Chapter 47
Chapter 47
sauran baqi na gidan,har ta isa qofar setting room din. Jim tayi tana duban baqin half cover din dake qofar setting room din,wanda keta sheqi "Waye ma to a ciki?" Ta tambayi kanta,bata sani ba don haka ta tabe baki,cikin wannan d'arin d'arin nata da rashin sabo da maza ta saka kai ciki tare da yin sallama. A lokacin kansa yana duqe a qasa,yanata trying number hafsat ce,wadda tunda ya taho basuyi waya ba,duk kiran da zaiyi sai ace masa is switched off. A hankali ya daga kansa yana motsa labbansa tare da amsa mata sallamar,idanuwansa suka fada a kanta sanda take takowa kamar mai takatsantsan kada ta taka kwalba,baby face dinta dake tsakiyar blue black din hijab dinta ta fito fes,qananun gashinta masu santsi dake kwance gaban goshinta sun sake qawata fuskar,dan qaramin bakinta me red lips ta dan tsukeshi waje guda,fuskarta sam babu fara'a,sai ya lumshe idanuwansa kana ya maidasu qasa ga hannunsa inda wayarsa ke riqe,shidai baisan me hajiya ta hango ba data zabi ya auri qaramar yarinya har haka,kyau?....ko kuwa me hajiyan ta kalla?,shi kansa bai sani ba. Tazarar wasu inches ta bayar a tsakaninsu ta ajjiye kwandon,tana daga tsugunne ta gaidashi da siririyar muryarta "Ina kwana?" "Kin tashi lafiya?" Ya amsa mata yana sake daga kanshi gareta a karo na biyu,bata amsa masa ba sai miqewa da tayi tsaye ta soma shirin ficewa a setting room din,saboda gaba daya a tsorace take,already ummu tayi mata horon tsoron maza sosai da shan inuwa daya dasu,a yanzun kuma bata gama sanin muhimmancin abbas din ba Da kallo yabi bayanta,dariya ta taso masa can qasan ransa,ta yaya cikakkiyar budurwa mai shekaru da wayo ta aikata haka?,sai ya gyara zamansa kadan yana lalubo sunanta "Widad" ya furta a tausashe,tsayawa tayi cak gabanta yana faduwa,dama yasan sunanta wai?,ta tambayi kanta "Zo mana" ya sake fadi,abinda yasa ta waiwayo kenan,suna hada idanu duk wani kuzarinta yayi nasa waje,sai ta narke fuska "Ummu zata yimin fada idan na dade" kai ya girgiza yana lumshe idanunsa kamar yadda yake a al'adarsa "Ba zaki dade din ba,yanzun nan zaki tafi" kallonsa takeyi,sai ya jinjina mata kai alamun tabbatarwa,don haka ta dawo a hankali,ta samu nesa dashi ta zauna. Tattara dukka hankalinsa yayi ya zuba mata idanu,yanzun ta ina zai fara mata bayani ma?da wanne harshe zai mata magana ta fahimci abinda yake cewa quruciya duk ta baibayeta?,a qa'ida babbar budurwa ce yanzun zaune a gabansa,sai yafi sanin yadda zai dinga handling abubuwa har su saba da juna. Motsawa tayi kadan tana hade rai saboda yadda yake kallon nata ya sake takurata,ya fahimci haka sai ya aje wayar hannunsa,a bisa tilas ya arawa fuskarsa murmushi sannan ya fara magana "Ummu ta gaya miki an daura miki aure ko?" Kai ta gyada tana kallonsa "Good,daga yanzu na zama yayanki,na zama kuma abbanki,zamu tafi dake can zan kaiki gidana,zamu tafi tare,kema gidanki ne duka,zakiyi duk abinda kikeso a ciki,kina so?" Idanunta masu tsananin haske da ratsin gold color ta fara rarrabawa a tsakanin nasa idanun,sai ya kafeta da idanu sosai yana kallon yadda suke juyawa,yadda ta mele baki ta kuma tabe fuska hadi da lumshe idanunta,eye brows dinta masu tsayi suka hade waje guda sannan ta sake bude idanun warrrr a kansa yasa tsigar jikinsa ta zuba "Bazan dade ba zaka dawo dani wajen ummu?" Ajiyar zuciya mai nauyi ya sake yana dan murmushi kadan "In sha Allah,nima daga yau na zama yayanki ko?" "Uncle dina dai ko?,naji nujood na cewa sunanka uncle abb...." Kasa qarasa sunan nashi tayi,tana jin kada tayi abinda bata kyauta ba,murmushi ya subuce masa ba tare da ya shirya ba,har fararen