Chapter 95
Chapter 95
iskar data kwasota bai kalla ba,yaci gaba da shirinsa,kafin ya sanya kayansa ya tsaya ya tsaftace sassansa,ya kuma dafa coffee yasha sannan ya qarasa shiryawa ya fice abinsa,yasan bazai rasa abinci gidan hajiya ba. Tun daga wannan maganar ta dauke masa wuta gaba daya,shima kuma ya tattarata ya watsar ya baiwa banza ajiyarsa,yana ganin guga koda baiyi tsiran komai ba yayi na igiya,ta yaya zatayi kishi da mahaifiyarsa ko nawa kuwa zai kashe mata?,ita din ai ba tsararta bace. Duka kwanakin da yayi kowa sabgarsa yake,amma hafsa din ta fishi damuwa,saboda tana da buqatar kudi a wajensa,baya ga haka tanason ya dawo da widad din har su dawo daga tafiyar,a wata dayan da zasuyi tasan zata moreta sosai,zata kuma dora mata karatun da zai zauna daram a kwanyarta,amma girman kai da jin tafi qarfin tayi qasa yasa taji gwara tayi shuru duk abinda ma ya yanke shikenan. Ta bangaren widad kuwa cikin kwanaki qalilan karatun hausa novels ya shigeta sosai,idan tana karantawa tana jinta ne kamar a wata duniyar ta daban,yana debe mata kewa,tana kuma ganin abubuwan da suke bata mamaki,duk kuwa girki ko drinks din data gani saita gwada,a lokacin kitchen dinta yaga rayuwa,saidai duk abinda ta gwada din idan taga yayi farinciki cikata yakeyi,mai aikin maama(hajiya amina) ke tayata wani bin,tana ganinta kamar latifa saboda kirkinta. Ranar da zai baro kadunan zai biya ta gidan hajiya ya daukota su wuce,har ya kammala shirinsa tsaf a sassansa tana nata sashen tana baccinta,don tun daga waccan ranar basu qara hada makwanci ba,tana sashenta yana nasa,yaci alwashin ko meye zatayi badai shi da qafafunsa ya bita yayi begging nata ba,yasan abinda takeso kenan. Tare dasu mimi suka fito,a wajensa yaran suka kwana,tsaf dasu don su kansu sai daya shiryasu ya kuma gyara sasssan,suna riqe da hannunsa ya tura ya shiga,falon a hargitse kamar wanda aka tashi taron biki,harsa pampers din nawwara da yayi imanin idan bana shekaran jiya bane na jiya ne "Ku zauna nayi sallama da mamanku" ya fada yana kallonsu,sai suka amsa suna hayewa saman kujerar,ya ajjiye luggage dinsa ya nufi qofar bedroom dinta,don ko takalminsa bai fidda ba saboda tsaftar tiles din ma bata gamsheshi ba,duka yayi rod'i rod'i kamar an watsar da ruwan tea ya fara bushewa samansa. Sau uku yana knocking sannan yaji ana tambayar waye da cunkusashiyar muryar bacci,gyaran murya kawai yayi,ta taso tana turbune fuskarta daya kacame saboda bacci ta buda qofar. Ido hudu sukayi, doguwar rigar wata kodaddiyar atamfa ce a jikinta da aka yiwa adon net,net din har ya soma bubbulewa alamun dake nuna ya fara gajiya da aikinsa,kanta gashinta ne him daya hautsine kamar ciyawar da aka tara za'a ciyar da dabbobi,abinka da baqar fata idan bai shafa mai ba....duk jikinta yayi fari fari,dakin yana fidda irin abinda jikinta ke fiddawa,da alama ya kama ko ina. Kansa ya dauke,don takaicinta bazai kasheshi ba,ya fara gajiya da al'amuranta da kullum babu gyara sai gaba da abun yakeyi,ya sanya kai cikin dakin,dole ta kauce masa ya rabe ya shige,sai ya kasa zama,yana kallonta ta tsince pant dinta da bra dake watse a qasa "Ina kwana?" Ta gaisheshi murya a cushe "Lafiya....mu zamu wuce" ya bata saqo a gaggauce,saboda qagauta da yayi da wanzuwarsa cikin dakin,ya zura hannunsa a aljihu ya fiddo rafa na kudi ya matsa gefanta ya ajjiye mata yana cewa "jibi zamu tashi,zamuyi sati uku idan ta kama har hudu ma,saboda inaso zamu tsaya egypt hajiya zataga likita,duk yadda ta kama dai....shikenan babu wani abu?" sai a sannan ta dago ta sake kallon sa "Daa ka sani ma baka shigo ba,inda wucewarka kayi da hakan yafi" tsareta