Chapter 132
Chapter 132
take nufi,dole ta yarda tadanyi gyara a ranar ko zata cimma manufofinta ta ruwan sanyi. Suna gama wayar ta miqe tana tunanin ta inda zata fara,sai ta yanke ta shiga da kanta ta kira widad din,can qasan ranta tana mamakin yadda ko motsinta bata sake ji ba bare ta shigo taga abinda ya kamata tayi mata. Tun bata qarasa ba taga sassan nata a kulle,ta juya cike da mamakin ina taje?,ko gidan hajiyan da aka rufe babinsa ta koma?,harta dawo da baya.....amma tana kallon sashen abbas din akalar tunaninta ya canza,saita nufi can,duk da zuciyarta na gaya mata bata ciki,to amma mafi rinjaye na tunaninta yana rinjayarta ga zuwa sashen nasa. Tana buda qofar falon abbas dake riqe da hannun widad yana bude ta bedroom din,idanunsa na kallon gefansa yana magana da widad din,cak hafsat din ta tsaya kamar an dasata,qirjinta yana harbawa,ta zuba masa ido tana son ganin waye yake biye dashi. Wani mugun ashar ne taji ya taso mata,saidai abinda yazo ya tsaya mata a wuya ya hana kowanne kalma fita daga bakinta,widad fa take gani,widad yau a dakin mijinta?,riqe da hannunsa?,baqar zuciya da kuma fushin dake cin zuciyarta ya sanyata cikin zafin nama ta harbo zuwa cikin falon. Takunta yaja hankalinsa sanda yake tsokanar mimi tayi kyau,ya tashi daga durquson da yayi,ya zuba mata idanu,don kallo daya yayi mata zuciyarsa ta bashi akwai wani abu na daban. Kafin ta qaraso idanunsu suka sarqe cikin na juna,wani irin baiwar idanu gareshi masu tsananin kwarjini,abinda yayi mata tasiri kenan,kallonsa ya ratsa zuciyarta ya karya duk wani zafi data debo da kima qissime qissime da zuciyarta keyi mata na irin abinda zata aiwatar,saurin data kwaso ya canza zuwa nawa. Kallon kallo suka ci gaba da yiwa juna,sai taji zuciyarta kamar zata fashe idan bata ce komai ba,a sannan ta tuna ita din me laifi ce,ta kuma tuna gargadin da anty ummee tayi mata "Kissa saida kwantar da kai"maganar data gaya mata ta qarshe kenan "Nace me za'a dafa maka?" Ta maye gurbin dukka wani bala'i daje qasan zuciyarta da wannan tambayar,tambayar da yaji sam bata dace da yanayin da ya ganta a ciki ba,to amma koda ta tambaya dinne da gaske,yanajin ya zuwa yanzu ya kamata ya nuna mata fushinsa,saiya dauke idonsa daga kanta ya maida kan 'yarsa "Bana buqatar komai" ya amsa mata a dake yana duqawa yana gyarawa mimi kwalar rigarta. Wasu irin hawaye ne masu dumi suka cika mata idanu,ta zubawa widad ido,wadda sam idanunta baya wajen,ta tattareshi akan tv,haka kawai takejin wani irin itama cikin ranta, yanayin gidan a yau ya sake mata rashin dadi,ta tabbatar a lokaci irin wannan a kaduna ita dashi din suna kitchen tare suna girki,ko suna backyard dinsu suna wankin undies,ko suna karatu ko kallo. Qwafa taja can qasan ranta tana danne hawayen,batason ta zubdashi a gaban widad din,ta juya tana barin falon,kamar zatayi bindiga ta fashe haka takejin kanta,nadama da dana sanin ma tambayarsa me za'a girka din ya cika Zuciyarta,gashi ya yarfata a gaban qaramar yarinyar da a haife ta haifeta. Hanyar data fita yabi da kallo,yaja dan qaramin tsaki sannan ya koma ya zauna kusa da mimi "Hadamin coffee ko black tea" ya bata umarni yanason danne shima nasa fushin,tadan kalleshi da wani irin yanayi,cikin zuciyarta takejin akwai wani abu dake damunsa,don ba haka yake ba,kamar zatayi magana saita fasa,ta miqe tana nufar qofa. Tana sanya qafarta a falonta taji an biyo bayanta,ta tsorata sosai,taja da baya tana dubanta,sai data gane hafsat dince saita saki ajiyar zuciya tana lumshe idanunta hadi da budesu tana kallonta. Wani irin kallo take bin widad dashi,tana jin kamar ta fincikota ta rufeta