haqoransa suna bayyana,ya fuskanci nauyin kiran sunan nasa take "Uhnnnn,uncle abbas" sai ta gyada kanta tana hade hannayenta waje guda,yakai duba ga hannun nata,tsararren jan lallen nan nata yana nan tas saman hannunta,ya zuba masa idanu kamar mai karnatar taswirar zane,lallai akwai hikima mai yawa ga masu yin lalle,har da suke iya tsara zane haka ya bada wani kala da nau'i mai kyau. Rai ta hada sosai ganin yana ta kallon hannun nata, saita zare hannuwan nata zuwa cikin hijabin tana sake qudundunewa waje guda,ya dauke kansa yana maidawa ga dan qaramin leda yar mitsitsiya daya shigo da ita,sai ya dauka ya tura mata "Wannan waya ce,ki cewa ummu a kunna miki,akwai komai a ciki,zan dinga kiranki,sauran kuma kudi ne,duk abinda kikeson siya ko kike son amfani dashi ki dauka a ciki,kada ki sake tambayar kowa yayi miki wani abu" murna farinciki da kuma mamakin bata waya da akayi ya lullubeta,to amma kuma tana tsoron kaiwa umnu kayan tace wani ne ya bata,duk yadda take zumudin wayar saita noqe "Wallahi ummu zata dakeni,zatace waye ya bani" murmushin dole ya sake subuce masa "Kice uncle abbas ne,idan ma bata yarda ba kice a kirani,bazata miki fada ba" sai ta matso kadan,ta dauki ledar tana cewa "An gode,Allah ya saka da alheri" girma yaji addu'ar tayi masa,sai ya bita sa kallo kawai harta fice,ya maido dubansa cikin falon yana sauke gauron numfashi,tsahon zamansa da hafsa bata taba fadin haka ba,duk girman kyauta idan yayi mata 'An gode' shine iya abinda ta iya fade kenan,bata buqatar cin komai,so yake kawai yaga sun dauki hanyar bauchi,to amma babu dadi su kawo suga baici komai ba,gashi ya baro baqi a masauki,don haka ya fidda qaramin flask din tea dake cikin kayan,ya hada tea. A gaggauce yake sipping,yana tsaka da kurba uncle muhsin yayi sallama "Aah ya haka bakaci komai ba?" Ya fada bayan sun gama gaisawa yaga abbas na ajjiye cup din "Sauri nake ne,ya kamata mu dauki hanya da wuri,saboda kamar gobe nakeson komawa kaduna,akwai gyare gyare da za'a yi acan,a office ma kuma ina da ayyuka da ban gama settling nasu ba bare na dora da nawa,ban taba aiki a kaduna ba sai wannan karon,kaga ina buqatar maida hankali na sauke nauyin al'umma dake kaina" kai muhsin ya jinjina "Gaskiya ne,to shikenan,muje kayi sallama dasu saimu fita tare,zaka saukeni a al-hamsad tower zan shiga wani shago akwai abinda nakeson dubawa,zuwa azahar an kammala walima in sha Allah saiku wuce kafin la'asar" Sai data gama nuqu nuqu da fargabar nunawa ummu kayan daya bata,da taga ba zata iya ba saita wuce sassan anty madina,ta sameta ta fito a wanka,don haka ta zauna cikinsu walid dake falo suna kallo harta gama shiryawa ta fito ta sameta "Widad,har ya tafi baqon?" Kai ta gyada tana miqa mata ledar "Wannan ya bani,sai da nace bazan karba ba ummu zatamin fada,yace wai ba zata min komai ba" dariya ta subucewa anty madina "Taso nan" tace da ita bayan ta karba ledar,suka matsa gefe can inda yaran ba zasu jiyosu ba,zama tayi ta zaunar da ita a gefanta "Shi wannan ai ba baqo bane yanzu,mijinki ne kin gane?,kamar ni da abban walid,kamar ummu da alhaji,kin gane?" Tadai jita,amma bata gane mai take nufi ba,ita kallon abban walid da anty madina takeyi a mazaunin yayanta ne,ummu kuma alhaji babanta ne "Bari muga me miji ya baiwa matarsa kyautar farko?" Ta fada tana dariya,ta zazzage ledar,kwalin kyakkyawar waya qirar samsung ta fado hade da sabbin kudi a miqe fil dasu "Lalalala,ah lallai wannan diya tamu da goshi take,tun yanzu?" Dariya ta kubcewa widad,haka kawia taji kunya ta kamata,saita sanya tafin hannunta ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155