Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 29

Chapter 29

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,308 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kenan?" "Dama ina tunanin next week qarshensa taje taga ummu din,saboda ita kanta ummu kwanan nan maganar na dawo mata da yarinya taketa yi" shuru ya ratsa tsakaninsu,har uncle muhsin din ya fuskanci kamar ta shiga damuwa ne,don haka yayi gyaran murya "Ni banji komai game da haka ba hadiyya,abbas yana da nagartar da ko nujood yace yana so zan bashi,zai riqe mana widad da amana, sa'annan kuma ina da tabbaci hundred percent karatunta bazai yanke ba,zataci gaba da karatu har zuwa inda takeso,so kinga babu wannan haufin" "Gaskiya kam" ta amsa masa tana dan jin nutsuwa kadan,to amma batun zama da kishiya tasan ba abu bane mai sauqi,koda ga babbar macace bare yarinya irin widad,GOYON KAKA. ********** Tunda hajiya ta samu tabbacin samun widad daga wajen uncle muhsin wata nutsuwa da farinciki ta dinga saukar mata,haka kawai ta dinga jin nutsuwa da gamsuwa da al'amarin,ta dinga ji kamar ta daga waya tace yazo tana son ganinsa,to amma tasan zuwa qarshen wata zai zo ganinta,babu buqatar ta daga masa hankali ta sanyashi biyo hanya,sai tayi amfani da wannan damar ta yawaita addu'a kan Allah ya sanya dukkan alkhairinsa akan lamarin,yasa ayi a sa'a,ya kade dukkan fitina. ************ Dukka shirin da yakeyi tana zaune gefan gado tana kallonsa,a yanzun da zai tafi bauchi tana jin inama yace ta shirya ta bishi,zaman garin ya gama kai mata ko ina,daurewa kawai take tana cijewa,ita kam duk inda zama zai kaita indai ba cikin garinta ba bataso. Bugu da qari taga sabon key din mota garin bincike bincikenta,tana sake dauriya akan dauriya ne cike da fatan wannan motar ta zamana tata ce kamar yadda anty ummee data baiwa labari tayi mata hasashe. Tsaf ya shirya cikin yadin kufta,wanda yayi matuqar masa kyau,ya fidda kwarjininsa da kuma kyan zubi da Allah ya bashi,saita sake karkata kai tana qare masa kallo,sau tari ita kanta takan gayawa kanta tabbas abbas wani rabo ne nata da Allah ya tsaga mata sai ta sameshi,amma ita kanta idan ta tsaya ta kalli kanta tana gano tarjn banbance banbance tsakaninta dashi,shi yasa take qara matsa qaimi wajen kishinsa,saboda tana tsoro.....tana tsoron kada idanun wata ya fada kansa,ta kuma sani wasu 'yammatan indai suka baza komarsu sai sun samu,bata fiya damuwa dashi ba,tasan sam mata basu a lissafinsa,amma shi din yana cikin lissafin gomayyar mata da suke kwana su kuma tashi da soyayyarsa,koda cikin danginsa kuwa tana da wannan information din akansa. Hure mata idanu yayi da sassanyar iskar bakinsa,abinda ya sanyata ja da baya da sauri,sai kuma ta saki murmushi "Har ka bani tsoro" ta fada tana dan harararsa "Ni kika bawa tsoro,wannan kallon kamar zaki cinyeni?" Murmushi ta saki "Da da hali cinyekan zanyi,don banason kowacce mace ta kalleka kota rabeka,ni kaina bansan adadin kishinka da nake ba" daga kai yayi ya kalleta daga daura agogon da yakeyi,har launin fuskarta ya sauya,sai ya maida kai yaci gaba da daura agogonsa ba tare da yace da ita komai ba. Ya rasa wanne irin dan banzan kishi take dashi,wanda kullum baya raguwa saima daduwa da yakeyi,abun takaicin har yau batasan yadda zata tsare masa komai ba,inda yadda take kishinsa haka ta tsaya masa wajen komai da lallai ya gama yin sa'a. Ganin bai bata amsa ba tasan bazai ce komai ba,don haka ta sauya akalar maganarta "Nidai da zaka barni Allah wannan watan zan