Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 63

Chapter 63

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,316 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

satar kallon widad din,bata da matsala da komai,tana kuma jin komai zai tafi dai dai,damuwarta daya irin kyawun da yarinyar take dashi,tana tsoron kada wannan ya zama mabudin nasarar jan hankalin abbas... "Inaaaa,bazan bari ba" ta tabbatarwa kanta da kanta cikin zuciyarta,zatayi dukkan mai yuwuwa ta hana wannan kyan tasiri a fuska da idanunsa. Kusan da latifa suke hirar,ita widad ta maida hankalinta gasu mimi,kasancewarta mai son qananun yara,duka sai suka ja hankalinta,tana ta duban fuskar nawwara da taga tana mata kama da fuskarshi "Ke dawa kike kama?" Ta tambayi yarinyar tana dan murmushi,mimi tayi wuf tace "Da daddynmu mana,ni kuma da mommy na,wai shine su anty bara suke cewa ta fini kyau,wai daddy yafi mommy kyau" daga idanunta widad tayi ta dubi fuskar hafsat dake magana da latifa,eh itama taga wannan duk da qarancin shekarunta,amma dai tasan kyau "Eh wallahi,ya fita kyau" widad ta fada hankalinta kwance cikin yanayi na quruciya. Rigime mata mimi tayi ta soma qwalawa uwar kira "Mommy,kinji anty ma tace daddy yafiki kyau,kuma nawwara ta fini kyau?" Dariya latifa tadan saki tana kama baki,widad din tayi wauta,amma da alama ma ita a wajenta ba komai bane,yayin da hafsat ta kafe widad da idanu,wani abu mai kama da bacin rai yana motsa mata qasan ranta,sai kuma ta buge da murmushin yaqe "Tsokanarki takeyi,kuma ni nafi daddynku kyau,saidai ya nunamin manyan ido kawai" cikin murna mimi ta waiwaya tana duban widad "To kinji ko?" Dariya ta saki tana jawota jikinta "Wasa nake miki,kema kina kama da daddyn naki ai" kau da idanunta hafsat tayi daga kansu, zuciyarta na raya mata wani abu. Yau dinma kai tsaye sassan hafsat din ya fara isa,bai taras da kowa a falon ba,don haka ya sanya kai bedroom dinta,yana taka lallausan sabon carfet din daya sauya mata dab da bikin nan,amma har datti ya fara cikashi laushinsa ya ragu ainun. Dakin yaran ya fara budewa,komai a hargitse a zaune da duwawunshi,ash and baby pink ne color din dakin,amma pink din har ya dauki hanyar zama ash din shima,ya taka a hankali yana tattare kayan sawarsu dake watse a qasan dakin,sun cakude waje daya,ba zaka banbance wankakke da wanda baida wanki ko kuma guga ba,ya kwashe gaba daya,ya buda laundry basket dinsu da niyyar zubawa,sai ya sameshi a cike fam da kaya. Ransa ya sosu,baiga amfanin yaron da ya aje saboda ya dinga musu wanki ba,bayan duk wata sai ya ajjiye kudinsa,to kudin ake bashi a banza ko kuwa,ya daga kayan da niyyar zubasu a haka yaci karo da undies din hafsat din,harda brassieres. Kishinsa ne ya motsa,ransa ya sake baci fiye da dazu,sai ya watsar da kayan yaran gefe daya,ya soma birkito kwandon,nan ya dinga cin karo da undies dinta,ya dinga tarasu a gefe,har ya gama kwashesu tsaf,sannan ya zuba kayansu mimi din,ya buda toilet dinsu ya leqa,dole ya dawo baya da sauri,saboda abun babu kyan gani,mutum ne shi me masifar tsantsami,idan kanaso kaga fadansa to yaga qazanta. Dogon tsaki yaja kamar zai tsinke harshensa,yana dai tunanin me aikin da bayaso daga qarshe daqyar idan ba ita zai sa a daukowa hafsat din ba,ya gaji da ganin wannan qazantar gaba daya,to amma kuma hakan kamar daure mata qarqashi ne,kada ta sake sangarcewa ta miqe qafa,tun a baya yaqi a kawota dinne saboda gudun ta sake tabarbarewa,amma a yanzu dukka alamu suna nuna