Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 60

Chapter 60

A Rubuce Take Book 1 Complete Hausa Novel – Widad and the Secret of House 1,314 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

cikin bacin rai take,saboda tasan yana buqatar sauyin abinci kenan,zai kuma yita mata tsirfar kala kalar girki,tafi jin dadi idan cefanensu ya qare,zata girka abinda duk ranta yakeso babu wahalar da kai. Ita ta masa rakiya har bakin motarsa,ya shiga ya kunnata ya fice,ranta yayi mata dadi sosai,ganin ya share batun shiga sashenta "Wannan abun yana aiki,sai dan banzan wahala" ta fada a ranta,bata taba kawo zai fice bai shige ba,to amma auren soyayya ne kuwa hakan?,anya ba hadin hajiyar bane kamar yadda taketa jin qishin qishin tana qaryatawa?. Duk yadda latifa tayi kan widad tayi shuru amma abun ya faskara,yadda suke hanya suna ta cin kwalta har zuwa garin kano,haka ta lafe cikin kujerun ta ta dinga rera kuka,tun tana zaune tana aikin lallashi harta haqura ta zuba mata idanu,sallah kawai ta tashi tayi ta koma fa kwanta taci gaba da kukanta,koda latifan ta gama girkin rana wajen qarfe biyu da rabi na rana tayi mata maganar ta tashi taci qin tashi tayi,tayita lallabarta amma tayi funfurus,har akayi la'asar,ta sake lallabata amma taqi koda kallon abincin sai ruwan hawaye,bayan wasu mintuna ta gwada bata baki,saita tarar bacci yayi awon gaba da ita cikin kujerun "Gwara ma kiyi baccin kya samu salama,wanann kuka haka?" Ta fada tana jin tausayinta cikin ranta,saita samu dama ta shirya abincin dare mai rai da lafiya,tunda bata ga alamun girki daga wajen hafsat ba,tunda rana ma da jama'ar kano suka tafi bata sake jin duriyarta ba,tana sanya ran a nan zaici abinci indai abun ya tafi kamar yadda yake a tsare a shari'a,don haka ta tsara abincin da kyau. Dab da sallar magariba widad din ta motsa kadan,sai ta tsaya cak tana qarewa falon kallo tana daga kwance,kwanaki biyun nan mantawa take ba'a gida take ba,duk sanda tayi bacci ta farka saita zata zata farka ne ta ganta a dakin ummu. Tuna komai da tayi cikin yinin yau sai ta fara tara sababbin hawaye,sannan ta miqe daga kwanciyar tana zuro qafafunta qasa,dai dai lokacin latifa ta fito daga daya dakin da ta zabi zama a ciki "ai gwara da kika tashi,kwanciyar tayi yawa" ta fada tana qarasowa inda take zaunen,sai kuma ta dubeta "Aah,kukan dai widad?,to kiyi haquri mana,tashi kiyi sallah kizo kici abinci" kamar jiran me tanka mata takeyi wasu sabbin hawayen suka fara sauka,da qyar latifa ta lallabata ta shiga bayinta ta dauro alwala tayi sallar,amma qememe taqi daukan abincin ko cokali daya taci,sai dan banzan kuka da takeyi,abinda ya daga hankalin latifa kenan,tayi lallashin duniya amma widad din taqiyin shuru,tana kuma tsoron kira mata ummu taje ta birkice mata fiye da yanzu,a haka suka zauna ta sakata gaba har aka idar da sallah isha'i. Koda ya dawo a masallaci ya tsaya,sai da aka gama sallar isha'i sannan ya qaraso gidan,yau din shi daya ne,shi yayi driving abinsa,ya tsaida motar a parking lot na gidan ya kashe motar ya fito. Tsayawa yayi yana duban sassan guda biyu,baisan yadda akeyi ba,baisan wanne zai shiga ba,tsahon wasu mintuna kafin ya zare hannayensa daga aljihu,ya soma takawa zuwa sassan hafsa,tunaninsa ya bashi ya fara da babba tukunna. Yana tura qofar falon muryar mimi ya fara ji,sallamarsa ta ja hankalinsu,suka watsar da kayan wasan dake hannunsu suka nufoshi a guje,kowacce na kiran "Daddy oyoyo" dukka su biyun ya hada ya rungume a jikinsa,yana kallon yadda sukayi