Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 67

Chapter 67

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,307 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

idanu yayi sosai fiye da dazu yana kallon zallar ainihin rashin kunya daga wajen hafsat din,eh rashin kunya mana,banda haka ta manta abinda tayi masa "Tunda kika zabi zama a bauchi baki isa ki bini ko ina ba,kince na nema mai zama dani a kaduna kuma na samu fine....na dauka hankali kikayi kika fara gyaro kura kurenki,ashe ba haka bane,to a wannan karon ina mai gaya miki da kakkausar murya,kibi a hankali,don bazanci gaba da lamuntar halayenki ba,if not kuma.....mu zuba dani dake" daga haka yayi gaba ya bude qofar toilet din ya shige abinsa. Wasu qwalla masu zafi ne suka biyo kuncinta "Wallahi zankai inda za'a qwatar min hakkina,nima na gaji" ta fadi tana juyawa da gudu gudu ta fice daga dakin. Sanda ta gifta sassan widad dake kulle sai taji kamar ta koma ta shiga ta shaqeta ko zata rage zugi da radadin da zuciyarta ke mata,amma wata zuciyar ta hanata,ta wuce da sauri sauri zuwa sashenta tana kuka sosai. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 43 Gefan gadonta ta zauna hannuwanta rufe da fuskarta tana kuka sosai,me yasa abbas bazai fuskanceta su zauna lafiya ba?,yasha gaya mata zai bata mamaki,bata taba zaton irin wannan mamakin zai bata ba,ba ruwansa da harkar mata,kamar ma baida damuwa dasu,wannan yasa ta saki jikin cewa duk wani mataki da zai dauka a kanta bazai wuce ya qaurace mata ba,ita kuma bata da wannan damuwar,bata da yawan buqata,tasa buqatar ma damunta takeyi. Wayarta ta jawo dake gefan gadon ta soma laluba number kyawunta zatayi abinda ta saba wato kai qara,saidai tana kallon agogo taga dare yayi,wata zuciyar na ingizata ta kirashi,wata zuciyar na cewa tayi haquri ta barwa safiya,saita aje wayar,amma kuma yadda zuciyarta ta cika ta tumbatsa da bacin rai da kuma fushi,sai taji ba zata iya kwana ita daya da wannan baqincikin a cikin ranta ba,don haka ta sake daukar wayar ta kira number anty ummee. Cikin sa'a ta shiga,tana shiga din kuma ta daga "Ke lafiyarki a wannan tsohon daren?" Ta jefa mata tambayar jin ta fashe mata da kuka "Anty kaduna zai dauketa jibi su tafi" "Ita wa?,au amaryar taki?" Kalmar tayi mata ciwo,amma saita gyada kai kamar tana wajen "To sai kuma me ya faru?" "Na gaya masa ni.ban yarda ba,shine yake wani gayamin wai aini na zabi haka, mukayi fada dai dashi na baro masa dakin" wani tsaki anty ummee taja "Dadina dake wallahi baki da qwaqwalwa kwata kwata wani zubun hafsatu,ke da zaki nuna murna,kice hakan da yayi shine dai dai,zasufi sabawa da juna?" Ido hafsat ta zaro,kukanta ya tsaya cak "Anty?,suje su kebe su biyu wani abun ya faru kenan fa?,kaduna fa nake gaya miki,gidan da daga shi sai ita" "To ubanme ma zakije kiyi a garin da baki da ko kashi?,kibar kowa naki asalinki da tushenki a nan,suje sai sun dawo,sannan ma kuma sai akace miki haka zaki barta idan sun tashi tafiyar?,tsaya kiji,bude kunnenki da kyau" tarawa anty ummee nutsuwarta tayi,duk da tanajin babu wata mafita data wuce tayi masa bore,ko ya tafi da ita ko ya aje yarinyar a gida,saidai cikin minti biyar da fara sauraran anty ummee fuskarta ta washe da farinciki. **********Tun daren jiya bai kwanta ba sai daya tabbatar ya hada duk kayan da zaiyi tafiyar dasu ranar asabar din,idan da sabo kusan ya zame masa jiki,a shekarun da sukayi