Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 56

Chapter 56

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,331 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

din bata fahimci komai ba,ta taho abinta ne gaba gadi "Anty deena ta kyauta,kinga ta fiki kirki,sai ita tayi tunanin kizo ki gaida mijinki" ya bata amsa yana sake maida hankalinsa ga system din nasa "Uhmmm" ta fada cikin rashin sabo da kuma baqunta. Coffee din gabansa ya tura mata yana sake kallonta,saita girgiza kai alamun a'ah,saboda ummu ta hanata karbar abun hannun maza,yana nan kuma daram a kanta bata manta ba,bai sake cewa komai ba sai kawai ya miqa hannunsa,ya jawo allonsa yaci gaba da aikinsa,abun da ya dauki hankalin widad kenan,ta dinga binsa da kallo "Dama malamin makaranta ne?,amma kuma nujood tace mata har bindiga ce dashi,to amma wa yake koyawa karatu bayan shi kadai ne a dakin?,inama zai dinga koya mata,tayi missing makaranta da karatu sosai,tanason karatu" ire iren wadan nan tunanukan ta dinga yi,har sai da taga aikinsa yakeyi sosai cike da qawa zuci,ta dan fara motsawa,so take ta koma,amma kuma tasan ba zata iya fita ita kadai ba,saidai ya rakata,amma kuma ta kasa buda baki ta gaya masa. Marker din hannunsa ya ajjiye yana fesar da iska daga bakinsa,yayi taku biyu baya a hankali,sannan ya duqa dab da ita,idanu suka sake hadawa,sai ya kauda kai ya soma zuge jakar dake aje a gefanta,wasu tsofaffin takardu ne da yasa samuel ya kawo masa su zai duba wani abu a jiki,yasoma zarosu,sai tsanya tayi tsalle ta biyosu har guda biyu,daya ta fada gefe dayar kuma kai tsaye ta fada jikin widad. Gigitaccen ihu data saki ya sanyashi watsar da takardun hannun nasa,kafin ya ankara tayo kansa tana tsalle gami da kiran wayyo Allah,wayyo ummu,taso rudashi amma ya tattara hankalinsa waje guda,saidai duk yadda yakeson dawo da ita nutsuwarta widad batasan yana yi ba,mayafi tuni ta cillar dashi,dankwali ma ya zame,lafiyayyen baqin gashinta dake fitar da qamshi ya tarwatse. Suciyarsa tayi wani mugun bugawa sanda ta shige jikinsa tana,sassalkan gashinta ya wanzu a fuskarsa,ihu take da zazzaqar muryarta dake cike da tsoro tana fadin ya cire mata "Calm down,ki nutsu,tsanyace fa kawai" ya fada muryarsa na dan rawa kadan,saidai ko daya bata jishi ba,tsoro ya cika kwanyarta a lokacin. *AREWABOOKS:HUGUMA* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 36 Yadda ta shige masan tamkar zata koma cikinsa,gaba daya ta kasa gane me yake fada,sai kawai ya buda hannayensa,ya kuma rungumeta sosai a jikinsa,yayi mata riqon tsauri ta yadda ba zataci gaba da tsalle ba. A hankali ta fara samun nutsuwa,kukanta ya fara ja baya,sai a sannan kuma ta tuna ajikin wani take,tayi wani irin zillo ta zame daga jikinsa,cikin tashin hankali hadi da wani sabon tsoron,tunda take tsahon rayuwarta ko yatsarta ba wanda ya taba riqewa,amma yau gata a jikin wani?,ta shiga uku?,yanzu shikenan ta zama 'yar iska?,idan ta samu ciki ta mutu fa?,bata kyautawa ummu ba,sai sabbin hawaye suka barke mata,jikinta har rawa yakeyi "Tafiya zanyi" ta fada bakinta yana rawa,kafeta yayi da idanu yanason gane me ya tsoratata kuma dai?,kafin ya gama wannan tunanin aka fara knocking qofar,ya maida kallonsa ga qofar,kafin ya bada izini an murda handle din an shigo. Hafsat ce dauke da jug da cup,da farki idanunta naga abbas,sai kuma sabon qamshin da taji ya baibaye falon yaja hankalinta,a hankali idanunwanta suka sauka kan widad dake tsaye tana tsuma,jikinta yana rawa,kanta babu dankwali bare mayafi,dukka