bika,kamar na shekara banje gida ba haka nakeji" "Sai next month kamar yadda nace" ranta tadan bata kadan,har ya gama shirinsa ya fito bata sake magana ba. "Rakiyar ta isa daga nan" ya fada yana dakatar da ita daga qofar falon,saboda akwai driver daga waje da zasuyi tafiyar tare,mutum ne shi mai tsananin kishin iyalinsa,yakai bakinsa saman goshinta yayi kissing dinsa yana fadin "Sai na dawo,ki kula da gida da yaran" "A dawo lafiya" ta fada a taqaice tana dubansa har ya fice,tana tsaye ta window tana leqensa har motarsu ta fice,taja da baya ta zauna saman kujera tana jan tsaki "Babu biki ba suna ba barka,an takure a baqon muhalli" ta sake fadi a fili,sai kuma ta miqe ta nufi dakinsa,ta buda ta shiga ta isa inda taga key din motar,ta jawo da zummar sake duba motar wacce ce?. Wayam taga wajen babu muqullin,ta shiga birkitawa kamar wadda ta bashi ajiya,saidai babu shi ba alamarsa,da alamu ya dauka kenan,to amma me zaiyi dashi?,ta tambayi kanta tana zurfafa tunaninta,to ba tata bace kenan?,amma kuma motar da suka fita cikinta ai tasan motar,ba sabuwa bace,gaba daya sai ranta ya baci,ta jawo waya kamar zata kirashi ta tambayeshi sai wata zuciyar ta hanata,ta shawarceta ta bari ya isa gida tukunna. *_RUMBUN K'AYA_* *_IDON NERA_* *_DAUDAR GORA_* *_KI KULANI_* *_A RUBUCE TAKE_* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank. Shaidar biya tanan👇🏻 09033181070 *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: Huguma* Page 19 Kafin ya iso tuni hajiyan ta sanya an tanadar masa abincin da yafiso har kala biyu,irin abincin da tasan zaiyi wuya ya samu a gidansa,duk da qaunar da yake masa,ta kuma hada masa lemo shima kala biyu,zobo da kuma ginger drink da aka dan matsa lemon tsami kadan a ciki qamshinsa ya fito. Da yake tun karfe tara na safiya ya taso,ana azahar yana shiga layinsu,jakarsa kawai ya bayar aka shiga dasu shi da drivern nashi da yake usulmi ne suka wuce masallaci. Ana idar da sallah yace masa zai juya ya koma kaduna,yasan akwai aikin da ya baro,saboda haka bai matsashi ba,yadai karba abincin wajen hajiyar ya hadashi dashi,yace yaci a mota,ya kuma fidda kudi masu dan nauyi yayi masa ihsani,wannan yana daya daga cikin abinda yasa abbas din ke samun biyayya da qauna gami da daukaka a wajen aikinsu,duk da biyayya dole ce a tsarin aikunsu,amma suna masa soyayya ne ta har cikin ransu saboda kyawawan dabi'unsa. Cikin nutsuwa ya shiga gidan nasu,yana jin farincikin ganin hajiyar tasa,jtama tana falo a zaune tana ta dakon shigowarsa,ta amsa sallamarsa ya sanyo kai falon fuskokinsu dukka dauke da murmushi. Kamar kullum ya duqa a qabanta ya gaidata,ta amsa masa cikin kulawa addu'a gami da tambayar lafiyarsa data iyalinsa,ya tabbatar mata da komai lafiya lau,ya kuma isar mata da saqon gaisuwa daga hafsa din,wanda a zahiri bata samu hakan ba,shi ya qirqira abinsa saboda sama mata soyayya da kuma kare martabarta a idanun mahaifiyarsa. Da kanta tayi serving nashi,yana cin abincin suna hira,wanda kusan abubuwane da suka dan faffaru da baya nan,ciki harda ciwon da diyar babbar yayarsu tayi "Zanyi qoqari na shiga in sha Allah" "Ya kamata,don ka kwana biyu bakaje mata ba,tana ta min qorafi rannan" "In sha Allah". Sai da aka kira la'asar sannan ya fita a falon,yace ma hajiyan zaije wajen Suraj,amma bayan magariba zai dawo "To Allah ya tsare,akwai maganar dama da nakeson nayi dakai" "To bari na zauna mu gama sai na wuce" "A'ah,jeka abunka,idan ka dawo

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});