "Am tired.....na gaji da wannan halayen naki hafsat,anzo gabar da dole ki gyara,bazan ci gaba da lamuntar haka ba" maganarsa ta farki zuciyarta ta kawo mata fassararta,zuciyarta na sake qarfafa mata gwiwa ba shakka akwai wata a qasa,bai taba gaya mata wannan kalmar ba sai yanzu,anya yarinyar can kuwa bata fara zamewa rayuwarta barazana ba *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 86 "Ka gaji?,ka gaji dani kenan kake nufi?,saika dauki mataki ai k......." Kafin ta qarasa ta daka mata tsawa,dukkan yadda yakeson ya taushi kansa haqurinsa ya gaza "Kada ki gayamin maganar banza da wofi,kin dauka ina tsoronki ne da bazan iya daukan mataki a kanki ba?,to ki shiga hankalinki wallahi,saboda idan nace hukuntaki zanyi abun bazai miki da kyau ba" yana kaiwa nan yayi gaba abinda har yana yin ball da botikin daya ciko da tarkacen kaya masu tsada daya wulaqantar. Da kallo ta bishi zuciyarta na suya,mamaki kuma ya cikata,wai yau ita abbas yakewa haka?,sai zuciyarta ta karye qafafunta sukayi sanyi,hawaye ya fara sauka daga idonta,ta koma ta zauna gefan gadonta tana share hawaye. Zuciyarsa na zafafe sosai sanda ya baro mata sashen,ya isa sashensa kai tsaye ya wuce bedroom dinsa,wannan karon bazai qyaleta ba,ko yaya zaiyi magana da wani magabacinta ko za'a samu sassaucin wani abu,yana tsoron faruwar abubuwa da yawa a nan gaba daga gareshi,baisan me zamansu zai zama ba a gaba,ga yara mata da yake dasu da yasan dolen dole wataran gidan wani zasu je,uwa uba kuma yanayi na lafiya,ta yaya muhalli babu cikakkiyar tsafta za'a samu ingantacciyar lafiya?. Saman sofa bed dinsa ya zauna yayi waya ta a qalla mintuna goma,koda ya gama wayar riqeta yayi a hannunsa yana jin banbarakwai babu dadi,yau ya aikata abinda bai taba aikatawa ba wato kai qarar hafsat din, tsahon zamansu tare na wasu shekaru. Ta bangaren widad tuni ta gama tsaftace sassanta, hankalinta bai kwanta ba saida ko ina ya dauki qamshi,ta fiddawa mimi uniform dinta ta sake mata wanka,akwai ragowar kayanta a sassan tun wancan zuwan da tayi,ta saka mata su,saita tsaya tana kallonta. Yarinyar kyakkyawace,kawai rashin tsafta da gyara ne yake dakushe duk wani kyau nata "Anty ki kaini wajen daddy yaga kwalliyata,dama inata cewa mommy tayimin tana cewa bata da lokacin wannan" murmushi ta sake "Wanka zanyi nima,ki bari idan nayi saina kaiki" marairaicewa tayi "Don Allah anty,nidai yanzu" ba yadda zatayi,dole haka ta dora qaramin mayafinta ta kama hannun mimin suka fice tana cewa "Duk chocolate din da daddyn ya baki kin yarda zamu raba?" Tana dariya ta gyada mata kai. Babu shi a parlor din sanda suka shiga,saita cewa mimi "Bari na duba shi a daki" ta gyada kai yarinyar ta zauna saman kujera cikin zaquwa. A nutse ta tura qofar dakin,daidai lokacin da yake zaune cikin sofa bed din,ya kwantar da bayansa sosai a jikin sofa din,idanunsa da suka rusuna ya daga yana kallon fuskarta sanda ta tsaya daga bakin qofar tana riqe da handle din tana kallonsa kamar yadda shima.ya zuba mata ido,duk sai taga kamar ya sauya daga zuwansu bauchin. Hannunsa ya daga yayi mata nuni da tazo,ta saki qofar ta soma takawa a hankali kamar mai tausayin qasa,ya zuba mata ido yana jin nutsuwa tun gabanin ta iso gareshi. Hannunsa ya bata sanda ta iso kusa dashi,ta