Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 90

Chapter 90

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,309 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

manta am a police,da tsalle daya muna iya hayewa saman gini dake da tsahon da yafi na wannan,kin tuna?" Kai ta gyada tana murmushi,saita kasa ci gaba da cewa komai saboda yadda yake kallonta tsakiyar idanunta yana sanyata tana jin wani iri. Shuru kitchen din ya dauka,yayin data buda wayarta tana duba recipe na abinda zata dafa din,tana daukowa daya bayan daya tana ajjiyewa,har ta kammala ta fara aikinta. Haka kawai ya samu kansa da daga kai time to time yana kallonta,hakan ya sanya duk kai kawonta take yinsa cikin idanunsa ba tare data ankara ba,aiki yayi aiki,taja igiyar rigar ta daureta don tafi jin dadin yin aikin,saidai abinda bata sani ba,gaba daya ta fidda shape na mazaunanta qugunta da kuma qirjinta. Ya sake dagowa yaga a inda girkin ya tsaya idanunsa sukayi kyakkyawan gani,yaso janye idanun nasa amma sai ya kasa,karon farko kamar an zare masa laka daga jikinsa,yaso ya maida kai ga wayarsa amma sai yaji ya kasa,dole ya kashe abinda yakeyi din,ya aje wayar a gefe,ya jingina da bango ya harde hannayensa a qirjinsa ya zuba mata idanu. Sam batasan yana kallon ta din ba,saboda ta bada hankalinta gaba daya ga abincin,tanason yayi dadin da zai yaba mata,ta waiwayo zata dauki chopping board har ta juya ta fara yanka albasa jikinta ya bata kamar kallon ta yake,tana juyawa sukayi ido hudu,sai gabanta ya fadi,ta juya da sauri ta saki igiyar rigar tata,ta koma shapeless kamar yadda take idan ba igiyar a jiki,jikinta yadan dauki rawa kadan,ta sunkui da kanta tana yankan da sauri sauri. Bata son kallo ko kadan,bare shi da a duk sanda ya kalleta sai taji nashi idanun kamar sun banbanta dana kowa,ta fara nisa a tunani,don haka har ya sauko daga inda yake zaunen,ya tako a hankali ya tsaya a bayanta bata jishi ba. Sosai ya zuqi qamshin splash da jikinta ke fitarwa kadan kadan yana kadawa hagu da dama gaba da bayanta,taku biyu ya qara ya sake rage kusancin dake tsakaninsu,sai a lokacin taji kamar iskar dake bayanta ta canza da wani kalar qamshi na body mist na daban. Cikin hanzari ta waiwayo,ta manta da wuqar dake hannunta tana datsa albasa,tariga ta dora ashe saman yatsanta ne,tayi wurgi sa wuqar tana yarfar da hannunta gefe daya,saidai duk da zafin da taji kusancin shi da ita yafi daga mata hankali,ta kafeshi da idanu qirjinta na wani irin bugawar da bai taba yiba,ta kuma ja baya sosai har ta qure da jikin kitchen cabinet din. Kallon kallo aka shiga yi tsakanin shi da ita,a hankali ya sanya hannunsa ya lalubo hannunta data yanke din ba tare daya janye idanunsa daga cikin nata ba,sai daya sanya hannun cikin tafin hannunsa sannan ya maida dubansa akai. Kusan lokaci daya suke duban hannun shi da ita,sannan suka kalli juna "Kinga abinda kikayi ko?" Ya tambayeta da wata shaqaqqiyar muryar,kamar jiransa dama takeyi sai ga hawaye ya cika mata idanu "Kaine fa ka bani tsoro" dariya taso bashi amma ya dake,saiya langabe kai kamar yadda yaga tayi "Banda ke banga wadda take tsoron mijinta ba" kamar ya tunzurata,don batason kalmar miji,sai ta fara qoqarin zame hannnunta daga cikin nashi "Ni ba mijina bane kai" "To waye ni?" Ya tambayeta yana dage girarsa sama "Uncle" kai ya girgiza kawai yana sake sakin boyayyen murmushi "Riqe uncle dinki,banaso,let me treat your wound first" ya fada yana sake kamo hannunta. Kujera ya saka mata ta zauna akai,sannan shima ya jawo wata ya zauna,har gwiwoyinsu suna haduwa da juna,ya bude first aid kit din ya fada wanke jinin,yana yi tana rintse idanu,ya daga idanunsa ya kalleta,idanuwansu