fes dasu suka canza,da alama suna samun kulawa da tafi ta mahaifiyarsu "Yaushe Kuka dawo?" Ya fad yana barewa nawwara chocolate "Dazu anty maamaa ta dawo damu" dai dai sannan hafsat dake kitchen tana ta faman yadda zata hada masa abinci me kyau da zai janye hankalinsa ta fito. "Sannu da zuwa" ta fada tana goge hannuwanta a jikin zanin jikinta,ya kalli zanin,kayan jikinta ne tun na safe,ya kuma tabbatar bata sake wani wankan ba,ya dauka zaiga canji ko yaya ne,amma ba wani abu daya canza,hatta da falonta a birkice yake,har da sauran maqalallun dattin yinin bikin da tayi da ba'a gama tsaftacewa ba,duk da haka ya danne shima,yana kallon yadda itama taketa qoqarin danne komai,duk kuwa da irin mugun baqin kishinta "Yauwa madam,kun yini lafiya ya yara?" Ya fada yana kashe mata ido,saita dauke kai tana jin wani zafi a ranta,duk sanda ta tuna akwai wata cikin gidan fa wai itama matarsa ce,sai taji kamar ta shaqeshi "Lafiya qalau" ta bashi amsa a gajarce tana nufar kitchen din "Bari na kawo maka abinci" ajjiye nawwara ya fara qoqarin yi,shekaru kusan bakwai ta kasa haddace me dame yakeso idan ya dawo "Noo,zan fara zuwa nayi wanka tukunna,kin kunna min heater dinne?" Da zaiyiwu ashar ya kamata ta qunduma,saidai tasan ko giyar wake tasha wannan shine kuskure mafi muni da zata aikata,me yakeson maidata?, baiwa?,wai da wanne ma zata ji?,da hidimar yara ko da ta kitchen ko kuma da tasa hidimar? "Ban kunna ba,banma shiga sashen ba yau kwata kwata" kai yadan kada,yanzun kenan yadda ya baro sashen haka zai koma ya tadda shi,babu shara ba komai,duk da cewa dama ya saba da hakan,sai ya sake kada kansa yana nufar qofa "Okay,ki shirya abincin,sai ki shiga ki kira qanwar taki kafin na fito" da harara ta bishi,sai taja tsaki bayan ya fice "To ubana,ga jaka tayi mata girki ko?" Buguzum buguzum tayi hanyar kitchen din tana mita hade da bala'i kamar zata fashe "Ni gaskiya na gaji,na gaji wallahi,dama hausawa sunce abun aro baya rufe katara,wannan attitude din dana ara ya fara isata,pretending din ya fara kaini bango" ta qarashe fada tana jan kwanon data gama hada coleslaw,bata kula ba santsi yasa ya subuce a hannunta ya fadi qasa ya tarwatse,abinda ke ciki yayi nasa guri "Innalillahi,kai jama'a" ta fada qwalla na cika idanunta,sai gasu kuwa sun gangaro,ta duqa a wajen ta fashe da kuka,dukka yaran da suka biyota sai sukayi carko carko suna kallonta. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 39 Cikin girmamawa latifa dake zaune gaban widad wadda ke lafe cikin kujera kamar wata 'yar mage tana hawaye ta amsa sallamarsa,idanunsa a kanta ya qaraso shigo wa,sai ya janye idanuwan nasa ya tsaya tsakiyar falon yana rungume da hannayensa. Gaidashi latifan tayi,ya amsa a mutunce sanann ya sake maida dubansa ga widad tare da tura tambayarsa ga latifa "Lafiya dai ko?,ba wani matsala?" Gyara tsaiwarta kadan tayi "Uhmmm,wallahi gata nan,tunda suka tafi take kuka,nayi nayi da ita amma taqi yin shuru,yau ko abinci bata ci ba" "Ya salam" ya fada yana lumshe idanunsa hadi da. Budesu lokaci guda "Matsala kan matsala" ya furta qasan ransa,saiya sauke hannuwansa ya fara takowa zuwa inda take kwance,ganin haka sai latifa ta juya ta nufi daki. Dab da ita ya tsaya yana dubanta,ita kuma saita cusa kanta cikin pillow tana sake sakin sabon kuka,batason ganinsa kwata kwata,saboda shi ya jawo mata,qila da tuni yanzu suna wajen anty madina suna hirarsu abinsu,qila da

Table of Contents

Chapters

155 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});