saka nata hannun a ciki,sai ya fincikota cikin jikinsa a tausashe,ya mata kyakkyawan masauki a qirjinsa,yasa labbansa masu taushi yayi kissing goshinta,sai ta dan saki ajiyar zuciya "Mimi na rako zata nuna maka kwalliyarta" ta fada a shagwabe kamar yadda ta saba yi masa magana,birkitota kadan yayi yana kallon fuskarta "Ina taki kwalliyar.....ita tafi muhimmanci" kunya ta kamata ta sauke fuskarta a qirjinsa tana shaqar daddadan qamshinsa "Banfa yi wanka ba,aiki na gama yi,gurin duk yayi qura" girarsa ya dage sama duka biyun "Iyyee,abun 'yar haka ne?,shine kika share iya wajenki banda nawa ko?" Kai ta girgiza da sauri tana 'yar dariya "Ba haka bane uncle,nasan mummy hafsat ta gyara maka fa" kai kawai ya jinjina "Yanzu yaushe ne za'a yimin kwalliyar,ta musamman nakeso,i will pay" dariya ta saki,tanajin dadin yadda yake yaba komai nata "Za'a yi maka uncle" ta furta tana rufe fuskarta da hannunta "That's my baby doll" shima ya amsa mata yana jan dogon hancinta "Muje naga mimi' ya sake fada yana dagata a jikinsa,gaba daya sai ya rasa kaso hamsin na bacin ransa, shigowarta kawai ya tafi da komai,ta miqe ya sanya hannunsa cikin nata ya riqe gam suka fara takowa xuwa falon. Babu irin abinda bata saqa a ranta ba sanda take tsaka da kukan,sai datayi me isarta sannan ta dauraye fuskarta,bata da wata mafita,komai ya tsaya mata cak,batasan me ya kamata tayi ba,saita dauki wayarta ta soma lalubar number anty ummee ko xata samu wasu shawarwari. Abun takaicin tana kira taji suna sanar mata kudinta ya qare,dama already taci bashin mtn na kusan dubu uku,duk kuwa da cewa duk wata sai abbas din ya saka mata kudin credit ta account dinta bama credit din ba,taja tsaki ta sauka ta koma bank dinta ta sakawa layin bashin da suke binta,bonus din da suka bata tayi amfani dashi ta kira anty ummee din. Shuru tayi har ta gama bayaninta sannan ta dora "Ina tsoron kada yarinyar nan ta fara shiga rayuwarsa anty ummee,ni zuwan nan da sukayi ma sai naga kamar ta fara budewa ta zama mace,harda kai mata kayanta sashenta fa,duk da na sanshi bashi da girman kan wannan wa iyalinsa,amma yarinyar ai bata cancanci wannan kulawar ba" baki anty ummee ta tabe,tana jin kamar ta jawo hafsat din tayita jibga "Nidai da farko saidai nayi miki addu'ar Allah ya yaye miki wannan baqar qazantar,bansan irin ribar da kike samu da ita ba" maganar ta bata ran hafsat,don duk yadda kake da ita kace mata qazama ce to sai an ganku a rana "Meye haka anty ummee?,nifa ba akan wannan na nemi shawararki ba,tunda dai ni ina iya bakin qoqarina,abubuwane sukeyimin yawa,kuma nayi nayi ya daukon mai aiki yaqi,to bazan kashe kaina ba" kai anty ummeen ta jinjina,gwara ta bita a yadda suka soma,kada ta yiwa kanta rasa rasa "Ke gaskiya ce baki so,na daina kuma gaya miki,amma indai kansa kike san shawowa dole kidan gyara inda idanunsa zasu ganki tsaf,tunda da tsafta aka jarabceshi ke kuma ea qazanta.....muddin kinason ganin dai dai dole ki sauko daga ra'ayinsa kibi nasa ko yaya ne,koni da kikaga ina yadda nakeso,wasu abubuwan ra'ayinsa nake bi kafin na murda idan naga ya biyu yadda nakeso na koma kan nawa ra'ayin" sun dan dauki lokaci suna fafatawa ma kafin hafsat ta fahimci abinda anty ummee
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155