Chapter 43
Chapter 43
saka sabbabi,yace muzo dasu suyi aikin" ta zuba masa ido ne taga zaiyin ko bazaiyi ba,duk da zancan kullum yana ranta dashi take kwana take kuma tashi,duk da ranta a bace yake matuqa har komai ma baya burgeta,to amma kuma tana son alqawaruran da yayi mata din. "Su bani minti goma ina zuwa" ta fada tana juyawa,ya rusuna cikin girmamawa ya amsa mata da to. Dakinta ta koma ta fara kwashe abubuwanta masu muhimmanci waje daya,aikin nada dan yawa,don sai ta shiga dakinsu nawwara ma ta hada nasu kayan,tanason ta samu dan tayi,to amma tasan a dai dai wannan lokacin koda tayi waya gida babu lallai a samu me zuwa ya tayata,saboda kowa yasan halinta da dna banzan rowa,saidai kayi mata wahala,dole ta koma kitchen ta kashe gas din girkin,dama ba wani girkin arziqi ta aza ba,tafi sati ma basa abincin saidai yayo musu takeaway,ita kuma ta nema wani abun taci. Sai da ta kusa awa guda sannan ta gama,duk ya hada gumi saboda ba maison aiki bace,sanann ta koma kitchen tana maida numfashi,su kuma suka shiga aikin gyara dakunan. Ana idar da sallar magariba suka gama kafa kayan gadon,da yake ba mutum daya ko biyu bane,sun kusa su biyar,suna fidda wadancan kayan ta fito "Su kuma wadan nan za'a kaisu?" Ta tambayi shazali yaran gidan "Yace a fiddasu compound a ajjiyesu" kai ta kada "Ka bawa masu kayan gadon idan suna siyan second hand,tunda wadan nan ba wani dadewa sukayi ba,kuyi ciniki su baka kudin ka kawomin" kamar yace ba haka oga yace ayi ba,to amma sai yaga meye nasa?,tunda kayanta ne,kuma matarsa ce?,don haka ya amsa mata da to yana ficewa,ita kuma ta juya ta shige dakunan tana jan tsaki a ranta,kudi takeso ta tara mai yawa daga jikinsa,ko banza ta rage wani radadin. Sosai dakunan sukayi mata kyau,dukka ya zaba favourite colors dinta ne,dakunan sun canza gwanin sha'awa,duk da ranta a bace yake amma sai data danji ta sauka kadan. Ba'a rufa awa ba kuwa ya dawo mata da kudin kayan cas,ta karba ta soke abinta taci gaba da sabgarta hankali kwance,ranar baya nan,yaje azare,zai kuma kwana sai washegari zai dawo,don haka hankalinta kwance ta gama tsara abinda zatayi da kudin,koda kuwa ya dawo ya tambayi yadda akayi da kayan,barema tasan halinsa,zaiyi wuya ya tambaya din,don bashi da wannan,amma koda yana da niyyar ma ta shirya abin fada masa. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: Huguma* Page 28 *********Washegari tana dakin yaran tana sauya musu kaya bayan tayi musu wanka taji ana sallama a falon nata,qaramin tsaki taja,ita gaba daya batason baqi a rayuwarta tun asali,bare a yanzu da take cikin wannan yanayin,mimi ta aika ta dubo waye?,sai ta dawo tana ce mata baquwa ce,tadan harari yarinyar,har yanzu taqi tayi wayo irin yadda takeso,irin wayon da zata iyayi mata bayanin duk abinda takeson ji,saita ajjiye kayan nawwara da bata kai ga sanya mata ba,ta miqe tana cewa "Bari muga wanne munafukinne" tayi waje yaran suna biye da ita. Tun kafin ta qaraso ta hangi wacece,rabi'atu ce,cousins suke da abbas din,takan jima bataga rabi'atun ba,bama ita kadai ba,danginsa ma yawancinsu ba wani zuwa sukeyi ba,saidai idan an hadu a wani sha'ani idan ta samu zuwa saisu gaisa,suna girmama ta dai dai gwargwado,amma ta dauki hakanne a mazaunin don anga mijinta yana da rufin asiri ne. Fuskarta kadaram kadaham ta qaraso ta samu kujera daya ta