suka hadu waje daya,sai taji hakan ya mata nauyi sosai,ta kauda nata idanun numfashin su yana gauraya da juna. Har ya gama mata babu wanda ya sake cewa komai,ya sakar mata hannun yana hade kayan waje daya "Jibi idan Allah ya kaimu zanje bauchi" kallonsa tayi da sauri,hakanan kwanakin nan sai ta dinga jin batason zuwa garin "Zanje nayi one week,zamu taho da hajiya,the next day zamu wuce umara ni da ita in sha Allah" zuwan da yace hajiyan zatayi taji yayi mata dadi,har zumudinta ya bayyana a fili "Amma wata daya ya kamata tayi,ko ka dawo da ita nan kawai" ta fada tana langabar da kanta,cak ya tsaya yana kallonta,yaji mamakin jin furucin daga bakinta,abinda bai taba ji daga bakin hafsat ba tsahon zamansu da ita "Hajiya ba zata zauna ba" ya amsa mata yana miqewa riqe da kit din. Koda ya dawo sai ya fara rolling hannun rigarsa zuwa sama,tana daga zaune tana kallonsa har ya gama,idanuwanta suka sauka kan lallausar gargasar dake lullube da hannunsa,abar da take yawan burgeta ba tare da tasan dalilin ko kuma amfaninta "tell me what you are cooking sai na qarasa" idanu ta narke "Zan iya qarasawa uncle,don't spoil it" girarsa ya daga ya watsa hannayensa "I will finished it anyway idan ma baki gayamin ba" ya fada yana qarasawa,ya bubbada tukwanen "Kin kusa gamawa ai" ya fada ba tare daya juyo ba,yana mamakin qoqarin da tayi,kai ta gyada masa. A nutse yake ci gaba da aikin,har ya kammala,duk inda ya motsa idanunta suna biye dashi,yana ankare da ita amma bai nuna ya ganta ba,har ya kammala,zata karba gyara kitchen din shima ya hada ya gyara komai,mamakinsa sake cikata yakeyi kullum,shi kam baya jin aiki ne?. ************Tana nade saman kujerar falon,tayi lamo kamar 'yar magen data samu waje mai laushi,sanye take da atamfa dinkin riga da skert na atamfa,ta yane saman kanta da dankwalin atamfar,jikinta na fitar da tattausan qamshin turarenta,daga gaba kadan kujerar ta uku daga gefanta,abbas ne a tsaye yana qarasa zuge jakarsa ta tafiya,yanayi yana amsa waya daga office,har ya kammala,ya kashe wayar ya sanyata a aljihu,ya dauki jakar ya rataya a kafadarsa. Sai a sannan ya waiwayo inda take zaunen,yadan zuba mata idanu yana karantar yanayin fuskarta,duk sanda zayaje bauchi indai bada ita bane sai yaga wannan damuwar a tare da ita,saidai a wannan karon damuwar kamar tafi ta kowanne lokaci. Yadda tayin kamar wata marainiya ya bashi tausayi da kuma dariya,ya taka a hankali ya tsaya a gabanta,ya miqa mata dogayen lausasan hannunsa. Hannun tabi da kallo kafin ta mayar saman fuskarsa dake dauke da wani irin haiba da wani sirritaccen kyau da ba kasafai kake iya hangensa farat daya a fuskarsa ba,har cikin zuciyarta takejin wani iri babu dadi,saboda wannan ne karon farko da zaije yayi sati daya,kwana biyu rak yake ya dawo duk sanda ya tafin,idan da itane ma suke kwana uku. Sake miqa mata hannun yayi,saita noqe hannun nata tana lumshe idanunta hadi da kwantar da kanta tsakanin cinyoyinta. Murmushi ne mai sauti ya kubce masa,cikin taushin murya yace "Get up,tashi muyi sallama" curewa tayi waje daya,saita saki kuka kawai "Ya rabb"ya furta yana sauke jakarsa daga kafadarsa ya ajjiyeta a qasa,sannan ya duqa saman gwiwarsa a gabansa "Na gayawa hajiyane baki barni inje na daukota ba?,ko na gayawa maman mimi baki amince naje muyi sallama ba?" Furta sunan mommy hafsat da yayi ya sakata zabura,ta kuma daga kanta da sauri,sunanta kawai na sanya gabanta faduwa,hajiya kuwa tana jin nauyi da kuma kunyarta fiye da yadda baki zai furta,dukkansu babu wanda zataso ya gayawa abinda yace zai gaya musun. Kai ta girgiza masa da sauri,ya lumshe idanunsa ya kuma budesu duka

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});