yayi da idanunsa yana mamakin furucinta "Hafsa.....magana nake miki ta zanyi tafiyar da babu lallai na sake dawowa fa" gaba tayi tana qoqarin komawa cikin bargonta "Allah ki yaye hanya" ta fada cikin nuna halin ko in kula taja bargo ta rufa abinta,saidai tuni idanunta sun cika da hawaye,banda qin Allah,da kudin da zataga likitan basai ta haqura ba a biya musu tare,idan suka dawo taga likitan a nan ba,ai duka daya ne,to amma a'ah,wai dole sai an nuna maka iyakarka. Sai daya bata kusan mintuna a tsaye yana kallonta ta cikin bargon,zuciya na hasalashi amma ya hadiye ya juya a hankali ya soma fice daga dakin. Wuf tayi ta yaye rufar ta kuma sauko daga gadon,da gudu tasha gabansa "Au tafiyar zakayi?" Ta fada hawaye yana layi kan fuskarta,kallo daya yayi mata ya kauda kansa,saboda yadda zuciyarsa ke azalzalarsa "Tun ba yau ba nasan baka damu da damuwata ba dama,ba abinda ya shafeka da baqinciki na ko walwalata,to kaje,amma ka sani akwai hisabi tsakanina dakai,Allah bazai taba yafe maka ba idan ka zalunceni" ido ya runtse yana jin zafin maganganunta,ya budesu a hankali sai suka kan yaransu,mimi da nawwara suna tsaye daga bayanta sunyi carko carko,da alama sun fahimci wani abune mara dadi yake faruwa. Maganganu ne da yawa a ransa da amsoshin da zai bata,amma sai ya hadiye,muryarsa a sarqe yace "Naji,Allah ya saka mikin,matsa ki bani hanya" jagale tayi tana kallonsa,sai kuma ta saki qofar ta koma ciki da gudu ta fada gado tana sakin kuka,baiko waiwayeta ba ya matsa zuwa gaba,ya sunkuya yayi kissing goshin yaran sannan ya kama hannunsu zuwa falo ya kunna musu cartoon yayi musu dabara ya fice. Har suka kama hanyar kaduna ransa a bace yake amma yaketa dannewa saboda kada hajiya ta fahimta,yasan yanzu zata gaza nutsuwa. Sai da suka shiga garin kaduna sannan ya fara tunanin yadda zasu samu widad ita kuma,abinci da zasuci da sauransu,yau dai ba makaranta yasan tana gida,to amma abinci bashi da tabbacin zasu samu,tunda ga wadda a haife ta haifeta ma bata da wannan tunanin,ina ga ita?,ya yanke kawai idan sun isa yana kai hajiya ciki ya koma ya siya musu abinda zasuci ya hada musu da order din abincin dare,gobe kuma ya samu time yayi musu,da wannan tunanin suka shiga unguwarsu. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:huguma* Page 62 Tun jiya da ya kirata yace mata gobe zasu taho da hajiya,tayi murna sosai saboda zaman kadaicin ya isheta amma bata kawo wai ta tanadi komai ba,ta dauki littafinta taci gaba da karatunta,tana tsaka da karatun taga inda jarumar littafin ke shirye shiryen dawowar mijinta daga tafiya,abun sai ya burgeta sosai,ta idar da sallah azahar tana saman abun sallah abun ya sake fado mata,saita dauki wayarta ta kira anty deena tana labarta mata "Kema irin hakan zakiyi, bakiga abincin da aka kiya jiya ba a group?" Kai ta gyada "To haka zakiyi,ki shirya shi kamar yadda aka koyar ana shirya abincin mutum" daga kan abun sallar kuwa bata koma yin komai ba ta fara practicing abincin,datayi kuma yayi mata yadda takeso,suna da komai ba abinda zata buqata,saita fara shirya komai tun a ranar. Washegari gari yana yin haske ta gyara gidan,dama ta saba wannan ya fara zame mata jiki,saidai yau har dakinsa ta gyara kamar yadda anty deena tace mata,tana yi tana kiran anty deena ita kuma tana qara mata haske,tana aikin suna video call da anty deena ta watsapp,sannu sannan sai gashi har girkin ta gamashi tsaf,ta kuma zuba a warmer,ta jera,anty deena ta kalla ta cikin wayar,cikin farinciki tace "Well done qanwata,yanzu saura abu daya" langabe kai widad tayi "Allah anty na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155