da hafsat zai iya irga sau nawa ta taba hada masa kaya wai don zaiyi tafiya ko zai koma bakin aiki. Bai kwanta ba sai kusan biyu na dare,a nan ma tunani ya hanashi sakat,yayita juyi from side to side,yanata bitar halayen hafsat,ya yarda matar aure ta qwarai dace ne,bai taba kawowa hafsat din zata sauya haka ba,bai taba kawowa cewa haka halaye da dabi'unta suke a zahiri ba,bai samu bacci ba sai wajen uku da rabi na dare,asuba nayi yayi alwala ya wuce masallaci. Bai shigo gidan ba sai wajen qarfe tara na safe,ya tsaya taron magidanta da akeyi a unguwar duk qarshen wata,kafin sannan hafsat takai ta kawo a sassansa ya kusa sau uku,so take ta aiwatar da shirinta tun da wurwuri,plan din anty ummee yafi kwanta mata fiye da nata plan din,saboda idan tanason barin garinta to tana qaunar mutuwarta. Sunyi sabani,tana komawa sassanta yana shigowa gidan,kamar ko yaushe a matsayin widad na baquwa sai ya fara da sashenta. Dai dai lokacin suna bedroom din widad din,latifa ta gama musu breakfast,harma sunci,don basa iya cin abincin hafsa,wanna yasa ma basa jiranta,itama kuma ana kwanaki biyar ta daina kawowa,saidai ta aiko a kirata tazo suyi dinner,sai akaci sa'a widad din mai wahalar sabo ce bata zuwa. Sabbin kaya latifa ke ware mata,saboda ta soma shirin komawa kano,amma dai bata bari widad din ta sani ba,don kada ta birkice mata "Wadan nan kayan dasu zakici gaba da kwalliyar,kinji dai abinda anty deena ta gaya miki?" Kai ta gyada "Bakiga kullum sai nayi abinda tace din ba" "Eh amma har yanzu baki qara zuwa wajen uncle din naki ba,kuma na gaya miki a can ake kwana" ido ta fiddo,waisu basa jin kunya suke mata zancan ta kwana da namiji?,bayan ummu ta gaya mata ko hannunta aka riqe ciki zatayi kuma mutuwa zatayi?,kafin tace komai anyi knocking qofar,latifan tasan ba wanda zai.shigo kansa tsaye saimai gidan,don haka ta zube kayan hannunta tana yiwa widad nuni da.hannu akan ta bude qofar. Itakam bata gane komai ba,ta sauko daga saman gadon,ta isa bakin qofar ya buda a hankali manyan idanuwansa suka fada cikin manyan fararen nata idanun,ta saki qofar cikin rashin sabo da d'ari d'ari taja baya tana cewa "Ina kwana?" "Lafiya qalau" ya amsa mata yana duban kayan jikinta,kayan bacci ne riga da wando masu taushi da kauri,wandon iyakarsa qauri,rigar ce ma mai dogon hannu,ya kauda ganinsa yana sanyo kansa cikin dakin,sai tahau raba idanu tana duban latifa dake jiran ya gama shigowa su gaisa ta basu waje,gabanta tana dan faduwa. Gaidashi tayi ya amsa,sai ta juya ta nufi qofa,widad din batayi qasa a gwiwa ba tabi bayanta zata fice itama cikin jin tsoro "Zo nan" ya kirata a hankali,saita waiwayo fuskarta a narke kamar zata saki kuka,ya kalli siraran labbanta jajaye data tabesu "Bari na dauko hijabi na" ta sake fada tana sanya jelar dankwalinta tana faman boyon na shanunta da suka fara bayyana kansu ta cikin rigar jikinta. Dariya taso bashi acan qasan zuciyarsa,ya fuskanci me take boyewa,ko me zasu sakashi ji wadannan qananun abubuwan oho,ya fada a ransa,saiya sanya hannu ya jawo hijabin da ya gani a gefansa ya miqa mata,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,tana ta faman cukuikuye gaban rigarta ta qaraso ta sanya hannu ta karba hijabin ta zura,sannan ya nuna mata waje ta zauna. "Kice ta shirya miki kayanki,gobe in sha Allah zamu tafi kaduna" da farko daya fara zancan

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});