zauna tana dan satar kallon rabi'atun,saboda daga nesa taga yadda take satar kallon falon,zuciyarta kuma ta raya mata gyaran da akayi mata take kallo "Dangin miji irin jaraba" ta fada a ranta,babu dama suga sakakken abu a gida ko a jikinka sai sun nuna a fuska ko a kalaminsu(nace uhmmm,inama suka hadun ko sukazo gidan bare hakan ta faru?). Ba yabo ba fallasa suka gaisa da rabi'atun,sai kuma shuru yadan biyo baya,sai ita din da taketa qoqarin yiwa su mimi wasa,wadanda suka qi sakin jiki da ita saboda rashin sabo da basuyi da su ba. Kai rabi'atun ta dago tana cewa "Wai nan bayanku nazo suna,kinsan a nan qanwar mijina take aure" "Uhmmm,Allah sarki" ta fada a taqaice "Sai nace nari na qaraso mu gaisa,na kuma yi miki murna ko jaje zance,ashe kuma yaa abbas aure kishiya zai miki?,kuma a rasa wadda za'a rakito miki sai 'yar wani garin,kuma ma yarinya qanqanuwa wadda a haife ya kusa haifarta" da fari cin mutunci hafsat ta shirya yuwa rabi'atun,amma jin ta fara bata hint akan abubuwan da batasan dasu ba saita maida wuqarta tana gyara zamanta "Ya kusa haifarta fa kika ce?" "Wallahi haka inna ke gayamin,tunda kwata kwata bata wuce shekara sha uku zuwa sha hudu ba" wani abu ne ya tsargawa hafsat,saita nema tashin hankalinta kaso talatin cikin dari taji babu shi,ta aro sakin fuska ta dorawa fuskarta "Kin ganta ne rabi'ah don Allah?" Kai Rabia ta girgiza "Ban dai ganta ba,amma inna tacemin ta taba ganinta gidan sau daya,badai 'yar nan bace 'yar kano ce" gabanta yadan fadi kadi jin abinda ta fada daga qarshe,ana wata ga wata,ko zakayi kishi yafi kayi da 'yar garinku,kar tasan kar ne,bawai kayi da bare hayin wani gari ba,garin ma da tasha jin masu kishiyoyi daga wannan nahiyar suna qorafi,to amma 'yar shekara sha uku zuwa sha hudu kishiya ce ko 'yar raino?. "Ni irin wannan auren banda abin hajiyarsu,mutum na zaune da matarsa ya dauko aure,a kuma tsallake gida a tafi dawa?" "Da gidan da waje duk dai kishiya ce,ko daga dakinki aka fiddo miki da ita sunanta kishiya" hafsat din ta amsa mata rana dan hade rai,saboda tasan yadda 'yan mata da yawa cikin familyn ke sonshi,kamar shi kadai ne namiji a family din nasu,sai data dinga murje idonta tana yanka musu rashin mutunci ta samu salama. "Gaskiya dai" rabi'atu ta waske ta hanyar fadin haka,bata jima sosai ba saidai hafsat din tadan samu wani haske akan lamarin,da yadda hajiyansa ke maraba da abun,daga qarshe sukayi sallama,ko pure water rabi'atu bata samu daga wajenta ba,haka tabar gidan tana tsine mata cikin zuciyarta,saidai duk da haka sudai suna adawa da wannan auren,tunda nasu basu samu ba 'yan qannensu da suka zama 'yammata gwara a bata goma daya bata gyaru ba gaba daya. Rabiah tana fita hafsat ta wuce daki cikin hanzari,ta dauko wayarta ta soma neman number din anty ummeee ta labarta mata labarin data samu,saidai duk saurinta ya zama nawa saboda babu kati a wayar tata,dole ta koma ta mobile app din bankin da take amfani dashi,ta saka card din dari biyu ta kirata. Sai data kusa tsinkewa anty ummee din ta daga,hafsat na daga tsaye ta gaza zama,sai kai kawo takeyi "Anty ummee....kina jina?" Ta fada da matuqar zaquwa,har kana iya jiyo haka cikin muryarta "Ina jinki hafsatu,lafiya?" Guri ta samu saman bedside drawer dinta ta zauna sannan ta soma magana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155