da duka,yarinya qarama amma tana neman dagula mata lissafi,tanaji a jiki da zuciyarta abbas ya sake canzawa ne sosai ta sanadin aurenta,a baya idan ya fiya cika masa ciki tattarawa yake ya koma inda ya fito,sanda suna gari guda kuma saidai ya tsiri zaman gidan hajiya,ko kadan bata damuwa,saboda tasam ba wani wajen yaje ba,kuma shi din ba mai kula kulen mata bane,asalima sam basa cikin tsarinsa,don haka ba kasafai ta fiya damuwa,idan ya qare fushinsa zai dawo yaci gaba daci abincinsa ko yaya ta dafa kuwa,idan yaji bai masa bama zai shiga kitchen ya dafa da kansa (Hmmmm,duk a lokacin bata taba kawowa miskilanci bane irin na mijinta,ta aza hakan akan babu yadda zaiyi da itane,kamar dole yayi duka abinda yakeyi din). "Uban me kika shiga yi dakin abban mimi" kamar daga sama furucin yazowa widad,mamaki ya kamata,for now dai ta fahimci matsayinta daya da hafsat din,ta kuma fahimci me kalmar aure take nufi,indai haka ne bataga muhallin wannan tambayar ba,duka wannan ba damuwarta bane,abinda yafi bata mata rai kalmar UBAN WA data fada,wanda dai dai yake da zagi a wajenta "Dake nake!" Ta sake fada cikin tsawa kamar zata kai mata duka,amma ga mamakinta sai taga widad din ta tsireta da manyan idanunta "Ai ba haramun bane tunda kema naga kina shiga" ta fada a sakalce abunta tana dubanta. Zallar mamaki ya saukowa hafsat din,tayi sakato tana kallonta "Ni kike gayawa wannan maganar?" Ta fadi tana jin wani zafi har cikin ranta "Me nace mommy?" Ta tambayeta kanta tsaye,a karo.na biyu ta sake shiga mamaki,anya kuwa?,anya abinda take tunani bai faru ba?,yaushe yarinyar tabfara fahimtar abubuwa haka?.,da tayi wani qaramin tunani sai tabar wancan maganar tace "Ki wuce kije kiyi aikinki,suna can suna jiranki" "Tom,bari na dafawa uncle tea" tea?,har tea yake sakata dafa masa saboda zallar jawo mata raini?,wanne girki ta iya da zai buqaci tea daga wajenta "Ni kike.maidawa magana widad?" Juyowa tayi tana kallon hafsat din,ita gana daya sai taji ta sire mata daga zuciyarta,tunda ta fahimci akwai qaryayyaki da yawa data taba gaya mata,a dabi'arta kaifi daya ce,ko meye za'a yi mata bata qarya haka ta taso tun quruciyar ta,dalilin da ya sanya ta sake shan wahala kenan sosai a wajen 'yan uwanta da cousins dinta "Me nayi mommy?,aikinsa shine gaba da kowanne aiki fa,ba kyau miji ya saka kaqi" zuwa lokacin gaba daya hafsat din ta gama sarewa,lallai qaryarta ta fara qarewa,tund har yarinyar ta fara sanin ma'anar kalmar miji,ta kuma fara tantance bin umarnin wata a gaba da nata umarnin,basu taba musayar magana da ita ba koda da sau daya,amma yau da ita suke musu?,tana ce mata ga yadda za'a yi itama kuma tana fadin nata,ah wannan babbar musifa da babbar guguwar canji ce ta tunkarota,wadda take buqatar zama na musamamn da shawarwari don sanin meyenmatakin dauka na gaba,daga wannan sai bata sake cewa komai ba,ta juya tana barin wajen tana jin kamar duniyarta tazo qarshe gaba daya. Tsakin da batasan yazo bakinta ba shi ta fitar,tadan harari hanyar data wuce din "Kawai kawai ni...."sai kuma tayi shuru tana quna quni,ita tunda taga yadda taketa wani tsare mata uncle dinta da kallo taji tana jin haushinta,bata taba ma kula da haka take zuba masa ido ba sai yau din,haka ta shiga kitchen din,ta fara duba kayan hada tea din da tasan yana matuqar so ta fara hada masa,lokaci lokaci tana dan jan tsaki. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 87 Wayar anty ummee ta sake kira cikin mugun rudani da tashin hankali tafara gaya mata yadda ake ciki,ita kanta abun ya bata mamaki sosai "Wannan maganar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155