daukotan ya kusa zame masa wajibi. Dakin ya janyo musu ya wuce nata dakin,shima dai kamar dakin yaran,shikam natan harda tsami tsamin kayan wanki,bai saka kai da yawa ba ya dawo da baya yana ambaton sunan Allah,sai kawai ya juya ya fice daga sashen gaba daya. Duk da ransa babu dadi haka ya daure ya nufi sashen widad din,tunda dai itama matarsa ce kamar hafsat din,tana kuma da haqqi a kansa kamar ita. Sanda yayi sallama a falon yayi dai dai da sanda widad ke maimaitawa mimi karatun makarantar bokonta,yarinyar kuwa nata kamawa tana amsawa cikin jin dadi,don baqon abune a wajenta,mamarta bata taba tsayawa ko sau daya ta duba assignment dinta ko ta bibiyi karatunta ba,abbas din keyi mata assignment idan yana gari,idan baya nan kuma haka zata koma da litattafan ta, aunties dinsu sunsha rubuto letter suce ta kawo gida,hafsat ke karba,tana gama karantawa take yagawa,ta rubuta reply da cewa ayi haquri,mamanta ba mazauniya bace amma za'a gyara,har sun gaji da rubutun sun qyaleta,saboda suna ganin kudin ubanta ke tafiya,su basu da asara. Rige rigen zuwa yi masa sannu da zuwa sukeyi,widad ta bisu da kallo tana jin damuwarta da kewarta na raguwa,dan zaman awannin da sukayi dasu sun debe mata kewa matuqa. Tunda ya shigo din take bibiyar dukka motsinsa da idanuwanta,tana son taga shin ko zai kalli sassan da widad din ke zaune?,ko kuma zai saci kallonta ko sau daya ne?. *Arewabooks: Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 41 Latifa ce ta fara gaidashi,sannan ta kauce ta basu waje,falon ya zamana iya su yasu. Cikin baqunta tadan motsa kadan tana gyara zamanta gami da hade jikinta waje daya,kamar yadda ummu ta koya mata duk sanda wani baqo ya shigo sassansu,koda kuwa cikin mazan gidansu ne yayyenta 'ya'yan kawunnanta "Sannu da zuwa" itama fa fada kamar yadda su mimi suka fada,ba wani sakin jiki ko alamun sanayya a tattare da ita, yanayin da yayiwa hafsat dadi qwarai,ta kuma sake sanya idanu a tsakaninsu,tana kuma karantar yadda kowannensu ke nuna baqunta ga dan uwansa "Sannunki,kin wuni lafiya?" "Lafiya lau" ta amsa masa idanunta na a qasa,yayin da nasa hankalin yake kansu mimi,sai ya miqe dasu yana bare ma nawwara chocolate din daya shigo musu da ita. "Babu wani abu ko?" Yayi tambayar a wannan karon yana watsa idanunsa a kanta,ta girgiza kai da sauri "Ma sha Allah" ya fada yana kama hannun yaran,a sannan hafsat ta miqe,fuskarta fal murmushi "Amarya ki dinga sakin jiku mana kinji?,ba haka ya kamata ki marabci angon naki ba" sakato widad din tayi tana jin nauyin maganar hafsat din,zancan kuma yana mata girma "Ina zuwa bari.naje,ki shirya xamuci.abincin dare tare kinji ko?" Hafsat din ta fada tana danne dariya,yadda widad din tayi wuri wuri yayi mata dadi,bata amsa mata ba har ta fice. Sam batasan yana tsaye a wajen ba sai da tazo giftawa tana sauri don ta cimmasa saiji tayi an damqo hannunta,ya kuma jawota xuwa gabansa. Hannayensa ya sanya ya zage bayanta dasu,suka tsaya dab da juna suna ma juna kallon cikin idanu,ita ta fara janye idanunta,sabida bata fiya jurewa kallonsa ba,akwai wani irin kwarjini mai yawa cikin idanunsa,shi kuwa ci gaba yayi da.kallonta,irin wannan kallon yana tada masa feelings sosai a kanta,yana kuma karantar abubuwa masu yawa dake kwance a zuciyarta ta cikin idanun nata,saidai ya fuskanci ta koyi dabi'ar kaucema idanunsa din. Dan gyata tsaiwarsa yayi yana sake matsota kusa da jikinsa,duk da cewa ba irin wannan

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});