suna watse a qasa,ga hawaye shabe shabe kan fuskarta,gabanta yayi wani mummunan faduwa,abubuwa biyu suka bugeta lokaci daya. Zallar madarar kyau data gani kwance saman fuskar widad din,duk da shekarunta qananu,da kuma tunanin daya darsu a ranta a take a lokacin,abbas ya nemi tarayya da widad din,tunanin daya kusa sanyata zubar da kayan hannunta,jikinta duka ya dauki rawa. A nutse ya amsa mata sallamar,ya dauke kansa ya maida ga widad data fara yin gaba zata fice,har yanzu tana hawaye "Dakata" ya fada cikin salo na umarni,cak ta tsaya amma har yanzu jikinta rawa yake,tasan tata ta qare,tana shiga su anty deena zasu gane wani ya tabata. Inda ta yasar da dankwali da mayafin ya qarasa,ya dauko mata ya tsaya gabanta ya miqa mata yana kallonta,sannan yace da ita "Daura" jikinta na rawa ta karba din,amma ta gaza daura dankwalin,sai mayafin ta yafa kawai "Muje na rakaki" ya fada sannan ya waiwaya ga hafsat wadda ta yiwa kanta mazaunin dole don kada ta fadi "Ina zuwa" yace da ita suka fice shida widad din. Kuka sosai ta fashe dashi kamar qaramar yarinya,da gaske abbas neman tarayya da yarinyar yayi?,har zuciyar abbas ta fara qawata masa ita?,duk qoqari da jajircewar da taketa yi kenan tana neman tashi a banza?,ya akayi tayi saken da har yarinyar tasan tazo sashensa?,ba shakka sanyata akayi,tunda 'yan uwanta suna nan,tabbas ba zata ba haka ta sake faruwa ba,sai ta miqe tana barin flask din kawai ta fito ba tare data bi ta kansa ba,idanuwanta har basa gani sosai saboda tashin hankalin da takejin kanta a ciki,a daddafe ta dinga laluba hanya har takai kanta sassanta. A gaba ya sanyata yana biye da ita har suka isa sasssan nata,ita ta fara knocking,tayi tayi shuru ba alamun za'a bude,sai yace ta matsa shima ya shiga tayata,amma shuru kakeji,saiya waiwayo yana dubanta "I think duka sunyi bacci fa" kai ta langabe tana kallonsa,idanunta na fidda ruwan hawaye "To a ina zan kwana kenan?,don Allah ka tashesu mana" ido yadan zuba mata na wasu sakanni kafin ya kawar da kansa,quruciyarta ta gaske ce "Ki koma ki kwana a can,da safe saina rakoki,lokacin sun tashi ko?" Ya fada cikin sigar lallami,saboda yadda yakejin kansa yayi week,bacci ma dai a taqaice yaji yana saukar masa. "Amm....." "Ba'a musu da babba right?" Ya fadi cikin sigar tambaya yana ritsata da kallonsa,karon farko taji idanunsa sun dan mata nauyi,saita sadda kanta qasa,ya sake sakata a gaba kamar dazu suka koma,jikinta duk a mace, hankalinta a tashe,anty deena ce ta jawo mata,ta yaya zata kwana daki daya dashi?. Yayi mamaki sanda ya dawo yaga babu hafsat din ba dalilinta,sai ya tsugunna ya tattara komai waje daya ya adana,har a sannan widad na zaune a takure a waje daya,ac din dakin ya kashe gaba daya,ya rage fitilun falon,saiya kalleta "Muje ciki ki kwanta" fuska ta tattare waje daya,tanason cewa a'ah amma kuma batason yaga kamar ummu bata koya mata cewa ba'a yiwa babba musu ba,tunda gashi dazu ya fada,haka ta miqe tana biye dashi har cikin bedroom din nasa. Da ido take kallon komai,bedroom din nada wani irin weather mai saukar da nutsuwa,sassanyan qamshinsa ya kama dakin sosai,komai fari ne qal,kuma komai yana kan tsari a killace,saita haye kan sofa bed ta dunqule,shi kuma ya wuce bandaki. A ciki ya shirya cikin wasu silk pyjama sky blue,yayi brush ya feshe jiki da bakinsa da turarukansu "Zaki canza kaya ne?" Ya fada yana dan duban gefanta,cikinta ne ya bada qululu saboda tsoro,yana nufin ta cire kayan jikinta

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});